Page 19

552 25 3
                                    

Tunda ta fara tafiya bata waiwaya ba, cikin kasalar da take tunanin sauri take yi haka ta nufi titi ba tare data san inda take cillar ƙafafuwanta ba. Tana tafe tana share hawayen da yaƙi tsaya mata, ga wani masifar ciwo da jikinta yake yi mata, hannunta jinsa take tamkar ba a jikinta ba saboda karayar data samu lokacin da Baffa yake haɗa mata na jaki.

  "Ɗitt, ɗitt, ɗitt"
Haka wata dakakkiyar mota ke danna mata horn amma ina, Ridayya babu abinda take ji da matukin motar zai mata adalci da ya bi ta kan ta, kilan farinciki da jindadinta yana Aljannar firdaus. Tana ƙoƙarin shiga tsakiyar titin ta ji an saka hannu tare da fincikota zuwa baya rai ɓace mutumin ke magana idanunsa rufe

"Ke wacce kalar yarinya ce? Kurma ce ke da ana horn bakya ji? Who do you think you are? Eh? Salon ku jawa mutum bala'i a wannan rayuwar da ta tsada kuɗin diyya ma da ɗuwawun shi yake zaune, banda azumi sittin" Kasa cewa komai ta yi kanta ƙasa jikinta duk rawa yake don fargaba ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, musamman da ya ga taƙi kallonsa. Inda take fuskanta ya koma Ridayya ta yi saurin sauya direction ita bata so ya kalli fuskarta don bata san da wacce kalar dabbar zai haɗata shi kuma.

"Kurma ce ke da ina magana za ki yi ignoring nawa? Wace ke?" Ya faɗa yana sake kai hannu zai fusgota ta yi saurin juyawa tana haɗe hannunta biyu idanunta har yanzu hawaye yake fiddawa muryarta na rawa ta ce "Ka yi haƙuri don Allah" Zaka ɗauka iyayi ta yi wajan maganar saboda a sanyaye muryar ke fita, ga kukan da ya zama abokinta kodayaushe. "Goodness!"

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wa'innahu Sulaimanu wa'innahu Bismillahir.....," Da sauri ta buɗe dara-daran idanunta farare tas ta ƙura masa ido irin me kake nufi ɗin nan? Shi kam murya na rawa ya ce "Oh.... Shi.... Shikenan it's okay" Ya juya da sauri zuwa cikin mota ɓangaren direba yana addu'ar data zo bakinsa. Yana shiga motar ya kurma ihu ya ce "Aljana ce, mun shiga uku na yi gamo" Duk ya gigice saboda har zuciyarsa ya ɗauka gamon ya yi dalilin duhun magaribar daya kunno kai ga baƙin Ridayya gami da baƙar abayar data saka a jikinta. Wanda yake zaune a gefe ɗaya hannunsa riƙe da jarida yana dubawa don shigowar su garin Kano kenan tafiyayyiya sukai.

"What nonsense, Mahmud?" Wanda aka kira da Mahmud ya ja numfashi idanunsa waje ya ce "Aljana ce, Aljana na gani?" Ya ware Idanu da mamaki can ya taɓe baki tare da yin shiru. Mahmud ya ce

"Tajj da gaske Aljana ce wacce mu ke wa horn fa" Ya sake ɓata fuska ya ce "In Ramadan period?" Ya ce "Wallahi Tajj" Tajj bai sake magana ba don baya ra'ayinta da ƙyar Mahmud ya iya jan motar suka ɗauki hanya a ransa yana mamakin mugun halin Tajj Baita ko jajinta masa bai iya ba.

Ridayya kowa itama a tsorace ta matsa daga wajan domin ta ɗauka wani mugun abu mutumin ya gani, a hankali ta ja jiki waje guda a bakin titin banda ƙugi babu abinda cikinta ke yi mata, ga wani azabar ciwo da murɗawa da mararta ke yi mata tun safe sannu a hankali ciwon ke ratsa ta yana cin jikinta. Ta rufe idanunta bakinta ɗauke da sunan Allah, da sauri ta buɗe idanun ganin a wannan karan ma kamannin shi ya ƙara gittawa ta cikin idanunta. Ta marairaice fuska da gaske ya takura ta, bata san waye shi ba amma tunda ta fara shiga B.u.k kullum sai taga rukunin su _who is he?_

Ta ɗan yi murmushi kaɗan sanda ta runa farar fatarsa da idanunsa da kuma abin kunnensa, tana son ganin namiji ɗan gayu yana burgeta haka kurum. Sai kuma ta ɓata fuska sanda ta tuna Abbiey kullum cikin jallabiyya da hirami, wanda ta gani yana da bambanci da Abbiey ɗinta ƙwarai ko dan shi babba ne ya manyan ta? Ƙara rufe ido ta yi kamar alamar fuska ta ƙara gilmawa ta idanunta ta marairaice ta ce

"Kar ka hanani bacci, Uhm waye kai? Shaddarka mai kyau" Tunani ta fara to ina za ta je yanzu? Ga dare ya yi idan ta tafi Abbiey fa? Zai shiga damuwa saboda shi kawai zata koma gidan don shi ɗaya ta miƙe tana juyawa har zata shiga sai ta fasa ta nufin gidansu Mardiyya dake kusa da su. Tana shiga ta gaida babbarsu Mardiyya lokacin ana sallar isha'i kwanciya ta yi saman carpet idanunta rufe, sai juyi take a yanzu ba yunwar ke damunta ba tunaninta wanda ya yi tsaye a zuciyarta shi ne matsalar gashi bata san ainahin abinda ke faruwa da ita ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Yin duniya Mardiyya ta yi a kan Ridayya ta ci abinci amma ta ce Allahamdulillah ta son bawa Mar labari amma tana shakkar abinda hakan zai haifar.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now