"Accident? Mace da yaro?" Tajj dake bayan mota ya furta hakan, haka kurum gabansa ya faɗi bai tsaya an buɗe masa motar ba.
Ya ajjiye wayar hannunsa ya fito da sauri yana gyara zama suit ɗin jikinsa ya ce
"Subuhanallahi garin yaya aka bugeta? Is she alive?"
"Sir mun yi ƙoƙarin kauce mata amma mun kasa, da gudu ta shigo gabanmu kamar mahaukaciya ce ma ga baby a hannunta"
Tajj ya dinga kallon wacce ke kwance dukda abin bigeta amma tana ƙanƙame da yaronta wanda ya haska baƙar fatar jikinta. Ya ɗan juya kafin ya kalli sergeant Tukur ya ce
"Katsina to Kano awa ne zai ɗauke mu ne?"
"3 hr (176.0 km) Sir"
Ya yi jim sai kuma ya ce "Zata wahala har tsayin awa uku, ina tunanin za a yi booking Flight ni da ita da babyn kafin ku ƙarasa mun je asibiti" Cikin girmamawa Sergeant Tukur ya ce
"Yes sir"
Tajj bai tsaya tunanin wani abu ba ya ɗauki Ridayya ya sanya ta abayan mota, har lokacin bai ga fuskarta ba kawai ya samu kansa cikin mummunan faɗuwar gaba ne. Little Bilal kuma yana wajan sergeant a haka suka nufi masaukinsu kafin a samu booking Flight ɗin ya zama ready.
Cikin sa a suka samu jirgin da yake shirye da tashi har airport suka kai su a kan idanunsu suka shiga jirgin kuma basu bar wajan ba har jirgin ya tashi da D.c.p Tajj Mujid Baita da Ridayya da kuma babynta, sai sergeant da aka sanya shi cikin tafiyar saboda yaron, lokaci zuwa lokaci Tajj Baita ke kallon Ridayya da fuskarta take a rufe mamakin hakan ya cika sergeant domin ya fi kowa sanin waye Dcp ɗin baya shiga lamarin mace da sai dai idan harkar taimako ne yadda ya nuna tausayi da attention ɗinsa lokaci guda a kan Ridayya shi ne ya fi bashi mamaki sosai.
Aminu Kano Teaching hospital a nan aka kwantar da Ridayya nan da aka sanya mata ruwa tare da yi mata gwaje-gwaje bayan kammala komai Dr ya kalli Tajj ya ce "Office please" "Ok" Tajj ya faɗa yana rufawa Dr ɗin baya jikinsa a sanyaye ya shiga ya zauna sosai kafin Dr ya kalli Tajj ya ce
"Allahamdulillah mun kammala bincikenmu a kan wannan yarinyar?"
"Yarinya Dr?" Dr ya jinjina kai ya ce "E, yarinya zai wahala idan ta cika 17yrs daidai ma. Akwai abubuwan da take buƙata sosai" Tajj ya yi shiru jin hakan ya saka Dr gyara zama yana zame gilashin idanunsa ya fuskanci Tajj sosai ya ce
"Sir da farko tana buƙatar jini a ƙalla leda huɗu kenan,abu na biyu ta samu ƙari a wajan haihuwar da ta yi amma ba a kula ba domin wajan ya ɗan fara kamar ruwa zamu wanke kuma a yi mata ɗinki, a ɗinke wajan tas. Tana buƙatar hutu domin samun nutsuwar zuciya data kwakwalwa idan ba haka ba tunaninta na iya gurɓata ainun ko Depression ya kamata saboda bincike ya nuna mana tana cikin damuwa da ƙuncin zuciya duk wasu alamomin cutar damuwa sun gama bayyana tattare da ita"
"Dr na ji ba damuwa, a yi komai kawai" dr ya girgiza kai ya ce "A'a sir maybe da kwai wani abu ka fara shiga wajan yarinyar ka ganta ko?"
Ya ɗan ɓata fuska yana jan kujerar baya domin duk a gajiye yake ga wani irin bacci dake damunsa a kasalance ya ce "Ba sai na je ba ina tunanin ka tattara baya nan kuɗin ka bawa sergeant"
"Ka dai shiga"
Ganin yadda dr ya takura ya miƙe ya nufi ɗakin da aka ajjiyeta na musamman. Tunda ya ɗora idanunsa a kan fuskarta jikinsa ya yi sanyi ya ƙura mata idanu a hankali kuma ya ci-gaba da takawa zuwa gaban gadon zuciyarta na harbawa da ƙarfin gaske "You?" Ya furta daidai da kunnensa a zuciyarsa yake cewa"Finally i got you" Wani irin tausayinta nan take ya mamaye zuciyarsa baya son mace cikin wahala da rashin kwanciyar hankali, hankalinsa tashi yake sosai musamman irin yarinyar da a shekarunta ba zai shige ace tana makaranta tana karatu ko gaban iyayenta ba, yana buƙatar sanin wacece wannan yarinyar, daga ina ta fito ina zata, last time ya ganta a Kano yanzu kuma ya ganta a Katsina meke faruwa? Dole akwai wani ɓoyayyen al'amari a cikin rayuwarta wacce ita kawai tasan hakan. Ya ɗan haɗe rai a fili ya ce
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...