Khairy na kwance akan gado daga ita sai gajeren wandon Zameer, tana danna waya tare da ƙyaƙyacewa da dariya. Kamar daga sama taga Ridayya ta faɗo cikin ɗakin tana huci kamar wata mahaukaciya, jiri sai neman ka da ita yake neman yi amma ta turje.
Tsirarar wuƙar ta nunawa Khairy tana nufar wuyanta da ita, idanunta jajur hawayen baƙin ciki na zuba daga cikin idanunta, na tsananin kishi da soyayyar Zameer, imagining take ita cikin ya tabbata yana da kusanci da Zameer, to; a cikin biyu za a yi ɗaya, ko dai ta kashe Khairy ko kuma ta kashe kanta ta huta.
"Kar ki mini ihu a ɗakin nan, daga ni sai ke ba ki da wani mataimaki" Ridayya ta furta tana sake nunawa Khairy wuƙar. Ganin haka yasa Khairy rikicewa tsoro ya ɗarsu a zuciyarta. Bakinta na rawa da ɓari ta ce "Na shiga uku me na yi miki da zafi haka Anty Ridayya? Me ya sa kika tsane ni?""Riƙe kalamanki marasa daraja a wajena Khairy, bana buƙatar duk wasu shaci faɗe naki, idan yau ki kaga ban kashe ki ba, to wallahi gaskiya kika faɗa mini" Ganin al'amarin Ridayya da gaske ne domin ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta, maganganun fitar da kansu kawai suke ba tare data shirya ba ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Kisa kuma? Kashe ni za ki yi, me na yi miki kina cikin hankalinki kowa?" Ridayya ta yi dariya sosai dukda cewa bakinta a waskace yake, fuskar ta tattare saboda ƙona ta da Zameer ya yi, muninta ya sake bayyana ƙarara idan ka kalli fuskar Ridayya ba za ka so ka sake kallo ba.
Ridayya ta ce "Idan na yi miki lahani, na saɓa miki kamanni tare da ji miki rauni na kashe ki za ki gane ban haɗa hanya da dawanau ba balle a laƙaba mini sunan mahaukaciya, Khairiyya ki faɗa mini cikin waye a jikinki, mene ya haɗaki zama da ɗakin mijina bayan ga naki can? Ina dalilin sanya sutturar mijina bayan ta haramta a gare ki, gajeren wandonsa, tsaraicinsa ne" Lallai daman an ce; mai haƙuri bai iya fushi da tara mutum ba. Khairy ta rikice ta rasa da wanne kalamai za ta yi amfani da su wajan shimfiɗa ƙaryar da zata tseratar da ita, daga haukan Ridayya domin ta gama tattarawa tare da azata a gurbin sabbin masu taɓin hankali."Ci...ci...ciki kuma? Ni mene haɗina da ciki? Wallahi....," Kafin ta ƙarasa maganar Ridayya ta sauke mata wuƙa a gefen hannunta, nan take wajan ya dare jini ya fara zuba. Khairy ta zunduma ihu tare da faɗin.
"Wayyo Allah, mahaukaciya ce wallahi mahaukaciya ce jama'a a kawo mini ɗauki" Ridayya ta sake sheƙewa da dariya ta ce "Ai na faɗa miki, kashe ki zan yi muddin ba ki faɗa mini cikin waye a jikinki ba"
Suka shiga zagaye ɗakin, Khairy na riƙe da hannunta tana ihu a kawo mata ɗauki, amma tsit kake ji, tamkar malam ya ci shirwa. "Khairiyya kenan ki daina ɗauka ban san me nake ba, na sani ni yarinya ce, you're smarter than me, tunaninki da nawa ba ɗaya bane ba komai nake ganewa ba idan, idanuna suka makance, wallahi a yau ko za a kashe ni, ko zan tafi gidan yari sai kin faɗa mini gaskiya ko na kashe ki a nan, idan ya so a yi jana'izarmu tare Ubangiji ya yi mana hisabi ya kuma tantance mai gaskiya" Khairiyya na kuka sosai, bawai don Ridayya ta fi ƙarfinta ba, saboda makamin dake hannunta ba a wasa da mai wuƙa."Bani da ciki, mene zai haɗani da ciki kuma? Ki yi mini rai ni gidanki ma zan zo na tattara na bar miki, idan hakan zai zama farin giki a gare ki, da nutsuwar zuciyarki"
"Hehehe ki je ina? Ai ni dake mai ƙarfi yau shi zai ƙwaci kansa lashakka, ki bar gidan Ridayya matar mijin Zameer ban miki lahani ba? Ai ƙarya kike, Har ka tuna mini, an ce da mahaukaci ba ka duka, har ke ce kike cire kaya a gaban mijina ko? To bari na cire miki nono ɗaya sai naga gobe me za ki nuna" A gigice Khairiyya ta ce "Na shiga uku wallahi kin haukace, banda haka ni da nake ƙanwar miji meye na ɗora zargin naki akai na?" Ridayya ta ware idanu ta ce
"Au, ba rami mene ya kawo rami? Kin ji na Amjat zargi? Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa, ai shi ɗa na kowa ne, ƙanwar miji ai ƙanwa ce, dole na ba ki tarbiyya saboda gudun bakin jama'a"
Khairy ta ce "Don Allah ki barni na fita, na je gidanmu babu wani ciki a jikina" Ridayya ta ce
"Kin san Allah, wallahi ba zan barki ba, kowa ya yi maka kan kara, yi masa na itace" Da gudu Khairy ta juya ta nufi wajan ƙofa ta sunkuya zata buɗe, Ridayya ta sauke mata wuƙar a wuyanta ta ƙara sauke mata a damtsen hannu, Khairy ta gantsare tana kare cikinta don a duniya yanzu ba abinda take so dama da cikinta.
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...