Page 33

2.1K 102 59
                                    

Koda ya je ƙasa bai bari ya sare ba, baya son ciwo Ustaz ya dinga ƙoƙarin tashi ya kasa jinin zai zuba yake ta hancinsa. Ridayya kam ji ta yi gabɓanta sun yi sanyi duk maganar da Sadaukin yake bata fahimta kamar almara ta kasa juyawa kuma.

Tajj tun shigowarsa harabar gidan idanunsa ya sauka a kan Ustaz da sauri ya fito ko kashe motar bai ba cikin wani irin tashin hankali ya kira sunan Ustaz.

"Bilal Innalillahi Bilal"

Kiran sunan ya saka Ridayya juyawa da wani irin firgitaccen yanayi ta kwace hannunta daga na Sadauki har tana bangaje shi ta nufi inda Ustaz yake wanda Tajj ke ƙoƙarin riƙe shi amma ya hana a dole shi zai miƙe.

Tuni hawaye sun wanke mata fuska kamar yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke yi daga kusa da ita ta ce murya mai ɗauke da tashin hankali ta ce "Abbiey"

Kallon da ya yi mata ya saka ta fahimci  zuciyarta ce ta kira shi, raguwar halittar daya ya yi saura a cikinta shi ne ya kiranye shi.

"Kar ki zo mini nan kar ki taɓa ni" Ya furta da ƙyar yana numfashinsa na riƙewa zuciyarsa na tarwatse.

"Please Ustaz not here akwai Sadauki a wajan, ka bari mu je asibiti"

"Sadauki? Ka faɗa masa ya zo ya nemi aurenta waje na"

Yadda Ustaz ke maganar kamar baya nutsuwarsa kuma shi kansa bai san me yake cewa ba, taurin kai kuma ya hana shi ya kwanta yana miƙewa jiri kwasar shi. Ridayya kuka take ganin yadda Ustaz yake abu kamar zautacce

Tajj ya ƙarasa wajan Sadauki ya ce "Hamza jeka za mu yi magana"

"Where? Kana ji ya ce na zo na nemi aurenta a wajansa"

"Na ce ka je za mu yi magana ko Sadauki" idanun Sadauki ya yi jajur ya ce "Ba inda zani domin ba wajanka na zo ba, kai na nemi taimakonka ka share ni, bare ya fini...,"

Wani mari Tajj ya saukewa Sadauki a fuska ya ce "Ka shiga hankalinka kuma zanje wajan Daddy na ji da wanne irin abokai kake yawo"

"Babana babana ne ni ɗaya ka ce Prof zai fi daɗi a rai, daka ɗauke shi matsayin uba ba zaka wulaƙanta ni a kan wani ba, kuma ba zaka bari na rasa abinda nake so ba, so please stay away from me"

"Ok fine ka fita"

Sadauki ya nufi wajan Ridayya ta yi saurin yin baya idanunta a kan Ustaz da kansa ke ƙasa ya ƙarasa har gabanta idanunsa na zubar da wani rin hawaye mai zafi ya ce

"Zan tafi ba zan dawo ba sai da Daddy, i love You Ridayya don't ever ever trying to break my heart"  Ya runtse idanunsa "Wallahi ina son ki, idan kika rabu dani abin ba zai mana daɗi ba ki saka a ranki bana yafiya saboda tsakani da Allah nake tsananin ƙaunarki duk abinda nake ina sane na san me nake yi, don Allah karki barni"

Sai kawai ya fashe da kuka abin har tsoro ya bawa Tajj don bai taɓa ganin Sadauki ya yi ko hawaye ba balle kuka, ko abu ne sai ya ce ya fi ƙarfin ya saka wannan ɗan abun a rai shi ya sa bai taɓa gwada yin soyayya ba.

"Ridayyerh i love You. Love isn't something you find. Love is something that finds you, ban san yaushe nake miki wannan son ban"

"Sadauki get out, ka rabu da ita ko?"

"Tajuddeen Baita shut up ok, ka rabu dani kai baka san komai ba tunda Maman Nadra auren zumunci ne haɗa ku akai, baka san ya mutum yake ji a zuciya ba idan hakan ya kasance"

Tajj ya jinjina kai ya ce "Ok" wayarsa ya danna magana biyu ya yi ya kashe sai ga wasu ƴan'sanda sun shigo cikin gidan sukai kan Sadauki da mamaki Sadauki yake kallon ɗan'uwan nasa ya juya ya kalli Ridayya wacce itama a ruɗe take gabaɗaya ta kasa fahimtar mene hakan?

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now