Anuty Kaltum ta ce "Alhaji Mansur me kake nufi da jaririyar ba ƴarka ba ce?" Baffa ya yi wa Anuty Kaltum kallon ki shiga hankalinki kafin ya ce "Ina nufin abinda na faɗa, wannan yarinyar da Fatima ta haifa a nemi ubanta wani wajan, bani da haɗi na jini ko gamuwar ƙwayar halitta, ita ɗin ba jinina na ba ce, I'll never accept her as my biological daughter, kuna iya neman ubanta wani wajan"
"Kam bala'i, wa kake da suna Mansur ko wa? To wallahi ƙarya kake idan ma shaye-shaye ka fara ka zo zaka mana maye a nan to yanzu zan dawo da kai cikin hankalinka, kana da yaƙini da tabbacin Fatima bata taɓa yin wani saurayi bayan kai ba, balle ka ce wani abu ko ka saka kalmar zargi a ranka, wannan kuma jaririya bata da wani uba daya shige kai Alhaji Mansur Rano, kamar yadda su Junaid su Zuhura suke ƴaƴanka, wanda ka yi cikinsu to haka wanann jaririya" Anuty Kaltum ta ƙare maganar cikin masifa da kumfar baki, ita daman faɗa ba nata bama siya take balle ya shafi jikinta da suke uwa ɗaya uba ɗaya?.
Baffa ya yi kicin-kicin da fuska kana ya juya ya kalli yaransa da suke tsaye a wajan ya ce
"Wa kika gani baƙi ko mummuna a nan cikin jerin yarana? Tunda nake haife-haife ba a taɓa haifar mini jariri mai munin halitta da baƙin kamar kalwa ba sai wannan mummunar jaririyar, babu ta inda na zama ubanta ba zan taɓa zama ba" Anuty Kaltum ta ce "Ok sai ka faɗa mana waye ya amshi budurcin Fatima a daren aurenku?"Baffa ya ɗaga kafaɗa ya ce "I am the one, but this baby will never be my daughter" Yaya A'isha dake tsaye itama ta ce "Sai a yi DNA TEXT, a nan gaskiya zata fito"
Baffa ya ce "Ba DNA TEXT ba, ko cikin yarinyar zan ƙara a sake haifar ta, ba zan taɓa amsar ta, ku je ku nemi ƴar'uwarku ta yi muku explanation uban yarinyar sai a kai masa, amma....,"
Maruka aka shiga saukewa Baffa ta ko'ina, ya runtse idanunsa ganin yadda aka mare shi a kan idanun yaransa. Rai ɓace Hajiya ta ce "Ba shakka, dole ka nuna mini ka isa wannan shi ne kalar adalci da halaccin da zaka yi wa Fatima? Yarinyar da sadaukar da soyayyarta ga ƴar aminiyar babarta, ta haƙura har sai ta girma ta kai shekarun da iyayenta suka ɗiba na girmanta, a bayanka; wanne kalar samari ne Fatima ba ta yi ba, wanda suka fika kyau, arziƙi na saba, cancanta? Amma duk ta saka kamar ta share su, tana ganinsu tamkar mata kai kaɗai ta kewa kallon namiji, wanda zai wadata mata da komai? Zai bata farin ciki, ta dinga jin kalaman soyayyar su, kamar busar sarewar Audu" Hajiya ta share hawayen idanunta ta ce"Cikin daka ƙwallafa rai a kan shi, ka ɗauki burin duniya ka saka wa cikin, har kake cewa duk abinda Fatima zata haifa maka tabbas mai ƙashin arziƙi ne, Mansur yau a gaban iyayen Fatima akan idanun surukarka kake aibata abinda ɗiyarta ta haifa? Kake ƙoƙarin liƙa wa ƴarta kalmar zina? Ina tunanin ba abinda Fatima ta haifa ba ko wata ta ɗakko daban zaka saka hannu bibbiyu ka riƙe, Mansur! Mansur! Wallahi ka haukace"
Baffa ya ce "Lafiya lou nake, wallahi Hajiya ina cikin hankalina a nemi uban yarinyar, matata Fatima kuma a mayar mini da ita gidana"Jama'ar wajan sun fi yarda Baffa ya samu matsala da tunaninsa, duk wani wanda ya san Baffa ya san labarin soyayyarsa da Fatima-zahrah bashi da wani sukuni sai nata, har ya yi aure jinsa yake empty without his Fatima Batool. Ammi har cewa take ya je ya ganota kar tunaninta ya haukata mata miji cike da zulaya take furta haka, sai kawai ya harereta irin ai na fiki sanin me nake.
Baba ƙarami yayan Baffa ya jinjina kai ya ce
"To ya kake so a yi kenan Mansur?" Kai tsaye ya ce"Kawai a nemi uban yarinyar, wallahi tamkar na saka hannu na murɗe wuyanta haka nake ji, wannan ai baƙar kadara ce, annoba, kuma wake ɗaya mai ɓata miya Fatima fara ce tas, ni ma fari ne tas, yarinya kuma da sharɓeɓan leɓe harshe a waje? Hanci zai yi goman nawa? Jibi suma duk saman fatarta? Wallahi ƙila aljana ce ba" Murmushi kawai Baba ƙarami ya yi ya ce "To wa za a nema matsayin uban nata? Ko zaka taya mu lalube ne Mansur?" Baffa ya yi shiru.
"Wanne suna kake so a saka mata?" Aka faɗa a taushashe cikin sanyin murya, Anuty Kaltum ta kalli wanda ya yi maganar domin tunda ya zo wajan gabaɗaya maganar da ya yi ba takai huɗu ba. Rai a matuƙar ɓace ta ce "Tambayi mahaukacin ubanta gashi nan" A fusace Baffa ya ɗaga hannu zai kifawa Anuty Kaltum mari, Mai ran ƙarfe ya yi saurin riƙe hannun. Anuty Kaltum ta fashe da dariya tana tafa hannu ta ce
"Basshi, basshi ya taɓa ya taɓa wa kansa masifa da bala'i, da matar soja kake magana, wallahi sai na saka a ɗaure ka ka yi life in prison, kaf zuciyarmu babu faƙiri matalauci, kuma mai ƙarancin ilimin addini, aikin banza nifa daman tun farko wannan mutumin bai mini ba"
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...