3 Dare

958 53 2
                                    

Ridayya ji ta yi ciwon da zuciyarta ke yi mata ya dawo sabu fil, cikin wani irin rikitaccen tashin hankali daya gama mamaye ilahirin lungu da saƙo na ƙofofin halittar ƙirjinta, wacce take ƙara kissima mata soyayyar Zameer a kullum.
"Kada ki nemi kashe ni da rai na Amma, kada ki ce zaki hukata ni ta hanyar da zuciya, gangar jikina ba za su ɗauka ba"
Ganin amma taƙi yadda ta kalleta, ya saka Ridayya sakinta tare da
juyawa ta kalli Zameer dake tsaye, idanunsa cike da hawayen daya gama ƙirƙirar su a wajan ta ce "Kalamanki kamar fitar dalma haka suke sauka a ƙirjina Amma, rabani da mijina kamar bayyanar ranar mutuwa ce, wallahi duk duniya ba wanda nake so sama da Zameer idan ki ka cire Mami, ina ji a jikina bayan bautar Ubangiji; Allah ya halicce ni domin na rayu da soyayyar Meer, me ya sa kuke ƙoƙarin kashe ni da rai na? Bayan ina numfashi? Kuna kallona na faɗa muku ina son shi mene ribarku idan kun rabani da shi"
Ridayya ta ƙare maganar tana jan numfashi a wahale, komai nata ya yi tsayiyuwar sojojin da suke tsaka da fareti.

Murmushin baƙin ciki da kuma takaicin halin Ridayya Junaid ya yi, duk yadda ya tursasa zuciyarsa wajan ganin bata ɓaci ba, a kan haukan da Ridayya ke yi musu a cikin asibiti abin yaci tura. "Makauniyyar soyayya ko? Ridayya anya baki haukace ba? Kin san kalaman da bakinki suke furtawa Amma? Ko giyar wake kika sha kin yi tsararo ki sauke mana ita a nan, ramin da kika haƙa kin yi
kaɗan ki faɗa ciki damu, sai dai ki kwashi turɓayar data rufe miki ƙofifin zuciyarki ki rufe kan ki da ita wallahi"  A hargitse Junaid yake maganar kamar zai kai mata dukan ɓarin makauniyya.

Baki Ridha ta buɗe, a ƙoƙarinta na son fayyace musu irin so da ƙaunar da Zameer yake mata, amma sun sanya audiga mai kauri tare da toshe kunnuwansu, tilas baza su saurayi kukan nata ba, balle surutanta a wanda suke musu kama dana sabon kamo.
  "Yaa Junaid wall...,"
Wani mahagon mari aka ɗauke Ridayya da shi, daga bahagon hannun daya jima bai duka ba. Mami ta rasa me zata furta akan Ridayya, da gaske duk wata kalma da zata yi futar mashi daga cikin bakinta ba zata yi kyau ba, abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba, bata so yin mummunan kalamai akan Ridayya, domin yin haka na nufin ƙara lalacewarta, tabbatacce ne kaifin bakin uwa akan yaranta.
“Ridayya!!”
Ta kasa faɗin abinda ta yi niyya, cikin hanzari kamar tafiyar hadari a saman gajimare ta fice daga cikin room ɗin.
Amma ta juya ta kalli Baba ƙarami dake tsaye yana nazarin yanayin da Bilal ke ciki, wanda kalaman Ridayya suka jefa zuciyarsa cike dake ɗauke da rufaffen kuma ɓoyayyen sirrin da yaƙi bawa kowa damar fahimta, sai yanzu da a nutse da kuma idanun basira daya saka Baba ƙarami yake wassafowa yana gina shi a tubali ma'ana.

"Ridayya ki ƙaddara silar mutuwar aurenki zai saka ki haɗiye zuciya ki mace, wallahi sai Zameer ya sakeki a yanzu...,"
"Assha! Assha ban so ki ka rantse ba, ina jiye miki kaffara musamman ta azumi" Baba ƙarami ya tari numfashin Amma da hakan. Ta rusuna a ladabce cikin girmamawa ta ce "Ka yi mini haƙuri da afuwa kada ka dakatar da ƙudirana na ceton Ridayya daga duhun rijiyar data zama shekararriya, karka hana ni ina son kawo ƙarshen alaƙar dake tsakanin su biyun" Baba ƙarami ya girgiza kai a hankali kuma ya nemi saman kujera tare da zaunawa akai, ya jima da fahimtar idan aka biyewa mata maimakon a gyara ɗaya sai goma ta ɓaci.

  Bilal zufar dake yankowa a saman goshinsa yake saka hannu a hankali tare da sharewa, dokawa zuciyarsa take da wani irin sabon sauti da bai taɓa jin irinsa ba a tattare da shi. Ya saba da bugun luguden da take masa a ko wacce da ƙika dake tafiya, ta dalilin tunanin Ridayya, al'amarin da ya gama addabar rayuwarsa ta kowacce siga. Sunanta kaɗai yana sawa halittar gashin dake kwance a saman fatarsa mimmiƙewa, tsigar jikinsa na tashi ƙirjinsa na dokawa da ƙarfin da yake kasa fitar da numfashi. A yanzu ma haka ɗinne Bilal kokawa yake da zuciyarsa wajan ganin bai juyawa ya kalli Ridayya da yanayin da take ciki ba, baya fatan ace hawaye ne suke fita daga kwarmin idanunta, ba zai jure ba, da gaske ba zai jure yanayin da take ciki ba. Juyawa ya yi da nufin barin ɗakin jinyar dake cikin asibiti jiri na kwasarshi kasancewar yana da kyakkawan jiki a buɗe ya saka hakan bai faru ba.
"Babban mutum"
Baba ƙarami ya kira Bilal, kiran daya dakatar da shi daga ficewa, yana tsaye inda yake. "Dawo ka zauna" Ya bashi umarni kai tsaye.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now