Page 29

1.3K 92 29
                                    

Ganin abin na Ustaz azumin ne ya saka Mahmah kama hannun Nadra ta ce "Mu je ciki"

"Ki haɗa da Junior"

Tajuddeen ɗin ya furta da ƙyar yana jin wani abu mai zafi na tsaya masa a ƙahon zuciya, mene ya shiga tunanin Ustaz har haka? Mene tsakaninsa da Ridayya girman tuzuruntakar tasa har ya kai ya fara kama yaran mutane? Gabaɗaya tunanin Tajj ya tsaya wani abu mai kama da zullumi ya fara kawo masa ziyara.

Miƙewa ya yi tare da yin waje ya bi bayan Sadauki domin ya lura da shigowar tasa da kuma sauyin daya gani tattare da shi ɗin.

Bakin Ridayya ne ya fara rawa idanunta a fuskar Ustaz har yanzu ta kasa kallon cikin idanunsa wanda kuma hakan shi yake buƙata, jininta na rawa tana jin saukar numfashinsa a fuskarta yana saukar mata saboda fuskarsa dake ɗan rakaɓe da nata ya kasa furta komai. Da sauri kuma ta yi saurin zame fuskar tana yin baya tare da ƙare masa kallo.

Sai kuma ta shiga girgiza kai while hawaye running down on her face. Ta buɗe baki cikin firgitaccen yanayi ta ce

"Mafarki nake da gaske mafarki ba kai nake gani ba, irin mafarkin dana saba yi ne a kullum a koyaushe ba zaka taɓa zuwa gare ni bakai bane you're not my father...... My Abbiey is dead, he is in the grave"

Baki Ustaz ya buɗe zai yi magana ya kasa ta yi saurin cewa

"Me zaka ce? Shiru ko na san mafarki nake ni kaɗai ce bani da kowa sai wanda yaga Allah ya taimaki rayuwata me ya sa zaka bar ruhinka ya fito domin ya firgitar dani Abbiey why why why?"

"Don Allah ka yi magana ka ce kai ne ka dawo gare ni baka mutu ba, wayyo Allah wayyo ni Ridayya na shiga uku"

Ji ya yi kamar an saka sofa glue  tare da manne masa laɓɓansa ya kasa buɗe baki balle furta komai ya kasa nufar inda yake da tunanin idan ya riƙe ta da hannayensa zata dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta. Duk dauriyarsa da yadda ya so riƙe kansa kasawa ya yi jikinsa ya shiga ɓari hatta laɓɓansa rawa yake baya son tunkararta kai tsaye domin a farkon ma, tsananin ta'ajjuji ya saka shi yin hakan da son fahimtar da gaske ita ɗin ce tsaye a gabansa shekaru nawa? Wata nawa? Kwanaki nawa? Mintunawa nawa? Daƙiƙo nawa ya shafe yana jiran wannan ranar?

Abu biyu ne zai faru idan ya ƙarasa wajan wanda kuma a yanzu bai isa ya hana zuciyarsa da gangar jikinsa hana afkuwar hakan ba, domin baya da iko da su a yanzu sune suke jan ragamar shi. Idan bai riƙe Ustaza ya sanyata cikin jikinsa ta jiyo ɗuminsa wanda ta saba da shi tun tana ƙaramar, to idan bai hakan ba yasan sauran abinda zai biyo baya shi kansa bai sani ba yana tabbacin sahihiyar runguma ce zata samu matsayin tarba a gare shi.

Yana kallo ta juya tare da shigewa ɗaki ta rufe ƙofar kai tsaye kuma zaman dirshen ta yi saman carpet ta saki wani irin raunataccen kuka na ƙuncin rayuwarta. Tunanin Abbiey har ya kai ya dinga zuwar mata idanu biyu? Ya fito daga kabarinsa yana wasa da tunaninsa tasan tunda ya kasa furta komai to wannan mutum mutuminsa ne kuka take da iya ƙarfinta har sai da ta ga ji ta fara shassheƙa tare da kwanciya saman carpet ɗin duniyar ta mata zafi cikin wani irin sounds na fitar hayayci ta ce

"Allah ya isa Zameer Allah ya isa ka rusa mini rayuwata ka hanani sukuni da jin daɗi na yi regretting  sanin ka a rayuwa, ka yi amfani da rashin gata na, rashin farin ciki, kushe da zunɗen da ake mini a kan halittar da Ubangiji ya yi mini ka yi amfani da son da nake maka ka rabani da jin daɗina ban san haka ɗabi'unka suke ba ashe kura ce da fatar akuya ashe kyan ɗan'maciji ka yi ka zame mini ƙarfen ƙafa bani da sukuni sai na fargabar abinda za ka iya yi mini. Ka zame mini MUNAFUKIN MIJI ba tare dana fargaba ka yi mini illa ka yi mini shamaki da dukkan wani ɗa'namiji babu mai dubana idan ya ji zumubin dana aikata saboda soyayya!"

Wani irin ɗaci take ji a duk sanda ta tuna lokacin data bawa Zameer kanta wai saboda kar ya daina son ta ya koma wajan wata ko ya fasa aurenta. Batun bidiyon da ya yi musu ya fi komai ɗaga mata hankali video ne da zai iya taɓa career ɗinta dana iyayenta da suna raye a ranta take jin ko zai yi sanadin da kowa zai guje ta; ta zama mujiya ba zata taɓa komawa auren Giɗaɗo ba.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now