Shimfiɗa

2.6K 79 15
                                    

Wani irin murɗawa mararta ta yi, kafin ɗan dake cikinta ya samu damar juyawa daga hango zuwa dama, dalilin wani rikitaccen tashin hankali daya tattaro waje guda ya ruftuwa zuciyarta wacce take a ƙudundune tsayin shekaru ta tsaya mata a tsakiya, baƙar fuskarta sai maiƙo take kamar an yi ɓarin baƙin mai a saman kwalta.
"Zaki kashe ni,
da gaske zaki kashe ni Mar..."
Sauran maganganun suka tsaya mata cur a maƙoshi kamar tsayi yiwuwar bushashshen itace. A gigice kuma ta yi wurgi da wayar dake maƙale a hannunta ƙirar Infinix ban da sauke ajjiyar zuciya da jan numfashi babu abinda take yi, mararta ta ɗaure tamau kamar mai jin fitsari. Bata so ko ƙaunar juyawa ta sake ganin mummunan photon dake saman fuskar wayar ƙara gani na nufin wani abu, hakan daidai yake da bugawar zuciyarta wacce zata iya kawo sanadin ƙarshen numfashinta.

Hannu Maridiyya ta sanya tare da riƙe kafaɗun Ridayya, da son dawo da ita cikin nutsuwarta ta riga ta fahimci a zauce take haukata kanta take son yi da gaske akan ɗa namiji.
"Kin yi wawta Ridha, lallai kin yi wawta soyayya ta rufe miki ido, kin cilla zuciyarki inda ba a maraba da ita, ba a gani kima da darajarta, inda ba a san muhimmacin ta ba, kin tafka kuskure na tsayin rayuwarki wanda zai ta yin motsi a zuciyarki, kin bada soyayyarki wajan da ba a son ƙimar SO ba, ba a kuma gane bambanci matar aure da budurwa ba, matar halak da wacce take waje sakakkiyya!"
Girgiza kai kawai Ridha ke yi cikin tsanar kalaman Maridiyya wanda suke kamar saukar dalma a zuciyarta.
"Baƙin ciki kike mini Maridiyya? Ni kike ma baƙin da zaman gidan mijina Diyya?" Maridiyya ta girgiza kai cike da tausayin Ridha, wani abu na motsa mata a zuciya, da son sanyata cikin zullumi har take jin tamkar ta rabu da Ridha domin ta riga da ta yi nisa, wanda ba zata iya jin duk kiranyen da za a yi mata ba, haƙurin Ridha daban yake lallai da gaske zata ci ribar hakan.
Maridiyya ta sauke wahalallan numfashi wanda take riƙe da shi tsayin daƙiƙo kafin ta ce
"Ridha ba zaki yarda photon mijinki Zameer ne wannan ba? Baki yarda shi ɗin ne riƙe da hannun mace ba?....,"

"Idan shi ne mene ya faru? Kina da matsala da haka ɗin ne?" Ridha ta dakatar da Maridiyya da faɗin hakan, tare da buƙatar jin meye matsalarta da rayuwar aurenta a gidan mijinta? Murmushin takaici Maridiyya ta yi, ta gane Ridha makauniyyar gaske ce, makanta biyu ta haɗe mata, data ido da zuciya!
"Ni kam bani da matsala, ina son taimaka miki wajan fiddoki daga kabarin da kika rufe kan ki ne, Ridha ba damuwata macen dake photo tare da mijinki bane, gigitata bai huce ganin yarinyar da Zameer ya kawo miki cikin gidanki matsayin ƙanwar miji ba, ƙanwar shi; ki duba da kyau Riddahh, duba da idanunki wanda suke aiki ba makafin ba"

Ridayya ta ƙurawa photon ido, da gaske abin begenta ne, rayuwarta ne, farin cikinta ne, tsaginta ne, bugun numfashinta ne, mutumin data sadaukar da abubuwa da yawa saboda shi, ZAMEER! mijinta ne a photon. Ta bi fuskarsa dake shimfiɗe da lallausan murmushin da ba ko yaushe take ganinsa da shi ba, gajiyayyun idanun nan nasa masu narkar da raunatacciyar zuciyarta zube akan yarinyar dake gefen shi, yadda idanunsa ke kanta zai fasaltawa mai kallon photon gane wani irin ɓoyayyen sirri dake cikin su, sirrin dako shi kansa Zameer bai sani ba, baya da tabbaci akai,bai kuma san komai dan gane da hakan ba, akwai zalama da muradi a idanun wanda kai tsaye yanayinsu ya bayyana abin da zuciyarsa ke rufewa, yarinyar kusa da shi kuma ta ɗan shagwaɓe fuska tana kallon hannunsu dake sarƙafe da juna.

Ridayya ji ta yi kamar fitsarin dake maƙale a mararta na bin cinyoyinta,  numfashinta ya fara kai komo a karo na biyu! Ta sake cilli da wayar tana dafe cikinta daya girma, wanda yake gab da shiga watan haihuwa.
"Karki nemi haukata ni Maridiyya, karki saka na haife abin da ke cikina ba tare da cikar wa'adinsa ba, me mijina ya yi muku? Da kuke son tilasta ni naga baƙin shi? Ina son shi, ku fahimta ku barni,ku barni haka nan,ku barni Maridiyya...."
Ridayya ta daddafe kanta dake juyawa ta kasa gane ainahin meke damunta. Bata son ma ta gane ɗin balle ta samu rauni da ji da motsin son Zameer.
“No man succeeds without a good woman behind him. Wife or Mother, if it’s both, he is twice blessed” Maridiyya ta faɗa Idanunta cike da hawaye.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now