Har wani jan hawaye ne ke kwanciya a idanun Bilal, wanda yake ƙara tabbatar da mai kallonsa halin da zuciyarsa ke ciki a bayyane, duk da haɗiye abubuwan daya zama ɗaya daga cikin ɗabi'arsa. Babu abinda yake ɗaga masa hankali irin kalmar sana'ar “Ƴar tsala" da Ridayya take
Meta rasa a duniya? Ta zaɓi miji sama da komai.
Ƙiitttt! Sautin ƙarar haɗuwar motoci biyun ya bayar, cikin saurin driven ɗaya motar ya riƙe nashi kan motar, da hanzari ya ɗago da nufin sauke bala'in dake cin ransa tun a hanya, wanda ya gani cikin ɗaya motar ya sanya bakinsa tsayawa a hangame sai kuma ya buɗe ya ce. "Bilal" A fili kuma da ƙarfi Junaid ya furta hakan saboda ta'ajjujin ganin Bilal gashi a tsakiyar titi amma tunaninsa da hankalinsa ya rabauta.
Junaid ya zuro kansa ta gilashin motar ya ce "Bilal! Bilal!" A gigice Bilal ya dawo tunaninsa yana take motar a fili ya ce
"Su.. Subuhanallahi"
Ya faɗa da ƙyar, sarai; ya gane mamallakin muryar kawai ya zo masa a bazata ne, baya so, da gaske sam baya son kutse cikin lamarin shi, ya daidaita nutsuwarsa har lau bai kalli Junaid ba. "Bilal ina magana ka manshe ni banza"
“Junaid zanci Ubanka, wallahi zanci Ubanka ka sake kiran ko kalmar B balle Bilal ka tsahirta mini" Tun da ya ji Bilal ya yi zagi ya san ba sauƙi, a hankali ya ce
"Girman naka ne idan ka yi zagin ma babu laifi, ka sassauta ka yi parking da motar taka mu yi magana" Junaid ware idanunsa akan Bilal.
Bilal ya yi shiru, domin danja ke riƙe da shi dama da tuni ya san inda dare ya yi masa
"Karka ce mini akan Ridayya kake haka, ban yi zaton haka daka gareka ba, ko da kowa a mafarki ne, Ridayya dai? Uhmm!"
Kammala maganar ya yi daidai da bada damar shigewa Bilal ya take giyar motarsa, da sauri Junaid ya mara masa baya, ganin da gaske ba zai daina binsa ba ya sanya Bilal juyawa ya ɗauki hanyar gida kai tsaye. Bilal na zuwa ya fita daga cikin motarsa, daidai nan Junaid ya fito yana faɗin "Don Allah ka saurare ni, Amma ta turo ni, kai ba a iya gane halin da kake ciki balle hukuncin da zaka ɗauka" Bilal ya tsaya yana ware idanunsa akan Junaid, wata kalar dokawa zuciyarsa ke masa baya ƙaunar jin maganar da duk ta shafi Ridayya. A fili ya ce
"Junaid ka haife ni ne? Shayar dani ake? To; tun kafin na fasa maka baki ka saurara mini"
Ya shige bayan kammala maganar, sashin Baba ƙarami ya nufa, Junaid kuma ya shige sashin su Amma. Tunani fal a ransa na abubuwan da suke faruwa a rayuwar Ridayya.Zameer tun sassafe bayan dawowa daga masallaci ya shirya tsaf cikin yadi mai laushi ya yi kyau sosai, kwarjinin da nutsuwarsa ta bayyana a fili, asalin kyansa wanda yake ƙara narkar da zuciyar Ridayya ya fiddo kansa da kansa, wani sahihin kyau ne da shi wanda sai ka nutsa zaka gani, baya da hayaniya a kame fuskarsa take koda yaushe. Yana ɗaura lins ɗin rigar Khairy ta dube shi sosai sai kuma ta ce
"Meer fita zaka yi ne?"
Ta furta a kasalance, wanda hakan ya yi tasirin wajan Meer, duk yadda yake kokawa da kansa wajan ganin ya gujewa kallonta haƙarsa bata cimma ruwa ba, zuciyarsa ta sanya ƙata tare da shure gargaɗin na Meer, yana riƙe kansa ba tare da zato gabaɗaya yaga idanunsa kwance akan kyakkawar fuskarta fara tas da ita, irin farin da yake so.
"Kina zalunta ta Khary,
Karki sa na sake aikata abinda ban shirya ba"
Khairy ta juya idanunta, fusga numfashin Meer ya fara a gaggauce, ya juya mata baya.
"Idan ka fita dame zan yi breakfast?" A taƙaice ya ce "Ina raguwar Indomie dana kawo miki katan guda?" Ta ce
"Saura biyu, ƙwan ma haka" Yana ƙanƙance ido a wannan karan duk nacin zuciyarsa ya yi alƙawarin bazai taɓa juyawa ya kalli Khary ba
"Indomie biyu Khairy bai isa ba? Ba isa ba Khairy?" Ta miƙe tsaye, daga ita sai kayan bacci.“Ba zan samwa matarka ba, Meer ina son matarka ta san wacece ni da ma'anar zamana a gidan nan, kai da kanka kasan kaf danginka babu mai suna Khairiyya"
Ya girgiza kai a hankali ya ce "Ke da kika san dangin nawa, Ridayya bata sani ba" Ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Khairy shan gabansa ta ce
"Ka daina saka mini sunan matarka cikin lamarina, na ga ji da kwana zuciyata na dokawa na barazanar da zan iya samu wajan matarka, ka zaɓa kawai"
Ya juya ya kalleta
"Baki da hankali Khairy, zaɓa kike so na yi? Karki saka na yi abinda zuciyoyi zasu ɓaci"
Yana faɗin hakan ya fice daga cikin ɗakin, bayan ya tabbatar Khairiyya ba zata buƙaci komai ba. Sanda ya fito ko ƙofar ɗakin Ridayya bai kalla, ya dai yi mamakin rashin fitowa taskar gida da ba ta yi ba, bai damu da rashin zuwa gaishe ba, haka bai damu sanin abinda ya hanata fitowa ɗin ba, ya yi wajan yana baza ƙamshin turaren shi, kamar kullum.
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...