Chapter 43

1.8K 74 11
                                    

"Beloved" Sadauki ya furta idanunsa zube a kanta, ganin tana jan baya hannunta dafe da cikinta daya girma sosai ya saka ya ƙara kusanta kansa zuwa gare ta, tana ƙokarin juyawa ta gudu ya saka hannu ya jawota zuwa jikinsa, abinda ya yi masa iyaka tare da yi masa shamaki daga rungume ta ya saka shi saurin sakin hannun Ridayya. Ciki! Shi ne abinda Sadauki ya gani har ya girma cikin haihuwa ko nacin abinci mene ya haɗa his fiance da ciki? Innalillahi!

Zuciyar Sadauki ce ta fara rawa tana wani irin yunƙuru masa har maƙoshinsa yake jin numfashinta, ya sake buɗe idanunsa da sukai laushi ya zuba akan cikin dake maƙale a jikin Ridayya,what does that mean? Did she cheat or what? Hatta ƙafafuwansa rawa suke suna neman gaza ɗaukar gangar jikinsa a karo na farko kuma kusan na biyu.

Murmushi ya suɓuce masa dukda cewa idanunsa a rine suke tana iya hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Kallon Ridayya kawai yake irin kallon dake nuna, I love you so much, the kind of crazy love that even in Ustaz's eyes she has never seen that. Har ya juya sai kuma ya sake tsayawa irin me ya sa zan tafi? Why should i do that? Ridayya ce fa? Ba zata taɓa cin amanar shi ba, ya aminta da ita aminta mai yawa amintar da har zuciya da gangar jikinsa sai da suka shaida hakan, murmushi ya dinga yi shi kansa bai san dalilin faruwar murmushin nasa ba.

"Wow! U look so beautiful shanshan kin sauya a idanuna sosai" yana magana yana ɗan hargitsa sumar kansa alamar ya fara fita daga yanayin da yake na Hamza zuwa na Sadauki.

Ya zubawa cikin Ridayya idanu domin tabbatar da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, idan cikin gaske ne mene haɗin budurwar da zai aure da cikin haihuwa? What bring her here? Me ta ke yi a Japan?

Ƙara matsawa ya yi wajanta ta girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her a gigice Ridayya ta ce "Stop it, Stop it Stop it Sadauki" jikinta duka rawa yake tsoro da fargabar yanayin Sadauki ya saka mararta riƙe wa, idan ta tuna cewa Abbiey na hanya kamar yadda ya ce sai ta ji kamar abinda ke rayuwa a cikinta zai fito zuwa duniya ne, bata san hawaye ke fita daga cikin idanunta sai da ta ji saukar yatsar Sadauki manuniya ya sharce hawayen ta ɗago ta kalle shi ya mata murmushin a hankali nunfashinsa na sauka da kyar a fuskarta ya ce

"Wai Shanshan wannan sabon yanayin fa? Bai dace dani ba na miki wani abu ne?" A taushahe ya yi maganar Ridayya ta kasa cewa komai bata san haɗa idanu da shi tsananin tausayinsa ke addabar zuciyarta, ta san ta masa laifi kuma laifi mai girma "Sadauki ka fahimta mana!" Ta furta a fusge tana ja baya ya bita ya ce "Me zan fahimta bayan abinda na fahimta yanzu? Ki barni kin wofintar dani saboda muradin ki yi karatu? Tunaninki ba zan bari ki yi karatu ba ko mene? And wannan guje-gujen na mene eh?"

"I am sorry very very sorry Sadauki "

"Sorry for what? Zan jira ki zan dinga dakon soyayyar ki a nan ɗina" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa da hannunsa ya ce "Har zuwa ƙarshen numfashina, bani nake son ki ba Ridha ruhi da zuciya da gangar jikina ke ƙaunar ki, bana son komai sai rayuwa dake kawai so nake ki riƙe hannuna mu yi rayuwa tare.....,"

"I am sorry Sadauki ka yi haƙuri don Allah...," matse kafaɗunta ya yi idanunsa a rine ya ce "What wrong with Shanshan? Hakurin mene na miki uzuri na fahimci cimma muradinki zan jira da gaske zan jira ki, so halitta ne kuma jarrabwa ce na jarabtu akan ki Shanshan kawai ni ina son ki"

"Ciki gare ni Sadauki ciki ne dani haihuwa zan yi, na haramta a gare ciki gare ni Hamza Sadauki "

Ba kansa ne kawai ya harba ba hatta zuciyarsa sai data girgiza tana neman rabewa biyu a tsakiyar ƙirjinsa, kalmar CIKI kawai yake masa yawo komai nasa yana warware ƙirjinsa na matse masa guri guda, murmushi ya yi mai kama dana masu jin tatsuniya a fusge ya ce "Ciki? Wasan banza kenan" Ta girgiza kai ta ce "Da gaske nake"

Ya tausasa murya ya ce "How? A gida an sani? A ina kika same shi? Kin san uban cikin?"

Ta yi shiru kawai domin tana da yaƙinin Sadauki ba zai fahimce ta ba, tana kuma shakkar faɗa masa cewa ta yi aure ne, cikin sunna ne maƙale a mararta. Sadauki yana da naci da taurin kai kafin ta gama yanke shawarar abin yi ta ji ya damƙo hannunta ya ce "Ciki Ridayya? Abinda ya kawo ki makaranta kenan?" "Ba zaka gane ba Sadauki Please let go of me kar ka saka na shiga fushin Ubangiji"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now