Page 5

637 55 10
                                    

      NA YI COMPLAIN A KAN RASHIN COMMENTS KUN CE ZA KU NA YI, AMMA BA COMMENT BA VOTE NA SHA WAHALAR RUBUTU BA ZA KU IYA SUPPORTING NAWA TA HANYAR COMMENT DA  VOTE BA? DA ZAN CE YA ZAMA NA KUƊI SAI A GA LAIFI NA, GASKIYA KU SAUYA HALI.

Idanun Ustaz ya sauka akan abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ya yi zaton wani a cikin kitchen ɗin, amma mummunan ganin da ya yi ya sanya ya ɗan yi baya a tsora ce tare da rufe idanunsa can ƙasan zuciya Ustaz Bilal ya ce
"Ya subuhanallahi! Asstagafirullah" Ridayya ya gani da Zameer kwance a ƙasan kitchen ɗin, turmi da taɓarya, ya saka hannu ya shaƙe mata wuya sai shure shure take tana kakari tamkar na fitar hayyaci ko zarar rai.
Ustaz da ƙyar ya ja ƙafafuwansa da nufin barin wajan domin jiri ne ya ji ƙoƙarin yasar da shi a ƙasa, al'amari Ridayya kullum girmama yake yana sake lalacewa.

Karo suka ci da Baba ƙarami daya fito hakan ya sa Ustaz tsayawa tunda ya ga lokacin assalatu bai yi ba, balle ya yi zaton Baba ƙarami sallah ya fito yi.
"Ustaz ba dai ya zo kake dawowa ba?" Ustaz ya kalli baban nasa a hankali ya ce "E, dawowar kenan" Cikin gamsuwa ya jinjina kai yana mai faɗin.

"Ai tun ɗazo nake jiranka mu yi magana, har dare ya yi shiru ka jira ni a parlo zan duba naga ta'addin me nake ji tun a shashin baya har hanyar kitchen" Kafin Ustaz ya yi magana Baba ƙarami ya nufi hanyar kitchen ganin da gaske can ya nufa, kuma baya fatan ace mahaifinsa yaga abinda nasa idanun ya gani da ɗan saurin harshe ya ce
"Abba, ni ne fa"
Baba ƙarami ya tsahirta da tafiya ya ce "Kai ne me?" Kan Ustaz a ƙasa
"Ruwan zafi na haɗa, na ɗan zaga baya ne"

"Ruwan zafi a daren nan Mai babban suna? Kamar wani ƙaramin yaro kake suntiri da ɓuruntu?" Shi dai Bilal bai ce komai ba, domin baya buƙatar sake shimfiɗa wata ƙaryar akan kare Ridayya, ya nufi hanyar parlour. Yana zama Baba ƙarami ya zauna yana ƙarewa ɗan nasa kallo a nutse ya ce
"Bilal?" Da Idanu kawai Ustaz ya amsa Baba ƙarami ya ɗora da faɗin
"Ridayya tana gidan nan, na ɗakkota daga asibiti rayuwar yarinyar nan abar dubawa ce, bai kamata a ƙarancin shekarunta a ce tana fuskantar ƙalubalen gidan aure da matsalar miji ba, kasan rayuwar Ridayya ka fi kowa sani da halin data tsinci kanta a baya, me ya sa ba zaka aureta ba?"

"Aure Abba?"
Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce "Shi fa, naga ba haramun bane" Ganin Ustaz na shirin miƙewa ya saka cikin bada umarni Baba ƙarami ya ce "Kar ka kuskura ga tashi, ko baka son Ridayya zaka aureta"

"Mahaifi da auren ƴarsa ina aka taɓa haka? Asstagafirullah Allah ka ya fewa Abbana" Baba ƙarami ya saki baki kafin ya ce "Zan sassaɓa maka yanzu, idan ranka ya yi dubu to zai ɓaci, ka kuma gaggauta cire abin da ke yawo a zuciyarka ka daina haramtawa kan ka abinda yake halak ne zaka iya jahadi ne" Ustaz ya miƙe tsaye idanunsa jajur ya ce
"Abba kai na ciwo yake nikam ciwo kai na ke mini, Matar auren kake jingina mata auren wani Abba haza haramun Ya Rasulullah Asstagafirullah!" Yana faɗin hakan ya fice shi kansa bashi da tabbaci akan maganganun da yake furtawa.

Washegari wajan shi da na safe Baba ƙarami ya saka a haɗa abin karyawa zai kaiwa Ridayya ta sha, ta ci abinci ta ƙara hutawa sai a sauya mata asibiti domin wani abun da yake damun Ridayya hadda sakacin iyaye da rashin kula da al'amarin yaran su. Da sallama ya shiga ɗakin amma shiru ba amsa ya dinga bin ko'ina da kallo ba Ridayya babu mai kama da ita, yana shirin fita idanunsa ya a kan takardar da aka ajjiye saman gado ya saka hannu ya ɗauka, saƙon daya gani ya gigita shi tare da sauya masa lissafi da jin komai zai yi a rayuwa dole ya kashe auren Ridayya Ustaz ya aura, Ubangiji shi ne shaida bai aikata hakan domin ya ci mutuncin wani ba, ko ya lalata mata auren ta ba, zai yi ne domin taimakon rayuwar ƴar ɗan'uwansa. Ya sake ware farar faifa ɗin idanunsa ya sauka a kan rubutun nata.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now