Ridayya ta ɗauka kunnenta ne ya sa mu matsala, cikin sauri ta zame wayar daga jikinta tare da saka hannu ta shiga bubbuga kunnen a fili ta ce "Babu mamaki ruwa ne ya shiga ciki, ya toshe ƴar ƙofar ɗaukan sautin har take naɗo mini masifa da bala'i"
Ta mayar da wayar a hankali duk da ƙirjinta dake bugawa da muryarta ke rawa bai hana ta tattaro jarumta kamar jinin Iliya ɗan mai-ƙarfi ba ta ce "Rayuwata, ni ce matarka Ridayya ka na ji na?" Ta yi maganar cike da ƙarfafawa kanta qiwwa, da share gurɓataccen zaton da zuciyarta ta yi mata akan Zameer. Shiru babu amsa sai wayar data fara shuuuu!! Kamar kammalawa shirin gidan rediyo ya yin rufewa, da yin ban kwana da masu sauraro."Asstagafirullah! Allah na tuba ka yafe mini, daman nasan sharrin shaiɗanne kawai yake son kissima mini wani mummunan zato akan Meer" Ta yi shiru; tana sauraran bugun zuciyarta da take mata, kamar luguden gidan biki.
Duk yadda idanunta ya su runtsawa da samawa kanta nutsuwa al'amarin ya gagara, bacci ya ƙaurace wa idanunta. "Allah ya gani ina so da ƙaunar mijina, Yaa B ka yi haƙuri ba yin kai na ba ne, bana jin zan iya rayuwa ba tare da Zameer kusa dani ba"
Hawaye ya shiga zuba daga kwarmin idanunta, zuciyarta na tsananta bugawa ki manin daƙiƙar gudun lokaci.
Da ƙyar bacci ya ɗauketa gab da asuba, ba wani na kirki ta yi ba ta ji ƙarar wayarta alamar shigowar saƙon karta kwana, cikin ganɗoki ta ɗauka zuciyarta na faɗa mata Meer ganin wanda ba ta yi zato ba ya saka ta ƙura wa saƙon Idanu.Alert ɗin kuɗi ne, sai gajeren saƙo daya biyo bayan alert ɗin. Ridayya ta rufe idanunta, da gaske tana buƙatar taimako, daga na kuɗi har na kulawa, tana buƙatar sharing damuwarta da wanda zai fuskance ta, wanda zai kyautata mata zato akan soyayyar Zameer ba wanda zai dinga ganin laifinta ba.
Ta zubawa sunan Bilal idanu, wanne irin abu za ta yi masa wanda zai tsane ta? Tsana mai muni ya dinga ganin baƙin ta kamar yar da a yanzu take ganin nasa?
Kuɗi ne kimanin dubu hamsin ya tura mata zuwa asusun bakinta, yasan da gaske tana buƙatar su.
"Yaa Bilal why? Me ya sa? Bana ƙaunar ka, na tsane ka gwargwadon tsanar da ka yi wa mijina, ba kai ba duk wanda zai wulaƙanta Zameer a duniyar nan ko waye zai i ya wulaƙan ta shi..."
Ta yi maganar a fili kuma a raunace, sunan Yaa Bilal data ambata yana mata amsa kuwwa! A cikin kunnenta, bugun zuciyarta na ƙaru wa duk a dalilin jin sunan Bilal ɗin ya fita a bakinta.
Har aka gama sallah tana nan a zaune, da ƙyar ta yunƙura zuwa banɗakin dake cikin ɗakin asibitin. Shiru ba kowa sai ita, ga aikin da akai mata, ga gubar fiya-fiya data sha, ga damuwar zuciya wacce take tunanin babu wanda ya haddasa mata irin danginta. Mijinta bai rage ta da komai ba.
Nas ce ta buɗe ƙofa hannunta ɗauke da kayan duba mara lafiya, ta tsaya gaban Ridayya tana mata tambayoyi da ƙyar take buɗe baki wajan amsa mata har ta kammala.
"Can i ask you dear?"
Ridayya ta kalli Nas sai ta jinjina mata kai alamar "Why not?"
"Thank you"
A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana kallon Ridayya dake matar da shekarunta a haife zata haifi Ridayya a nutsu ta ce."Tunda nutsatstan magidancin nan ya kawo ki asibiti na fahimta a kwai damuwa a tattare dake, na ji tamkar ƴata Safiya ce a cikin condition ɗin da kike ciki, ƴa ƴa na kowa ne bawa sai mai shi. Zan so ki buɗe zuciyarki ki aminta dani ba zan cutar dake ba, ki faɗa mini mene damuwarki please, i just feel your pain"
Kan Ridayya a ƙasa ta kasa cewa komai saboda yar da ba ta jin daɗin al'amarin da yake riskar ta a yanzu.
"Ki yar da dani, mene dalilin shan fiya-fiyan da kikai? Ba rashin sani bane yunƙurin kashe kai da kai kikai ɗiyata, na karanci damuwar dake shimfiɗe a fuskarki what's going on? Waye shi? Su kuma su waye? Kyakkawan namijin nan waye?"
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...