Page 6

565 45 8
                                    

Ruwan da Ridayya ta ji ana sheƙa mata mai sanyi ya haddasa farfaɗo war ta daga suman hucin gadin da ta yi. "Ɗinkina zai farke, ka tausaya mini ba zan iya ba wayyy...,"
Zainaba ce ta jijjiga Ridayya da ƙarfi ganin kamar bata gama dawowa cikin hayyacinta ba cike da tausayi na halin da yarinyar ta saka kanta ciki ta ce
"Ridayya lafiyarki lou? Me ya sameki na gan ki a yashe kamar gawa? Ina shi mijin naki ya bar ki haka? Wacce kalar rayuwa ce wannan?"

Maganar Zainaba ya dawo da Ridayya cikin nutsuwarta ta fahimci ba Zameer ne a kusa da ita ba balle ta saka ran samun kulawa daga wajan shi tunda shi ya cillata halin da take ciki a yanzu. A karo na farko tun kafin auren su, da bayan auren su ta ji wani irin mummunan faɗuwa da ladamar abinda ya shuɗe sun dirar matar a zuciya ta ji babu abin da bata ƙauna irin tarayyar aure, rashin mafita da yar da zata fahimtar da Zameer ɗin ya saka take biye masa ba son ransa ba, yana nuna mata ƙarfin ikon shi akan ta matsayin miji.
"Allah na tuba, na tuba Allah ka yafe mini zunubin dana aikata a baya yake bibiyata na ji a jikina, idan har haka ne gwara mutuwa da rayuwa a gare ni" Zainaba ta yi saurin rufe mata baki, ita ma hawaye ne ke sauka daga cikin idanunta kamar yar da Ridayya ke kuka mara sauti mai cin zuciya.

"Komai ya yi zafi maganinsa Allah, Ubangiji baya taɓa ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, ba kuma ya ɗorawa bawa ƙaddarar a domin baya son shi ba, sai dai gwada imaninsa da Tauhidi" Ridayya bata fahimtar maganar Zainaba saboda tsoran daya rusketa da jin yar da ruwa ke gudu ta ƙasan cibiyarta. Zainaba ta yi saurin toshe hanci ta ce
"Ridayya warin mene wannan?"

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shikenan" Ridayya ta furta a raunace ganin yadda ɗinkin ya farke wajan ya yi jajur kamar yanzu ne aka yankata, ruwan dake zuba na fidda warin. Zainaba ta miƙe ta ce "Zama ai bai kama mu ba, dole a koma asibiti ki kira ƴan gidanku ki shaida musu" fahimtar kuka a rahama yake ya sa Ridayya bata damu da yadda hawayen ya tsaya mata ba, zuciyarta ta bushe tana mata wani irin suya, ta ƙura wa wajan ido numfashinta na fuska. "Babu wanda zan iya kira, domin na bar su"

"Kin bar su kamar ya?" Ridayya ta girgiza kai ta ce "Aurena za su kashe mini ta ƙarfin tsiya, suna son bawa Abbiey ni, na zaɓi mijina domin shi ne Aljannata" Baki sake Zainaba ke bin Ridayya ta ce "Kuma kin tabbata lafiya kike, ma'ana babu Aljanu a jikinki"
Murmushin takaici wanda ya fi kuka ciwo Ridayya ta yi.
"Idan ina da aljanu kawo yanzu da kin sani" Zainaba ta ƙara cewa
"Kuma babu wani asiri da tsinannan can ya yi miki?" Ridayya ta ɗaure fuska duk da halin da take ciki ta ce "Ki dai na zagin mijina cin mutunci ne wannan"

"Na ci uwar mijin ba mai ha ya ji, na ci shi ƙandas, na bisa da gudu aikin banza aikin wofi yanzu na ƙara tabbatar da bayan ƙuruciya har da rashin komawa ga Ubangiji da bijirewa iyaye" Zainaba ta ce
"Kin taɓa ganin inda iyaye suka mutu aka sauya wasu? Zaka iya sauya komai banda iyaye da dangi, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, iyaye ba abin wofintar wa bane Ridayya, a yau kika faɗi kika mutu jimawar duniya shi ne ki arba'in, zai yi sabuwar amarya ta tare a ɗakin da kike gadara da sunan ɗakin miji, gidan aure"

"Duk lalacewa GIDAN AURENA NE" Zainaba ji ta yi kamar ta yi wa Ridayya mugun duka, sai dai tausayinta ya danne haushin da take ƙunsa mata ta ce "Kira wannan kamilin ko shi ne ya kai ki asibiti" Ridayya ta yi shiru yanzu ta kira Abbiey ta ce masa me? Ustaz ina son ganinka?.
"Kira shi mana Ridayya ba lokaci idan ba haka ba kina kallo za ki ruɓe" Ridayya bata da zaɓin daya shige kiran Abbiey ɗin nata, idan kowa zai guje ta babu shi. Abin mamaki wayar baya tafiya tunda take bata taɓa kiran layinsa ya dawo mata ba sai yanzu. "Kiran baya tafiya" Zainaba ta yi shiru ta ce "Gashi babu kuɗi wajena, amma ina dubu biyar ɗin dana ba ki?" A hankali ta ce "Ya amsa?"

"Waye?" Cewar Zainaba duk da ta gane ta ce "Rayuwata" wata lailayayyiyar ashar Zainaba ta ƙunduma ta ce "Lahirar ki dai makashinki shege da munafukan idanunsa, dake ke makira ce uwar son miji shi ne kika kwashe kuɗin kika bashi? Ohhho ni Zainabu Abu ina ganin rayuwa a wannan gidan Munafukin mijin, Allah ka nuna mini sanda Ubangiji zai jarabci wannan mugun ya nuna mini ranar da zai ga amfanin matarsa"
Ridayya jin Zainaba take, ba don ta yar da ba ta ce
"Akwai wata Atamfa valisco da super was a akwatina idan za a samu masu siya, ki siyar mu je asibitin" Zainaba ta miƙe.

Neman duniya babu atamfofin nan sun yi ɓatan dabo hankalin Ridayya ya tashi domin sune kawai kadarar daya rage mata sai katifar da take kwana akai. Duk atamfa ɗaya ta kusa dubu hamsin haka Abbiey ke bata baya mata ƙaramar suttura. Waye zai ɗakko har ɗakinta. Zainaba ta ce
"Uhm, lokaci"
Fita ta yi babu jimawa ta dawo da kuɗi a wajanta ta dafawa Ridayya ruwa ko zani baya zama jikinta haka ta rufe wajan ɗinkin dauɗa na taso mata ta yafa ruwan. Ruwan shayi mai kauri Zainaba ta bata ta kasa sha ganinta take kamar kayan cikinta zai fita, ta dinga kiran Zameer a waya shiru baya ɗauka Maman Hajjo ta kwace wayar ta ce "Uwar me zai mana banda ƙaryar da zai shirya miki, napep na waje mu je" da ƙyar ta shiga napep suka rufe gidan tare da nufar asibiti,suka samu Nas Hajjara cikin sauri aka yi wa Ridayya komai a account ɗin Nas Hajjara aka cire kuɗi, a nan kuma Ridayya ta kwana washegari da dare aka sallame su da zummar nas Hajjara zata dinga zuwa duba ta, har sannan Zameer bai kira waya ba.
Gama shan shayinta kenan bayan sun yi sallama da Zainaba Zameer ya shigo a gigice yana zuwa ya saka hannu ya ɗauke Ridayya da mari za ta yi magana ya sake ɗauketa da mafi ya ce "Ni kika mayar mahaukaci a unguwa? Kika rufe gida kika ta fi yawon duniya abinki? Har ki kwana ki yini bin maza kika fara?"
Ta kasa magana balle kuka bakinta ya kumbura tare da ƙara tsine ya sauya mata kama abinka da baƙar mace mai rangwamen kyan halitta muninta ya fiddo fili.
Ganin yar da take jan numfashi jikinta ya fara rawa kamar mai jijjiga ya saka Zameer yin ƙasa da murya ya ce.
"My love, ban yi da niyya ba, na gigice na zama mahaukaci a wajan nemanki da gudun kar na rasa ki, tsananin farin ciki ya saka na mare ki ba tare dana tuna ba ki da lafiya" Rana ta farko da ya ce "My love, masoyiyata" sai ta nemi duka zafin marin ta rasa ta kasa cewa komai.
Ya tausasa murya ya ce
"Haba mana, ki rama idan ba ki haƙura ba" Ridayya ta ce "So kake Allah da mala'ikunsa su yi fushi dani?" Ya kashe mata ido ya ce "Well is allowed"
"Baka tambayi ina na je ba, baka kuma ka neme ni a waya ba ai kasan tana wajena" Ya shafa kai ya yi mitsi mitsi da ido kafin ya ce "Ohh ina kika je?" Ta ce "Asibiti, daka gamar biyan buƙatar rai ka fita ka bar ni yashe a sume" Kamar bai sani ba ya zare ido ya ce "Suma kikai? Ayya"
Kafin ta yi magana sun ji an ce "Sweetheart" da sauri Ridayya ta ɗaga kanta taga Khairy tsaye daga ita sai three qauter na Zameer da kuma half vest iya ƙirji.
"Me kika ce Khairiyya?"
"Sweetheart na ce"

"Yayan naki ne sweetheart? Wandonsa ne a jikinki fa? Kalli rigar da kika saka ai da haka kika fito zai fi"
Khairy ta fara yunƙurin cire vest ɗin tana faɗin "Ok bari na cire idan hakan zai fi" Zameer dai na zaune yan ta son ya juya ya kalli Khairy kaifin idanun matar tasa ya hana "Fitar mini daga ɗaki" Khairy ta ce
"Su ɗaki manya, kar fa ki manta gidan miji ne wannan ba gidan uba ba, a yanzu zai iya tafa miki rasit ki yi gaba ni kuma zama daram mai naƙuda ta samu katifa don haka ki saurara mini kar ki nemi ɗaga mini hankali"
Ridayya ta kalli Zameer ta ce "Kana jin mai ƙanwarka ke faɗa mini?" Ya juya ya kalli Khairy daidai lokacin data kammala cire vest ɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Wanne irin tashin hankali ne "Na shiga uku Khairiyya kina da hankali? Kalli ƙirjinki a bayyane kalli yar da yayanki ke binsu da ido"
Kasa magana ya yi ya miƙe tare da ficewa daga cikin ɗakin, wani irin kishi ya turnuƙe Ridayya ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta ta haƙura har lokacin bacci ya yi bai shigo ba, ga sauro kamar ya cinye Mutum.

Ganin ba a kawo nepa ba ya saka ta kunna hasken wayarta domin rage sauro. Cikin bacci kamar kuma ido biyu taga an zuro hannu tare da ɗauke wayar kafin ta motsa an yi waje da gudu ta laluba bata ji Zameer ba ta saki ihu tana faɗin "Wayyo jama'a ɓarawo.....

Ku yi haƙuri da jina shiru bana jin daɗi ne, wannan ma da ƙyar na yi ya ɗan yi short da yawa.A ci-gaba da bibiyar labarin RIDAYYA na MUNAFUKIN MIJI😢😭

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now