Chapter 46

1.4K 74 32
                                    

Jaririn shima ya zubawa idanu ya ce "Sun miki kama da wani ne?" Umma ta girgiza kai ta ce "Bana jin kaf RANO'S FAMILY akwai mai kyawun halittar jariran nan, Ustaz ne kyakkyawan ciki kuma sun ninka shi a kyau da komai yana jariri bai samu kyansu ba wallahi wannan girmansu abin kallo ne" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce

"They're blessed, Allah ya yi musu albarka ya ƙare haɗa kan iyayensu ya kau da idanun maƙiya akan su"

"Amin, yaran waye?" Umma ta tambaya cike da zaƙuwa saboda kyawun yaren ya gigita ta ainun ya sake murmushi ya ce

"Ki fara saka musu albarka tukunna tunda kin yaba" Umma da take jin wani irin matsananci daɗi ga wani farinciki daya saukar mata lokaci ɗaya wanda hakan ya faru ne sanadin ganin zuƙa-zuƙan jaririn guda uku sanye da kaya iri guda kuma kamanni guda ta ce "Wallahi tun kafin na furta komai na sanya musu addu'a tare da addu'ar Allah ya tsone idon maƙiya ya yi musu albarka, ya ƙara so da ƙauna a tsakanin iyayen su, ma sha Allah tubarakallah har cikin zuciyata nake jin ƙaunar yaren" yadda take nuna farinciki a fili zai nunawa mutum zahirin gaskiyar da take faɗa tsakani da Allah take son yaran kamar yadda ta furta.

Baba ƙarami ya sauke numfashi idanuna akan matarsa yana jinjina girman rabo, kuma duk inda jininka yake sai jikinka ya baka ya kasa furta komai deep down na zuciyarsa addu'a yake Allah yasa haihuwar yaran nan ya kawo daidaito tsakanin uwar yaran da kakarsu ya zama silar kwanciyar hankalin duka familyn bakiɗaya. Ya nemi waje tare da zama saman kujera yana girgiza ƙafa shi kansa yaran Ridayya da Ustaz sun jijjiga shi kyan yaran ya bashi mamaki dukda ba'a mamaki da ƙudirar Allah.

"Baka faɗa mini yaran waye ba? Ni dai na gama tunani daga dangina har naka babu mai haifar kyawawan yara kamar su" Baba ƙarami ya juya ya sake kallon yaran a hankali ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, Mardiyya kawai nake saka ran zata haifawa Muhammad kyakkyawan yaro kamar shi ko fiye da shi"

"Me ya sa kike tunanin namiji zata haifa kuma kyakkyawa kamar gwarzon ɗana" ta matsa kusa da shi ta ce "To ai haka ne kuma juma'ar da za ta yi kyau Hausawa suka ce tun daga Laraba ake gane ta, Mardiyya nada kyau haka Babban mutum kuma an ce abin cikin ƙwai yafi ƙwan daɗi kaga dole ɗan za su haifa shi da Mardiyya ya zama kyakkyawa" Baba ƙarami ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "Haka ne kam, kina da taki gaskiyar"

"Ni sai naga kamar baka ƙaunar yarinyar nan baka mayar da hankali akan lamuranta karka manta daughter-in-law ɗinka ce fa" Cikin sauri ya juya ya kalleta yana waro idanunsa waje ya ce "A'a karki mini sharri matar, ai jinin ka wuya za shi you're just like a drive mu duka passengers ne a tafiyar nan sai inda kika ajjiye mu, nina isa naƙi zaɓin uwar gidan Tahir" ita dai duk bata gane me yake son cewa ba, don haka ta tattara maganar ta ajjye waje guda. "Ki mini wata alfarma ɗaya mana Hadiza"

"Wacce alfarma?" Ya fito da A.t.m guda biyu ya ajjiye mata kana ya nuna mata jariran ya ce "Haɗaɗɗun kayan barka nake so ki haɗu na Triplets masu kyau na gani na faɗa, komai da kika sani na yara ki haɗu" Umma ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Wannan kam ai ba alfarma bace ko su waye waɗannan na san suna da muhimmanci a rayuwarka sosai. Zan wa wata friend ɗina magana da take kawo kaya irin wannan daga waje sai na yi mata list na duka abinda muke buƙata, sana'arta kenan ai" "To madallah ba damuwa a yi hakan"

"Uwar yaran fa?" Ya ce "Me fa?" Ta ce "Ina nufin me za a siya mata?" Baba ƙarami ya yi shiru can ya girgiza kai ya ce "Iya yaran dai kawai"

"A'a ba za a yi haka ba, uwar kam ai ta cancanci a yi mata ni zan haɗawa uwar da kuɗina kaga sai na kai daga nan naga yaran so ma sha Allah"

Yana miƙewa saboda kiran sallah ya ce "Lallai to muna godiya" har zai tafi ta ce "Don Allah yaushe ɗana zai dawo gare ni ne? Idan fushi yake wallahi hukuncin daya ɗauka ya yi yawa ina jiye masa fushin uwa Baba ƙarami, yana da kyau ya dawo kafin matarsa ta sauka ga kuma hakƙin matarsa" A hankali ya ce "Zai ba ki mamaki ne soon zai dawo ki shirya tarɓa ta musamman domin ya yi aure a inda yake"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now