Fitowa sukai daga ɓangaren emergency ɗin kana ganinsa zaka san yana cikin damuwa ya ce "Dr yanzu ya za mu yi da gawar? Kuma ba a samu labarin wanda sukai masa wannan rashin ɗa'ar ba?" Dr ya kalli Shaba da Moo ya ce "Ambulance za a kira sukai muku gawar, and wanda suka aikata hakan i think that is not part of my work, an dai samu labarin cewa ƴan daba ne suka same shi a bakin hanya, sukai ƙoƙarin amshe wayarsa ya hana su, garin haka suka soka masa wuƙa a ciki sai data ɓullo ta bayan shi, bayan wayar har motarsa suka gudu da ita shi kuma suka yasar da shi a ƙasa, kafin ma a zo asibiti ya cika" Moo ya sauke numfashi shikenan sun rasa Khalid? Yaushe za a daina ƙwacen waya? Yaushe ne za a daina shaye-shaye? Yaushe ne za a daina daɓa? Abin kullum ƙara girmama yake kamar cin ƙwan makauniyya? Faɗan sai ƙara yawa yake ba mai cewa komai babu mai ɗaukan mataki? Meke haddasa shaye-shaye da kuma daba? (Find out on MUTALLAB).
"Allah sarki Khalid Allah ya jiƙan shi bai so ya rasu bamu daidaita tsakaninsu da Zameer ba" cewar Moo kallon shi kawai Shaba ya yi without saying a single words. In few minutes rasuwar Khalid yaɗu cikin jama'a da kuma yadda ake Allah wadai da masu ƙwacen waya. Ambulance na zuwa aka saka gawarsa suka nufi gida, hankalin duka ƴan'uwa a tashe yake.
Zagaye yake cikin parlon nashi zufa sai yanko masa take ya juya ya kalli wanda ke tsaye a gabansa a hankali ya nisa ya ce "Kuma da gaske bai tura maka bidiyon ba kafin rasuwar shi? Bidiyon nan shine confidence ɗina kuma shinr hope nawa na ɓata farinjinin Muhammad Bilal, da kuma kawo naƙa su a takarar shi"
Guy ɗin ya girgiza kai ya ce "Oga bai tura mini ba, daman na baka shawara wannan aikin da mutum ɗaya kawai ya dace, baya tsoro, baya shakka baya damuwa da duk abinda zai biyo baya shi ɗin tamkar walƙiya haka yake, hagayi sa gabanka inda kake so, shi ɗin murucin kan dutse ne bai fito ba sai daya shirya, ɗan malam yaƙi halin malam, faɗa taka cikawa tashi kuɗi kawai shi ne a gabansa kaci amanar shi uwarka ta haifi wani, jan biro maganin daƙiƙin yaro..... Huhuhu kutumar uban nan wani aikin sai maza da an ganshi fitsari ake a wando, ya gagara matacce ne amma kullum firgita su yake mutum me aikin aljanu, mata maza wajan ƙin mata da sabgoginsu"
Nan da nan jiginsa ya fara rawa ganin haka ya saka Sakataren jam'iyar su Muhammad Bilal Ustaz mai suna Dr Ghali Uba ya ce "to waye wannan ɗin da kake ta yi wa kirari haka?" Shazali ya kalli Sakataren jam'iya ya ce
"MUTALLAB"
"MUTALLAB?"
Dr Ghali Uba ya maimaita sai kuma ta ce "Yanzu bamu da wani lokaci, amma idan ina raye ba zan bar Ustaz ya hau wannan kujerar ba, ni na nemi takarar kujerar wajan Uban jam'iyya amma saboda ya wulaƙantani ya ce ban dace da ita ba, ya je ya ɗakko wanda bai san darajar siyasa ba ya bashi? Na ci alwashin lalata jam'iyyar idan ya so na yi anti fati kawai"
"Oga kenan zagon ƙasa kake musu, sun yarda da kai fa? Shi ne kake ɓallo musu ruwa ta ƙasa? Ka daga oga"
Dr Ghali Uba ya ce "Shazali kenan siyasa sai ɗan siyasa, yanzu ka je ka yi bincike ka ji ko shi Khalid ɗin ya bawa wani kwafin bidiyon, kuma ka ce ina kiran shi yama sunan shi yawwa MUTALLAB TAHHB"
"Da ƙirinka oga ai MUTALLAB ko appointment ka nema da shi baza ka samu ba, saboda shegan ƙaro ne, innalillahi wani aikin sai ɗan Amina oga shi fa TAHHB ɗan balaja'u ne ko a rukunninsa ba kowa ya san shi ba" da mamaki Dr Ghali Uba yake kallon Shazali a ran shi yana tambayar who is MUTALLAB TAHHB?
Mardiyya ta yi tsuru-tsuru lokacin da ƙawarta ta shigo gidan daman shirye-shiryen kai Ustaz koto take yadda ta ƙarfi za a mallaka masa yarinyar. Umma ta juya ta kalli wacce ta shigo haka Baba ƙarami da Junaid da sauran mutanen wajan "Baiwar ke fa?" Cewar Aliyu kafin ta yi magana Umma ta ce "Na san wannan fuskar ƙawar wannan ƴar iskar ce" cikin sauri Mardiyya ta ce "Laa ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai yau" da wani irin mamaki ƙawar ta ce "Idan ba ki ce haka ba ai ba ki cika cikakkiyar munafuka ba, ke har ni za ki kalla ki cewa haka? To bari ki ji I'm not coming for this ga uban yarinyar da kika haifa can waje yana jiranki" gaban Mardiyya ya faɗi ƙirjinta na dukan saba'in saba'in ta ce "Ban gane ba" ta ce "Oh bari na yi yadda za ki gane" ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Sanda Mardiyya ta aureka tana da wanda take so, kuma maganar aure ya shiga tsakaninsu ma, tunda ta je gidan Ridayya suka samu saɓani ta ɗauki alwashin sai ta aureka, bayan an yi auren ta cigaba da mu'amala da Yaƙub suna haɗuwa a hotel kala-kala har mu'amala ta gitta tsakani ta samu cikin, hankalinta ya tashi domin a lokacin ta ji ta fara sakon ka gashi kana ƙoƙarin zama Gwamna, tana ta neman hanyar da za ku yi tarayyar aure saboda ta ɗauki bidiyo ya zama evidence na cewa cikinka ne, domin bata taɓa kawowa ranta zata haihu baka kasance ta ba, domin tabbatar da abinda nake faɗa ka je waje ai za kaga Yaƙub ɗin" Ustaz ya kasa cewa komai jin abinda yake kamar a littafan Hausa ko dram na film, ya juya tare da barin wajan. Mardiyya ta durƙushe a wajan tana rusa kuka bata taɓa ladamar abinda ta aikata ba sai yau, gashi wani irin mugun son Ustaz take kamar rai ji take kamar ta haɗeye shi ta hutawa ranta. Zuwan Hajia kenan ta ce "Amma dai kin watsa mini ƙasa a idanu Mardiyya, na yi bake bake raina bai huta ba sai dana ga kin auri yaron nan ashe tsatsa tuni ta cinye zuciyarki, to maza maza haɗa kayanki ki ɗauki ku yi gaba zuciyata har nunfashi take wajan ganin na ci miki mutunci" Inna ta ce "Ni dai daman zaman wanka na zo tunda abin ya zama haka ya lalace sai dai na ce Allah ya baku haƙuri amma tabbas anci mutuncin aure an kuma taɓa martabar aure" Tana kaiwa nan ta ja jakarta ko inda Mardiyya take bata kalla domin zata iya ci mata mutunci naƙin ƙarewa.

YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...