A kiɗime ta ƙara cewa "ɓarawo, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un ɓarawo a ɗakina, Meer rayuwata ɓarawo ya shigo mana" Babu wanda ya amsa Ridayya balle kawo mata ɗauki ta tashi zaune tare jingina da jikin bango, abu goma da ashirin ya haɗe mata. Ƴar raguwar wayar da ta yi mata saura a kadara itama an rabata da ita wai meke shirin faruwa ne. Daidai ɗaga labulen ɗakinta sa'arda nepa suka kawo wuta, hasken wutar ya haska fuskar Zameer da yake ɗan mustsike Idanu alamar bacci cikin kulawa ya ce
"Sama-sama ina bacci na ji ihunki lafiya?" Ya tambaya yana daga tsaye, domin baya jin zai iya zama a ɗakin.
Ridayya ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Kana gidan ashe?" Ya ware Idanu kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru kawai.
"Ina bacci ne ɓarawo ya shigo, ya ɗauke wayata" Zameer fuskarsa shimfiɗe da damuwar daya ƙirƙira a lokacin ya ce "Waya kawai aka ɗauka?" ta jinjina kai alamar "E" Ya ja tsaki a fili ya ce "Shi ne abin ihu a kan ɗaukar waya? Ke dai Ridayya ba ki da tawakkali Kwata-kwata, kece raki idan babu lafiya, kece surutun yunwa kamar za ki yanki naman jikina ki gasa kici, duk abinda na yi miki baya birgeka bana miki gwaninta daman kece kika zubar mini da ƙima da girmana a idanun ƴan'uwanki, ni kam na auri matar ƙaddara!""Matar ƙaddara!?"
Ta maimaita a fili idanunta tsaye cur cikin na Zameer domin a ko wanne yanayin a duk halin da zata tsinci kanta bata shayin sanya idanunta a cikin nasa. Muryarta na rawa laɓɓanta na karkarwa saboda ciwon ciki ta ce
"Ni kake kira da matar ƙaddara Rayuwata? Ni Ridayyanka?"
Ya ɗaga kafaɗusa duka biyun yana ƙanƙantar da idanu murya ƙasa ya ce
"Kar ki mini gurguwar fahimta, kar ki mini, ai ba kece ƙaddarar ba, ƴan'uwanki da auren sune, tunda na aureki ban hutawa raina ba, Allah ya ƙara mini haƙuri, shi ya sa magabata suke cewa Allah ya saɓa halayya"
Ikon Allah kawai Ridayya ke kallo ko dai mijin nata wani abu ya sha yau? Bai taɓa mata furuci makamancin wannan ba a hankali ta ce "Don na bar ƴan'uwana baya nufin bana son su ai" Ya riƙe ƙugu ya ce "Ba shakka, idan tururuwa ta so lalacewa, daman fiffike take yi ta tashi ai"
Idanunta suka cika da hawaye fal idan da sabo ta saba da kuka tun a daren amarcinta ta ce
"Meke damunka na rayuwata? Me na yi da zafi har haka? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mini"
Ya ja tsaki yana juyawa. Kasancewar a waje ya yi shimfiɗe tunda ya kammala buƙatarsa da Khairy. Juyi ya dinga yi akan tabarma shi sam ba haka ya tsara gani a auren Ridayya ba, duk abinda yake buri bai samu ba sai masifa kala-kala da auren ya jefa shi. Ridayya ta share hawayen da yaƙi tsaya mata, tana nan jingine da jikin bango, da tana da ikon tariyo rayuwarta ta baya babu shakka da ta yi hakan domin gyara ƙazantar data aikata wacce babu mamaki warinta ke bibiyarta a yanzu."Ƴar baƙata" Ta ji ya kirata jikinta na rawa ta miƙe zani na faɗuwa ɗuwawu a waskace saboda masifar zama waje guda ta zama tsohuwar gaske wacce masifaffiyar wahalar gidan miji ya mai da ita, daman ba kyakkawa ba domin Ridayya ko a kwatance tana cikin mutanen da za a yi kwatance da girman munin halittarsu. Domin saboda wannan yanayin nata zubin halittar ko a makarantar da aure ya datse mata ita Duduwa ake ce mata.
Kamar zata yi masa sujjada haka ta tsuguna a gabansa jikinta na rawar ɗari kar ya taɓa lafiyarta. A hankali ta ji ya ce "Sorry ƴar baƙa, raina ne a ɓace mece waya? Ni da nake saka ran siya miki zuƙeƙiya kalar ya yi, kin san komai na samu naki don ke nake fafutuka da ba ke, da tuni ina Lagos wallahi"
Ta yi shiru ya ce "Ki manta da faɗan ɗazo, zan yi miki swapping na sim ko?" A nutse ta ce
"Allah ya baka iko"
Tunawa da cewa bai tsarkake jikinsa ba ya ce "Ɗan dafa mini ruwan zafi" Ta kalle shi da sauri"Me za ka yi da ruwan zafi a wannan tsakiyar daren?" Ya haɗe fuska da kyau yana nutsa idanunsa a nata bisa dole ya ce "Wanka, zafi ake yau" Ta dinga kallon shi haka kurum gabanta ya dinga faɗuwa ta ce
"Ba gawayi ai" kai ya bata amsa da "Amma akwai ita ce ko Ridayya?"
Muryarta a sanyaye saboda rashin ƙwarin jiki da yunwa da gajiya da surutun Zameer domin wuta take buƙata.
"Duka manya ne, babu faskararre"
A zuciye yana ɗaga murya ya ce "Kuma Allah bai azurtaki da hannu ba? Bayan rashin fasali har da nakasa ko? Ina cewa akwai gatari a gidan nan, aure ba abin wasa bane dole ki yi bautar gidan miji, da ake cewa Aljanna da wajan miji ai ba banza ba, bauta kawai aka san mace da yi a gidan miji ta yi ta wahalarta masa yana saka mata albarka, idan albarkarce bakya so sai na ji ba'asi"
Miƙewa ta yi a tsakiyar daren ta tattare zaninta shi kuma ya ɗauki wayarsa yana ƙarasa kallon wani blue film yana rufe ƙananun idanunsa. Da ƙyar ta ja itacen zufa na yanko mata haka take ɗaga gatarin tana yin faskaren ana ƙarshe tana ɗagawa ruwan gatarin ya zare ya sauka a yatsan ƙafarta wani ihu da kururuwar azaba, zafi da raɗaɗin daya ratsa jijiyar kanta ya shiga rabawa sauran jijiyoyin jikinta, ƙofofin fatar jikinta ta mimmiƙe wani zazzaɓi mai zafi ya kunno kai ya ratsa jikinta, kuka take majina na fita daga hancinta ga jini na zuba sosai.
YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...