Page 8

653 46 9
                                    

Hatsari ne wanda duk wanda ya gani sai ya girgiza, wasu su kuka da faruwa mummunan al'amarina na yiyuwar rasa rayuka da dama, masu matsanancin tsoro ta iya yiwuwa su yi mafarkin yar da babbar motar ta bi ta kan, ta su Baffa. Titin ya cika da jama'a aka dinga parking da abeben hawa, da ƙoƙarin ceto wanda Allah ya nufa suke raye.
Da ƙyar aka samu damar zare motar jini na zuba sosai daidai ambulance suka danno kan motarsu, basu tsaya tantance akwai masu rai ko duk sun mace ba duka aka kwashe su zuwa mota aka nufi asibiti mafi kusa da wajan da hatsarin ya afku. Tsoran Allah ya ƙara shigar wasu.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yanzu haka ahhali guda ne irin tafiyar da ba'a so, duk wanda ya yi saura a dangin ji zai yi kamar shi ma ya mutu ya huta, sun fito lafiya babu wanda ya taɓa tunanin lokacin mutuwarsa ya yi, kana tafe ne baka san kwana ya ƙare ba, Allahu Akbar wayyo Allah!"
Wata mata dake gefen mota ta dinga faɗa kuka yaƙi tsaya mata hankalinta ya tashi ainun. Mijinta ya riƙe ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki Madam, kar ciwonki ya tashi kuma, shi ya sa a kullum a kodayaushe ake son bawa ya dinga aikata abin arziƙi domin mutuwa bata sallama balle kasan ranar tafiyarka lahira.
"Allah sarki ni fa sai naga hannun wata kamar ya cire ga kan wani ya yi daga-daga wallahi zai wahala idan duk basu mutu ba" Nan da nan hankalinta ya ƙara tashi ta rushe wa mijinta da kuka da ƙyar ya lallaɓa suka shiga mota. Ana ta rai da neman taimako, a gefe guda kuma wasu sun taro sun sace kayan mamatan babu tsoran Allah da tunanin suma za su je inda sauran suka je.

Emergency ɓangaren ƴan hatsari aka nufa da su, aka shiga duba wa ko akwai sauran masu rai, aka bar likitoci su yi aikinsu, ƴan'sandan kuma suka shiga fafutukar inda za su gano ƴan wanne gari ne mamatan, da inda za su samu wani nasu amma har gari ya waye babu wani Information da zai tabbatar da su waye su, har lokacin ba'a samu cikakken bayani na kasancewar wasu a raye ba, ko duk babu.

Kwana biyu da faruwar lamarin Ustaz na zaune a parlon gidansa ko wajan aiki ya kasa zuwa, haka kurum ya ji faɗuwar gaba na ruskarsa, fargaba da tsoran da basu da masaniyar komai a kan wanzuwar su a zuciyarsa suka shiga ratsa shi. Ya rufe idanu sai ya buɗe da sauri shi kaɗai amma duk a firgice yake dukda ƙoƙarin riƙe kansa da yake da kyau da gudun hana faruwar tashin ciwonsa. Wayarsa ya ɗauka yaga Baffa ne last wanda ya kira shi sai kuma a lokacin ya lura da saƙon Baffa dalilin notification dake alamta masa zuwan saƙon. Kai tsaye number Baffa ya kira amma baturiyar wayar na zayyana masa wayar a kashe take. Ustaz ya yi shiru yana sauke numfashi can ƙasa zuciyarsa kuma sunan Allah yake kiran a kan ya sassauta masa fargabar dake shirin tarwatsa masa zuciya ya miƙe tsaye a hankali ya ce "Ya Allah, Rabbi inni lima anzalta min khairin faƙir..." Number Baba ƙarami ya kira itama ƴar'uwar ɗayar ce duk a kashe ya koma da baya kamar zai zauna sai kuma ya tsaya saƙon da Baffa ya tura masa ya buɗe, ya ware idanu ƙirjinsa na dukan tara-tara a hankali ya fara bin abinda saƙon ke cewa.

_Muhammad-Bilal zan so wannan maganar na yi ta ga-ni ga-ka babu mamaki zaka fi fahimtar hali da raunin da zuciyata take ciki, faɗar kalmar ban yi wa Ridayya adalci a rayuwa ba wannan kuskure ne, ina tunanin ta zaɓi rabuwa dani ne bisa ga abubuwan da suka faru a baya, Bilal girma muke nasan cewa mutuwa da rayuwa na Allah ne, amma babu tabbacin ganin gobe balle jibi balle kuma sanda zamu dawo daidai da Ridayya, Kullum Baffa take ce mini bata taɓa guduna ba, a wannan karan Ridayya ta zaɓi rayuwa da mijinta a kaina, bata ƙaunar ganina ta ce kar mu sake nemanta, ba zan wa Ridayya baki ba balle hakan ya haddasa ƙara lalacewarta. Muhammad-Bilal, Abbiey kullum Ridayya ke kiranka tun tana ƙarama har ta girma, sai daga baya ta fahimci ba kai ka haifeta ba...,_

Kasa ƙarasa karatun Ustaz ya yi saboda ƙafewar da yawon bakinsa ya yi, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha kana ya kira number Junaid itama a kashe a fili ya ce "Ya Allah!"
Ya koma tare da ci-gaba da duba saƙon Baffa wanda yake tamkar wasiyya ce ga Ustaz ɗin

  _Ka ci-gaba da zama a matsayin Uba kuma jigo a rayuwarta, Bilal don Allah don Allah ka duba girman Allah ka bawa Mamana rayuwa mai kyau idan har mijinta bai kasheta ba, ka bata karatun data rasa a baya ka tabbatar bata sake kuka ba, sai yanzu na fahimci ba Ridayya ta yi kuskure ba, mune mukai muna muka bata lasisin zaɓar wanda ya fi mata muhimmaci a rayuwarta, Bilal, Muhammad-Bilal, Ustaz Ridayya taka ce amace yanzu a wajanka na bar maka ita halak malak har abada, da zarar mun dawo daka Rano duk zan raba auren su wanda bai yi mini wata rana ba, zan bata mijin da yanzu fitila ta haska mini da cewa; shi ne ya fi cancanta da rayuwarta, ba zance umarni nake baka ba, ba kuma zance saƙon zuciya zuwa zuciya bane, ina da yaƙinin cewa wannan ɗin tamkar WASIYYA ce, rashin tabbaci kawai nake da shi, Na barka lafiya yanzu zamu ɗauki hanyar zuwa Rano duba kakarku_

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now