Page 36

1.5K 97 49
                                        

“coward” ya ce yana ɗage mata gira da kashe Idanu ganin yadda jikinta ke rawa kamar ba a taɓa ya yi mata abinda ya yi yanzu ba, he just gave a little light kiss. Amma ya lura jikinta sai rawa da ɓari yake ta rufe Idanu kamar bata taɓa jin abu makamancin wannan ba.

Ya dungure mata kai ya ce "Lazy wife, buɗe idanun" Ridayya ta kasa saboda da wani dake masa yawo saman jikinta yana kai mata saƙo na musamman da ban kuma. Wanda a duniyarta bata san da shi ba, hatta babban yatsarta rawa yake wai Little? Abinda ya yi mata ya fi ƙarfin a kira shi da haka yin duniya Ustaz ya yi ta buɗe idanunta amma taƙi sai wasu hawaye da bata san na menene ba suka fara bin gefen hawayenta.

"Kuka Ustaza? To shikenan a fasa tafiyar" Ta yi saurin girgiza masa kai tana ci-gaba da shassheƙar kuka na rashin dalili abinda ya yi mata ya tsaya mata curr a zuciya.

Ya ɗagota zuwa gefensa tare da riƙe hannayenta duka biyun ɗayan ya tallafo haɓarta yana zubawa fuskarta Idanu da gajiyayyun idanunsa a hankali ya ce.
"Kukan fa? Na mene?"

"Why Abbiey?"

Ya juya Idanu yana ƙara mutuwa da kyau gudun kar ƴar mitsitsiyyar yarinya ta birkita masa lissafi. Dukda ya gane sai ya basar ya ce
"Me?"

"You ki....,"
Sai ta yi shiru tana shagwaɓe fuska still taƙi kallonsa kamar yadda yake son nutsa ganinsa cikin ƙwayar idanunta da son gano ai nahin abinda ta ji game da hakan.

"Uhm za ki me dalili"

"Me ka ce?"

Ya matse hannunta dake cikin nasa tare da yin ƙasa da bakinsa daidai kunnenta numfashinsa na sauka ya ce.

“Play the role of my wife and be my children's mom Mimi” Ta yi shiru sai duk ya damu da shirun nata, kuma a ɗabi'ance hakan ya yi mace mai alkunya a kamata kuma hakan damuwa ce a gare shi, ko ABBIEY ɗin zata ce yana son jin muryarta. Da ita ɗinne kawai ƙofar zuciyarsa ke buɗewa yake jingina da ita ya yi hirar daya jima bai yi da ita, shi kawai yana son ta kama hannunsa ta ja shi zuwa rayuwarta da kanta, samun damar haka zai bashi ƙarfin qwiwar share dukkan wani damuwa da baƙin cikin data wanzu da shi tsayin shekaru, zai bata cikakkiyar dama a matsayinta na matarsa, zai share mata hawayen data daɗe tana zubar wa. Babban rainonsa yadda zuciyarsa taƙi masa adalci wajan buɗewa ta faɗa mata ainahin menene SO da ƘAUNA da kuma bambancin da suke tattare da shi game da BIRGEWA so yake ya samu damar da zai faɗa mata dukkan abinda yake ji a zuciyarsa game da ita, sai dai ƙaddarar shi kenan zurfin ciki kuma a kan abinda ya fi so da bawa muhimmacin ya fi ganewa ya yi komai a zahiran ce ko za a fi fahimtar yaran nashi.

"Can you? Za ki iya?"

Ya maimaita a hankali ta buɗe idanunta ta kalli gefen fuskarsa ya riƙo ta ya ce

"Ƙwayar idanuna za ki kalla" Ta girgiza kai.

"Ok fine an fasa zuwa ko'ina ma"

"Ka yi haƙuri Abbiey ban iya ganin Idanunka" ta faɗa a kasalance wani abu na yunƙuro mata.

"Za ki iya Ustaza nutsu" Ya riƙe kafaɗunta duka biyun yana gyara zaman shi a gadon daya gama  cukurkuɗa shi da ita. Ya matsa gare ta sukai kusa da juna speaking calmly ya ce

"Rufe idonki" Ta yi yadda ya ce "Ja numfashi" Nan ma ta yi ya ce "Ok breath out" a hankali ta sauke numfashi zata buɗe idanun ya ce.

"Noo, wait a moment ɗan jira" Ustaz ya jima yana kallon fuskarta ƴar jaririyarsa yau ta girma har ta haifi Bilal, wanda da Allah ya ƙaddara a ɗan shi zai zo, lallai wani baya haifar wani rabo kuma ajali. Idan rabo ya rantse sai a rabo da juna a je wajan wani a haifa masa, Ubangiji ya sanya yana da rabon samun zuri'a da Ridha.

"Buɗe Idanunki, kai tsaye ki kalle ni Ustaza" ya ce yana riƙe fuskarta da duka tafukan hannunsa.

Kamar mai shirin ganin sabuwar halitta haka ta buɗe idanunta wanda kai tsaye suka samu gurbin sauka a cikin idanun Ustaz, wani abu ta ji ya tsarga mata a zuciya wanda ya sanya halittar ƙirjinta buɗewa da kyau tana fahimtar wani abu na musamman, wasu launi idanun Ustaz ke dasu, wanda ta kasa tantance ko na mene a karo na farko da take son ganin jallabiyya a jikinsa domin taga kamar ma ya fi kyau da ita, kallon ido cikin ido suke Ridayya ta dinga gani kamar ba Abbiey ɗinta ba, ya sauya ya ɗan birkice ya kuma rame  sai nutsuwa da kamala haɗi da daddakonsa suna nan.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now