Page 25

1K 52 10
                                    

"A'a ke za ki raini ɗanki ba za ki mutu ba, kin ji?" Cewar Hanne wacce ke riƙe da babyn. Ridayya ta rufe idanu ita kaɗai tasan zafin da zuciyarta ke yi mata ga jinin da yaƙi tsaya mata da ƙyar ta riƙe hannun Hanne ta ce

"Mene ya yi saura a rayuwata? Gwara na mutu maybe nawa farin cikin sai a lahira zai tarbe ni" Idanunta rufewa suke sosai jikinta na rawa har yanzu tana riƙe da hannun Hanne.

"Matar Giɗaɗo... Matar Giɗaɗo" Shiru Ridayya bata amsa ba, hakan yasa hanne rikicewa ta kurma ihun daya jawo hankalin jama'ar gidan da suke ta ɗauki babu daɗi su da su Khairy.

Abinda tunda yake bai taɓa ji ba a tsakanin shi da Ridayya shi ya ruski Zameer, mummunan faɗuwar gaba wani abu dake nuna ban shirya rasa ki ba shi ne yake ji yana matse masa zuciya. Ganin idanunsa ya sauka a kan jaririn dake hannun Hanne ga Ridayya a kwance ga jinin dake zuba ta jikinta ya saka ya ƙarasa wajan da sauri ƙuri har lokacin yana kallon halittar Ubangiji wacce kamar a kan Jaririn na Ridayya aka gama kyau, wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo.

"Ke Hanne wannan yaron fa? Ina kika same shi?" Domin shi zaton shi ko jaririn da Khairy ta kawo ne ya yi masa kallon tsoro da farko? Wancan baƙi ne yanayin halittarsa har ta ɓaci sosai ga shimfiɗeɗen baki ƙaton goshi kamar irin yaran ruwan nan wannan kuma zaka iya cewa haihuwar Larabawa ne irin usul ɗin nan.

"Matarka ta haife shi yanzu fa Giɗaɗo, kaga da mun yi aure da tuni ni ce na haifa maka wannan kyakkawan babyn" Mamaki ya kusa kashe Zameer sai ya dake  ya kama Ridayya ta yi saurin ƙwace hannunta da ƙyar ta buɗe baki ta ce

"Karka taɓa ni, Hanne kar ki kuskure ki bashi ɗa na don girman Allah"

Zameer ya ja tsaki sosai bai tsaya jiran me zata ƙara cewa ba ya sunkuce ta ya yi waje da ita zuwa can shargalan asibitin da suke da shi a gefen ƙauyen Batsari. Hanne ta rungume jaririn a ƙirjinta tana jin ƙaunar yaron na ratsa ta, dukda ta san zafin ciwo ya saka Ridayya cewa ta bar mata shi amma da gaske take ji inama ta bata shi? Amma ya za a yi mummuna kuma baƙar mace ta haifi wannan yaron?

"Ikon Allah" Hanne ta furta a fili. Ta juya ta kalli yaron da aka yasar a ƙasa yana ta tsala ihu da alama shima bai jima da zuwa duniya ba, ta juya ta kalli Iyatu ta ce

"Haba Iyatu kun bar yaro yana kuka a ƙasa? Akwai karara a gidan nan fa" a harzuƙe Iyatu ta ce

"Me ɗin zan taɓa? Wannan halittar Allah ya sauwaƙe, uwar Giɗaɗo ma bata taɓa shi ba sai ni da nake kishiyar uwarsa? Ai idan kin ganni a lahira wallahi kai ni a kai, gidan da kowa gashin kansa ya ke ji ya je can ya gama ta zubar ɗinsa a kawo shege ki ce na taɓa? Zunubin zan taɓa Hanne kema da zan ba ki shawara da kin haƙura haka nan kin yi auren ki, domin Giɗaɗo ba irin arziƙi bane tun yana ɗanƙaramin shi yake ƙoƙarin hakkewa yaran ƙauyen nan da gayya Malam ya kai shi bara ba? Ashe iskanci kawai yake zubawa a can birnin Kanon"

Wuff iya mahaifiyar Giɗaɗo ta fito daga ƴar bukka tana riƙe zani dake neman kuncewa ta ce "Baƙin ciki kike da ɗaukakar Giɗaɗo ya je birni ya yi ilimi na boko ya nemo mace mai ƙashin arziƙi ai ya bani labarin komai nan da ɗan ƙaramin lokaci jirgina zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki" Sai kumfar baki take yi ita ɗaya.

Iyatu ta buga cinya tana ajjiye abin kaɗin adudiga tare da yin shewa da tafi ta ce "Anzo wajan daidai wajan ma, ai ba girinrin ma ta yi ma, idan kuma kaga baƙin maciji ko baƙar leda ka gani ka shafawa hanyarka lafiya,ina ƙoda ina romansa?...," Wata shewa Iyatu ta sake yi tana juya ɗuwawu ta ce

"Riiiiiiii arziƙi kashi idan irin wannan arziƙin dana gani yau an kawo muku shi ne arziƙi to umma ta gaida assha, wai shi ɗan gidan mai dallla ne ko me?" Kafin ka ce me tuni sun hargitsa ɗan gidan nasu Hanne ta lallaɓa ta gudu da jaririn Ridayya zuwa gidansu domin ba zata iya da wannan azabar tasu ba, ko kunyarta sam basa ji.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now