Mami ta tsare Baffa da kallo zuciyarta na yi mata soya, ta girgiza kai tare da miƙewa zata fice. Baffa ya tare ta faɗin "Yawwa na ce ki tattara dukkan furnitures ɗin dana siya miki, na bar wa Ammi su" Maganar ta doki zuciyar Mami ta juya a sanyaye ta ce "Ban gane na tattara kayan ɗakina na bar wa kishiyata su ba, explanation please?" Cike da faɗa Baffa ya ce
"Ba wani explanation Hausa ce dai na san kina ji ko Fatima?" Ta jinjina kai alamar E, kafin ta ce
"Bana tunanin akwai wani yare da ka iya wanda ban iya shi ba, ma'ana da hujjar tattara furnitures ɗina na bawa wata ne ban wani ba Alhji Mansur, cikakken bayani"
Kamar zai make ta haka ya tunzura ya ce"Maryam ɗin ce wata? Abokiyar zaman ki ce fa. Ok fine zan maimaita ki tattara komai na ki na bar wa Maryam su ina nufin Ammi, kawai yanzu nake ganin ita ta cancanta da kayan bake ba, kuskure na yi wajan siya miki su wallahi tallahi" Mami ta dinga kallon Baffa ta kasa cewa komai ta fice idanunta na cika da hawayen baƙin ciki.Mami na komawa bedroom ɗinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, damuwar zuciyarta gabaɗaya ta addabe ta, duk yadda tasu ta yi sharing ɗinta ta wani ta gagara, gashi babbar damuwarta a duk sanda ta buɗe baki da nufin yin addu'a wajan faɗawa Ubangiji halin da take ciki, sai ta ji kamar an rufe mata baki ta kasa ambaton sunan Allah da nufin neman taimako. Ga wani irin masifaffen yanayi da cikin ya saka ta, na buƙatar mace zuwa ga mijinta babu abinda take so irin kasancewa da Alhji Mansur da shaƙar ƙamshin turaren shi. Ta share hawayenta komai yaƙi ƙare wa kamar cin ƙwan makauniyya.
Washegari da sassafe ta kwashe komai nata, ta ce a zo a kwashe Alhji Mansur Rano wato Baffa da kansa ya kira yara suka kwashe tas, ya ce ita kuma a mayar mata da furnitures ɗin Ammi ta ce ta gode. Kwana biyu da yin haka aka shigo da sabbin kaya ƴan Turkiyya masu masifar kyau lokacin suna zaune a parlour Umma ta shigo.
Ammi ta dinga kallon zubin kayan da tunanin ko Baffa ne ya siya masa sabo fil tana girgiza ƙafa cike da taƙama ta ce "Kayan ne?" Wani matashin saurayi ne ya ce "E, Hajiya sune ina za a saka" Ya ce yana danne dariyar data kama shi"Ok ku haura da su upstairs" cewar Ammi. Mami ta dinga murmushi kafin ta juya ta ce "Hilal har kun ƙarasu?" Ya ce "E Mami, Mimi na gaishe ki ma" Mami ta miƙe tana murmushi har lokacin ta ce
"Zan kira ta kam, amma kayan sun yi ma sha Allah". "Mami a wajan fa kaf babu irin su kin san kuɗin da Grandfather ya tura? Ai arziƙi ya yi idan kana da kuɗi ka shige duk wani raini da wulaƙanci wlh Mami"
Murmushi kawai Mami ta yi Hilal ya ce "Talk Mami, ai gaskiya ce duk wata mugunta a wajan ɗan talaka aka santa musamman idan ka samu gidan miji ba fus ba ass sai dai a shimfiɗa dugwayen ƙafafuwan na cin banza da damfara, ga mugun abu kamar haihuwar Katsinawa""Wallahi Allah ya shirya ka Hilal Yaya A'isha bata gasa maka baki ba halan?" Ya ɗan kashe murya ya ce "Surprise....."
"What?" Ya mirgina kai ya ce "Na ba ki gari" Ta girgiza kai ta ce "I'm not good da cankar Surprise but i like surprises, just giss me" Hilal ya ce
"Aure zan yi" sai ya ɓata fuska ya ce "Mimi ta ce na yi ƙanƙanta don Allah mene abin ƙanƙanta a nan? Shi aure ai raya sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, kinga haihuwar fari sai na saka sunan Mamina" Mami ta ce "Kuma kana da gaskiya, amma auren RUƊIN ƘURUCIYA ne"
"Mami Ridayya fa?" A wannan lokacin ita kan ta Umma mahaifiyar Ustaz kallon Mami ta yi tana jira ta ji me za ta ce? Amma ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin hakan yasa Hilal yin shiru.
Ammi kunya ta kama ta ganin yadda ya kwafsa, a ranta tana mamakin kuɗi irin na mahaifin Hajja Fatima wato Mami.Hilal suka fara gyara kaya, Mami kuma ta haɗa musu lunch. Hira suke sosai da Umma tana mata murnar kayan data siya ta ce "Hajja Fatima yaushe aka zuba miki kaya har kika sauya wasu?" Caraf Ammi ta ce "Lallai fa, cewa ta yi bata so tunda kinga ai haihuwa za ta yi shi ne Baffa ya ce ta bar mini su, da gudu na karɓa ina godiya" Girgiza kai kawai Mami ta yi tana jinjina munafurcin Alhji Mansur Rano. A ranta tana mamakin yadda Ammi ta gane tana da ciki domin kullum cikin hijab take a gidan, kamar wacce take duba?
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...