Page 21

500 38 14
                                    

Ustaz ya kasa magana sai kafaɗun Ustaza daya sake matse wa yana jijjigata idanunsa har wani ruwa ke kwanciya a cikinsu.

"Ustaza why? Ni na ce ba zan iya aurenki bane? Kar ki hukunta ni ta wannan hanyar Ustaza, na yafe miki ki janye maganar nan" Zuciyar Ridayya ce ta yi wani irin tsalle da ya tilasta mata rufe idanunta tare da ware su da kyau ta watsa a kan rikitacciyar fuskar ta Abbiey ɗin nata, bata san mene a idanunsa ba da yake mata shamaki wajan nutsa ganinta cikin nasa, ta kasa bisa dole ta janye idanunta na zubar da hawaye ta ce

"Me kake nufi Abbiey, ban gane ba wa zaka aura? Wani laifi ka yi mini Abbiey?"

Ustaz ya runtse idanunsa takaicin yadda maganin shaye-shayen nan ya dauɗar mata da kwakwalwa ke ƙuntata zuciyarsa a hankali ya ce

"Kin gane mana Ustaza, bambancin ko wacce rana shigar ta da fitar ta, na ƙara kusanta ni dake, ki yi mini alfamar a bar maganar haka nan"

"Ina son auren shi bana son karatun aure nake so nikam" ta faɗa hawaye na sake wanke mata fuska zuciyarta na yin ƙaura zuwa ga tunanin Zameer ɗinta.

"Ok zan miki aure, zan haɗa ki da miji na gari Ridayya" Kuka take sosai ganin yadda Abbiey ya kasa fahimtar ba kowa take muradin aure ba sai mutum ɗaya wanda a duniyar Ridayya babu wanda ke burgeta sama da shi domin har yanzu bata san ma mene soyayya ba, ta ɗauki alhakin yadda take jin a kan shi da yadda komai nasa yake Unique matsayin SO. Bata da hankali da nutsuwar tsayawa ta gane bambancin dake tsakanin SO da BIRGEWA.

"Shi ma na gari ne, wallahi Zameer na gari nikam shi zuciyata shi ta ke da muradi" A wannan karan wata tsawa Ustaz ya daka mata amma ko gezau ba ta yi ba, sai ma haɗe fuska da ta yi tana sake ci-gaba da kukanta.

"Shin ni bani da Qualities ɗin zama miji na gari a wajanki Ustaza? Ki yi tunani shekaruna nawa, mene ya hanani kasancewa da wata ɗiya mace, just because _I love you_"

Da sauri ya sake ta, jin yadda kalaman sukai futar da kan su tare da zama daram a kan shi bai shirya ba, bai san yadda akai ya saki abinda zuciyarsa ke danƙare da shi ba. "Kashe ni kawai Ridayya" Muhammad-Bilal Ustaz ya faɗa yana jin alamun zufa na yanko masa daga tsakiyar goshi zuwa bayan wuyansa, idanunsa na lumshe wa har wani dishi-dishi yake gani tare da wata yana-yana.

Ta durƙushe ta ce "Wallahi ban taɓa mafarkin ganin kai na a matsayin matarka ba, kai ɗin uba ne, babu wani tarihi da zai zo ya sauya sunana daga matsayin Ridayya Muhammad-Bilal Rano, bana son ka Abbiey komanka baya burgeni kana da tarin bambanci da Zameer wallahi.....,"
"Ya isa! Allah yafe miki Ustaza nikam na yafe miki" Yana faɗin hakan ya juya da sauri ya fice daga cikin ɗakin. Rasa inda zai nufa ya yi, baya da wani da yake sharing damuwarsa da shi, baya son mutane sam mutane basa ɗaukar hankalinsa. Ya tsani ƙarya magana biyu cuta ha'inci uwa uba rainin hankali wannan dalilin yasa ya ware kansa. Yana shiga bedroom ɗinsa ya dinga safa da marwa zufa ta gama wanke shi tas hannunsa goye a bayansa maganganun Ridayya na amsa kan su da kan su a kunnensa. Da sauri ya fice daga ɗakin ya nufi bedroom ɗin Baba ƙarami domin Umma bata nan.

Baba ƙarami na zaune saman laddumar dake shimfiɗe a carpet yana duba jarida. Idanu ya ji a jikinsa ganin daya bambanta dana ko wanne lokaci ya ɗago kai a hankali idanunsa ya sauka a kan na Muhammad-Bilal Ustaz. Rabon da yaga yanayin mai firgitar wa a tattare da Ustaz ya manta wannan shi ne karo na farko daya taɓa shiga irin wannan situation ɗin, tun yana ƙarami sai kuma yanzu. Kafin Baba ƙarami ya yi magana Ustaz ya ƙarasa ciki da sauri kuma ya kwanta yana ɗora kan shi a cinyarsa mahaifin nasa.

"Subuhanallahi! Babban mutum lafiya kar ka rikitar dani da wannan yanayin mene ne? Ridayya ce babu lafiya mene ya same ta?"

Domin a ransa yake jin babu wani abu da zai iya saka Ustaz shiga wannan halin sai Ridayya ko ciwon nata ne ya motsa? Mene ya samu Ridayya? "Babban mutum bar rufe ido faɗa mini ne kar ka yi give up da wurwuri kana da rayuwar muradan daya kama ta ka cimma"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now