Page 37

2.6K 130 70
                                    

Bayan ya fita daga gidan bai samu zarafin shiga motarsa ba, texci ya shiga zuwa tasha suna tafe Idanun Ustaz rufe zuciyarsa na bugawa da matsanancin ƙarfi.

A hankali a fili cikin sautin da shi kaɗai zai iya ji ya furta.

“Ridha, you are my choice, always. Even if fate brings me a fated mate, my heart will remain yours”
Ya sauke numfashi yana jin komai na fice masa a rai,hukuncin da Umma ta saka ya yanke daidai yake da tsaiwar numfashinsa wanda hakan ke nufin rayuwarsa na dab da zuwa ƙarshe.

Love is nothing but a destiny; dole kowa ya yarda soyayya ƙaddarar ko wanne mai rai mai zuciya ne a ƙirji. Ƙaramar wayarsa ya ji tana ringing ya kasa motsawa balle ya duba yaga waye? Kawai ƙasar yake son bari amma komai nasa yana gida bai san ya zai yi ba, ya koma ne ko ya tafi haka?

Wayar ya zaro ganin Baba ƙarami ya saka cikin nutsuwa da ladabi ya ɗauki kiran, yana mai yin shiru tare da sauraren abinda Baba ƙarami yake cewa can ya nisa ya ce.
“Huh! In sha Allah”

"Turn the car driver"

Cikin sauri driver ɗin ya juya lokaci zuwa lokaci yana juyawa tare da kallon Ustaz ganin yadda fuskarsa ta yi jajur har wani ruɗi-ruɗi take gabaɗaya jijiyoyin kansa sun tashi. Yanayin shi bai bari an gane ya yake ciki ba zafin ransa dai a bayyane yake.

Umma ta miƙe tsaye tana juya farar takardar dake naɗe a hannuna ta ce "Allahamdulillah! Allah abin godiya sai yau zan yi cikakken bacci tun bayan auren ƙaddarar nan bana runtsawa da kyau. Yadda ka yi shekaru har 43 ba zaka ƙare rayuwarka a bazawara ba, ina son ka yi aure na ƴanci ka bawa zuciyarka da gangan jikinka abinda ko wanne namiji yake buri, buƙata, da kwaɗayin samu. Yaro gabaɗaya ya gantalar da rayuwarsa akan bautawa yarinyar da bata son ciwonsa ba, bata san damuwarsa ba, sai da ruwa ya ƙare wa ɗan'kada za a ƙallaga masa ita banda ƙaddara da naci da kuma maitar soyayya wallahi Babban mutum ya fi ƙarfin auren Ridayya ta ko wacce siga" Ta faɗa rai ɓace fuskarta kuma na bayyana tsantsar farincikin da take ciki.

Baba ƙarami ya ƙarasa shiga ciki jikinsa duka a sanyaye tunanin makomar Muhammmmd kawai yake domin Allah ne shaida yana yi wa Ridayya son da shi kansa bai sani ba tun yana rufewa da murfin zuciyarsa har murfin ya gaza ɗaukan girman al'amarin rauninsa a kan ta ya fid da kan shi.

"Kin yi farincikin?"

"Kamarya?"

Baba ƙaramin ya zauna ba wasa a fuskarsa ya ce "E, you have to tunda kin yi abinda kike so yana da kyau ki zuba ruwa a ƙasa ki sha ko kuma ki kunna kiɗa ki taka rawa, kin saka an saki ƴar ƙanina kin mayar da ita bazawara"

"Wannan shi ake kira ga fara sa banga ƙaho ba, bazawara ta nawa kuma? Ba a zawarcin aka maƙala masa ita ba? Sanda take budurwa wane a cikinku ya yi tunanin haɗa auren su? Sai yanzu ta yi aure ta sha baƙar wahala miji ya ci ubanta son ran shi ta haihu ya gama kwashe albarka da ni'imar jikinta sannan kuka tuna da Muhammmmd ko? Uhm ni da bana ƙwai na sai da zakara kuma wallahi Babban mutum ya zama kwankwason jimina mai wuyar shafawa, ya ma ƴarku nisa"

"Ni kike zagi Hadiza?"

"Ni? Yaushe?" Umma ta ce tana gwalo Idanu.

"Ridayya bata da uban daya shige ni, kamar yadda Muhammad-Bilal ba shi da uban daya shige ni Alhji Tahir Rano. Kin yi playing role ɗinki da kyau amma ki sani Ridayya ba za ta yi zawarci ita kaɗai ba, dole ne su yi tare da surukarta idan kuma ta samu miji ta bar ki a titi mafi mushkila"

"Me kake nufi Alhji Tahir?"

"Ina nufin abinda kika ji Hajiya Hadiza. Bani takardar domin nasan saki nawa zan iya miki"

Tana karkaɗa ƙafa ta miƙa masa cukurkuɗaɗɗiyar takardar dukda ƙasan zuciyarta fargaba ce fal ita kam ina takama tsofe-tsofe da ita da yin wani zawarci?. Baba ƙarami ya buɗe paper ɗin a hankali ya fara dubawa gumi na yanko masa all over himself bai taɓa zato ko tunanin hakan ba, bai taɓa kawowa a ransa Ustaz zai yi saurin saduda ba har haka, girman abin da yake karantawa tamkar zunubi ne a wajan shi hakan ya saka Baba ƙarami rufe paper ɗin ya yi shiru na wani lokaci yana jan numfashi.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now