Chapter 47

1.2K 53 11
                                    

Cikin tashin hankali Umma ta ce "Bakin jariri kika ce fa Balkisa? Leɓe na jin baki irin nawa da nake magana kike nufi ko kuma wata tsoka ce ta yi tozo take neman faɗuwa ƙasa haka?" Ita kanta Balkisa mamaki da kallon baiwa da hikimar Ubangiji wajan iya tsara halitta shine ya cika mata zuciya da ƙyar ta zame idanunta akan jaririn ta ce

"Zai fi kyau ki nutsu Umma jaririn na hannunki ki duba da kyau sosai"

"Wannan ba dai jariri ba, sai dai idan ɗan aljanu kawai Mardiyya ta haifa, na rantse ban taɓa ganin jariri mai munin wannan ba, kalli hanci a bulaƙe kuma ya nane ta fata kalli halitta a jikin baki wai leɓe ce ko fa irin hasken jarirai babu a tattare da wannan jaririn" yadda Umma ke magana zai tabbatar da tashin hankalin da take ciki da gaske bata taɓa tsammanin jinin Babban mutum zai kasance haka ba, tana da yaƙinin jinin Muhammad mai ƙarfi ne duk yaron da zai haifa tabbas kamanninsa zai ɗauka.

Balkisa ta juya ta kalli Mardiyya da ko zafin haihuwar bai gama sakinta ba, fama ake ta yi ta mahaifa ta faɗo amma abu ya ci tura, dukda an ɗaure amma neman yin sama take wajan ƙirjinsa, hakan ya saka innar Mardiyya ta fara shiga tashin hankali domin tas mahaifa kan kashe mutum jini take sha sosai. Innar ta kalli Umma ta ce

"Haba baiwar Allah ke baki da imani da tausayi ne, kamar ba ki san ciwon haihuwa da zafin naƙuda ba zai yarfawa yarinya magana kike ina laifin ki yi lale da zuwan mai gidan naki? Halitta ɗaya ce dai kuma an haifa"

Wani banzan kallo Umma ta watsawa Inna ta dire jaririn da take jin ranta yana ɓaci a kansa, amma bata isa ta nuna masa ƙi ba saboda jininta ne amma har ƙasan zuciyarta take mamakin yadda yaron sam bai kwanta mata ba. "To Allahamdulilah mahaifa ta faɗo mun gode Allah an rabu lafiya"

"Ma sha Allah, sannu Mardiyya" cewar Balkisa ta shiga goge jinin wajan. Mardiyya ta sauke ajjiyar zuciya idanunta akan jaririn ganin babu inda ya bar mahaifinsa ta runtse idanunta tana jin fargaba mai tsanani na ratsa mata zuciya haihuwarta sa zuwan yaron duniya na nufin abubuwa da dama.

"Me na haifa ne Inna?" Ta furta da ƙyar Inna ta ce "Jaririya ce mace kika samu Mardi"

A firgice Umma ta ce "Mace kuma ke Balkisa ba namiji kika ce ba? Ai da maza jaririn ke kama"

"A'a Umma mace daman na ce miki ai"

Umma dai ta kasa furta komai sai girgiza kai take Mardiyya ta ce "Na yi wa Umma takwara a sakawa babyn Hadiza"  zanin Umma na faɗuwa ta ce "Wacce Hadizan za a yi takwara? Ba dai ni kike nufi ba Mardiyya"

"Umma mene laifina idan na saka sunanki jikarki ce fa? Ai farinciki ya kamata ki yi ko?"

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a na yafe idan an haifi wani a saka, ga innarki nan a saka ko"

Kafin su yi magana Yaya Zuhura ta shigo cikin murna ta ce "Umma albishirin ki?" Ta haɗe rai ta ce "Goro"

"Babban mutum ya dawo yanzu, Yaa Bilal is now at home" ba Umma hatta Mardiyya ba ta yi tsammanin jin hakan ba, ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi na farinciki da kuma na tashin hankalin da take tunanin yana gab da rikito mata. Farinciki ya saka Umma ta kasa cewa komai ta riƙe Yaya Zuhura ta ce

"Da gaske kike Zuhura?" "E Umma, yana main parlon ma" Umma ta juya zata fita Mardiyya ta ce "Umma ki tafi masa da babyn na san zai yi farinciki"

Ita dai Umma ko ta kan Mardiyya bata biba ta nufi hanyar fita Yaya Zuhura ta rufa mata baya, Balkisa ta miƙe ta ce "To Mardiyya bari na je na gaisa da ɗan'uwan nawa nima kafin ya shigo"

Inna dake satar kallon Balkisa ta ce "A'a kekam ai sai son barka sannu da ƙoƙari, uwar mijin dai ce naga ta na yi wa jinjirar wani gani-gani ai halittar Ubangiji ce"

Bayan Balkisa ta fita Inna ta ce "Mardi anya ba ki yi gamo da aljanu a wannan cikin ba? Ko kin watsawa ƴaƴan aljanu ruwan zafi ba ki sani ba?"

"Inna me kika gani?"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now