Ya juya ya kalleta jin yadda take ta kuka, zuciyarsa fes ya samu miliyan goma a caca ta sanadin yarjejeniyar soyayya ta samu budurcin Ridayya. "Kukan na mene kuma? Bafa dole na yi miki ba"
Kukan da bata san dalilin yin sa ba shi take a lokacin da ƙaddara ta yi fatali da dukkan wata kima da darajarta na ɗiya mace saboda ƊA NAMIJI, da soyayyar da bata tabbacin zahirin ta a cikin zuciyarta, ta wofintar da duk wata kulawa tarbiyar da Abbiey ya bata sun zama tarihi a yanzu. Shigowar Zameer cikin rayuwarta tsakanin wasu ƴan watanni ya rusa tarbiyyar shekara goma sha shida da watanni.
"Haba Pretty idan kina kukan nan ina jin kamar ban dace da ki mallaka mini komai a matsayina na wanda kike so kuma kike shirin aure ba"
Ta kasa magana sai sautin kukan dake tashi a hankali tana naɗe jikinta a bargo, haka kawai fargabar Abbiey ya san wannan abin mai shirin tarwatsa zuciya ya rusketa. Ta tsinkayi muryar Zameer dab da kunnenta yana kama hannunta da yanzu bashi da shamaki da shi ya ce
"Look into my eyes Ridayya, na yi miki dole? Ita fa soyayyar zamani haka take kina so na yi believing da haka, kuma wannan abin daya faruwa babu komai sai ƙauna kin bani kyauta mai muhimmanci wacce ba zan mance da ita ba, zan dinga tunawa a kullum, kin bani budurcinki na ba ki nawa kinga 50/50 kenan ko?"
"Idan har zaka aure ni shikenan hakan shi ne muradi na, i know nothing about the love.....,"
"Shi ya sa na fara nuna miki yadda soyayyar take yanzu ai, cikakken masoyi shi ne mai yin haka idan ban yarda da ke babu ta yadda za a yi na yi tarayya dake Ridayya" Ta jinjina kai a hankali ba tare da ta ce komai ba a hankali maganganun Zameer na yaudara ke ratsa zuciyarta ya ce
"Ki yi wanka na yi dropping naki gida baby" Da ƙyar ta ja ƙafafuwanta tana rufe Idanu saboda tsananin azabar dake ratsa gaɓoɓin jikinta yana kai wa zuwa jijiyar dake sadar da yanayin mutum a kwakwalwa.
Yana tsaye ya sauya kaya zuwa wani milk ɗin voyel mai manyan zane iya kyau da ɗaukar hankali Zameer ya yi, ya taje sumar kan da comb sai ɗaukar ido take komai nasa dabanne a idanun Ridayya ta yi tsaye tare da shagala da kallon shi.
"Ya dai? Wannan kallon fa Mai so na?" Ta ɗauke idanu sanyaye ta ce
"Ka iya kwalliya ko wanne kaya na yi maka kyau ina son yadda kake dressing" Ya ɗan taɓe fuska yana lumshe idanunsa can ya riƙe ƙugu ya ce
"Oh hello na fahimci ke kalmar _I love you_ wahala yake miki ban taɓa ji kin ce Zameer i love You ba, sai dai a ce na yi kyau? To ki riƙe yabon nikam yau kalmar soyayya nake buƙata wajan ki" Cikin yanayin da ya zame mata ɗabi'a ma rashin son magana da sanyin jiki ta ce
"To ai ban san me zan ce ba, Abbiey kawai nake iya cewa ina son shi" Ya watsa idanunsa cikin nata can ya ce "Say something different....,"
"Rayuwata"
Ya juya da sauri jin sunan da ta ce ya dinga binta da wani irin kallo can ya saka hannu ya cira ta sama yana zagaye da ita ya ce "Oh wow gaskiya I'm lucky person, irin wannan suna haka say it again"
"Rayuwata"
"Mai sona" Ya faɗa yana kallon idanunta da suke a lumshe komai nata a nutse yake hatta muryarta golden voice Ubangiji ya bata, idanunta sexcy eyes ne irin nasu kyau da tsari shi sam har lokacin a gigice yake da lamarin Ubangiji, yadda take da muni daban yadda Allah ya sanya ni'ima da baiwa a jikinta daban, ya kasa mance irin tagoma shin lagwadar daɗin daya kwasa, sanda ya fara kai hannunsa zuwa jikinta ya girgiza the real definition na jin daɗi fata mai kyau ita ce Ridayya's skin bashi da ƙarfin qiwwar faɗar taushi da laushi fatar ta, ko'ina ya taɓa lutsum yake nutsa hannunsa babu rama ko misƙata zarratan a jikinta. Lafiyayyen diri mai ɗaukan hankalin namiji gata a sangarce take komai kuka Abbiey ya riga daya lalata Ridayya a ɓangaren shagwaɓa ko tari baya so da ƙaunar yaga tayi hakan bai rufe masa ido wajan tsawatar mata ba idan ta kuskure.

YOU ARE READING
MUNAFUKIN MIJI
RomanceNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...