Page 28

1.3K 90 43
                                        

Duk yadda zuciyarsa ke bugawa bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin kai tsaye ba, ga wani irin hayaƙi da yake fitowa ya turnuƙe cikin kitchen ɗin gabaɗaya, hakan bai dame shi ba sai na zuciyarsa data ƙarfafe shi ta hanyar ƙara masa ƙwarin qiwwar shiga ciki ɗakko Nadra kamar yadda tunaninsu ya wanzar musu ita ce a ciki.

Yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarsa da nufin shiga ya ji an riƙe masa babbar riga ana faɗin "Uncle ƙani na kuka ƙani yana kuka" cak Ustaz ya tsaya ƙafar daya shigar cikin kitchen ɗin a nutse ya zaro ta, tare da mayar da ita baya yana juya idanunsa sosai da suke zube a kan yarinyar ba tare da ya ce komai ba.

Mahmah ta ce "Babban mutum dawo ka zauna ashe Nadra na bedroom ɗina tana mini wasa da bagaruwa, nasan baka son hayaƙi saboda ciwon kan ka, Sadauki shiga ka duba mene ya haddasa wannan hayaƙin idan dai gas ne sai dai mu fita daga gidan don sharrin shi yawa ne da shi"

Ustaz ya dawo da baya jarumta kawai ya nuna amma zuciyarsa ba ƙaramin tsalle take masa ba tana matsewa waje guda a ƙirjinsa tuni jijiyoyin kansa sun fara bayyana ya zauna saman kujera, ya kasa yin alkunyar ɗauke ganinsa daga kan Little Bilal.

"Mun same ku lafiya?
Yara gida da ayyuka?"

Ya faɗa a rarrabe bayan ya gama samun daidaito da tafiyar numfashinsa. A hankali ya saka hannayensa biyu ya ɗauki Little Bilal.

Mahmah ta murmusa cikin jin daɗin yadda ya ɗauki Little ta ce "Lafiya lou Babban mutum, kwana biyu zuwa kano baya yi maka wahala"

Ya lumshe idanunsa ya buɗe bai ce komai ba, sai nutsuwa da sanyin da yake samu deep down na zuciyarsa yana mamakin baiwa da ƙudirar Allah dake samar da mutane masu kamanni iri guda kuma ma bambanta jini, toshe da ƙwayar halittar haihuwa. Sosai ƙaunar Little ta zauna daram a zuciyarsa.

Mahmah ta ce "Sadauki ta shi mana, kana ganin baƙo babu gaisuwa?"

Baya son nuna halinsa da yi wa Mahmah gardama ya kalli Ustaz ya ce "Ina yini?" Tamkar Ustaz bai jima, haka ya yi shiru kai bama zaka ɗauka da shi Sadauki yake ba, can ya nisa ba tare daya ɗago kai ba ya ce

"Sannu"

Wani baƙin ciki Sadauki ya ji zuciyarsa kawai ya miƙe ya nufi kitchen ɗin a ransa yana mamakin waye shi a wajan Mahmah? Mene ya sanya yake yawan haɗuwa da shi? Kuma shi ne wanda yaje gidansu yana neman Ridayya kuma ga Ridayya ga shi what's going on?

Bayan tashin Sadauki Mahmah ta kalli Ustaz ta ce "Muhammad-Bilal ya kamata ka yi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ka ɗauki ƙaddara, Ubangiji shi ke rayawa kuma shi ke kashewa, shi ke samar wa kuma shi ne ke kwacewa, shi ke tadawa kuma shi ne sarkin dake kashewa. Ka ɗauka Ubangiji ya fi ƙaunar su Baffa da iyalanka shi ne yasa ya amshe su, suka koma gare shi dole ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara ka sakawa ranka cewa kaima ranarka na zuwa. Ka yi amfani da damarka ka ribaci lokacinka..."

Ta ɗan yi shiru, ta ɗora da faɗin "Aure! Ka yi aure Ustaz don Allah ka raya sunnar ma'aiki sallahu Alaihissalam, ka tara zuri'a yadda Ubangiji zai yi alfahari da kai wannan zaman da kake babu mace a gefenka is not good rashin aure ga baligi babban mutum irinka babbar matsala ce, shi aure ni'ima ce yana ƙarawa mutum nutsuwar zuciya da ɗauke damuwa rashin yinsa kuma yana taɓa kwakwalwa da gurɓata tunanin mutumin daya isa yin shi. Don Allah don Annabi Muhammad-Bilal ka yi aure kar ka tsufa a gida ƴan'matan su dinga gudunka nasan ba rasa matar aure ka yi ba, a taimaka a daure"

Ya kalli Mahmah sai kawai ya jinjina mata kai alamar “In sha Allah” don baya jin zai iya magana ya miƙe da Little Bilal a jikinsa wanda ya rungume Ustaz ya kwanta jikinsa tamkar jikin babansa, ya kama hannun Nadra yana ta tsaye bai ce komai ba. Fahimtar hakan yasa Mahmah cewa.

"Za ku fita kenan? Allah ya tsare Nadra banda ƙiriniya domin nasan halinki" nan ma jinjina kai kawai ya yi kana ya nufi waje da yaran a ransa yana ayyana inama yaran shi ne. Mahmah ta raka Ustaz da idanu ta ce

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now