Page 30

1.2K 63 20
                                    

Zazzare Idanu ta yi sai ta ji wani iri ta kasa kallonsa sunan Oum-Bilal ya yi mata wani iri. Sakin ta Ustaz ya yi bayan ya gama zuge mata zip ɗin data mance bata rufe ba, wanda shi ne dalilin biyo bayanta da kuma kusancin da suka samu wanda a tunaninta rungumeta zai yi.

Ya ja baya tamkar bashi ya yi magana ba ya ce

"long time Sayyada, irin zuba kyau haka?"

Ridayya ta kasa ɗago kanta dake ƙasa tsoro da kunyar Abbiey ɗin ya mamaye mata zuciya, tunanin hukuncin da zai yi mata a kan Sadauki kawai take yi, daman yasan tana nan amma ya kasa nemanta cikin shekarun nan ko watanni?

"Zo mana"

Ustaz ya furta a taushashe bayan ya gama daidaita zaman shi a saman gefen gadon ɗakin nata idanunsa a kan wayarta dake ringing an rubuta “Sahibi”

Ta ƙarasa tare da zubewa a gabansa ƙasan ƙafafuwansa ko zama ta kasa bakinta na rawa ta ce

"Ina yini Abbiey?"

"Allah ya yafe miki Ustaza ba haka muka saba ba kin ji ko"

Hannunsa na dama ya miƙa mata a hankali ta ɗago kanta tare da cira hannunta na dama ta miƙa masa sukai musabaha ya riƙe ɗan mitsitsin hannu idanunsa zube a fuskarta ya ce

"Assalamu'alaiki"

"Wasallamu'aika Abbiey"

"Sannu Oum-Bilal kina lafiya dai? Komai ƙalau?"

Ta jinjina masa kai ya zame hannunsa yana yin baya ya jingina da jikin frame wasu sakanni ya ɗauka kafin ya ce

"Masha Allah. Rabbi ya yi miki albarka"

"Amin"
Ta yi shiru na rashin abin faɗa banda harbawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta ke yi mata, a kullum Ustaz na yi mata kwarjini amma na yau na musamman ne ya sauya mata gabaɗaya babban abin ba wani sauyin kamanni a fuskarsa banda shekaru da ƙasumba daya ƙara da yawan sumar kai, sa nutsuwarsa da tarin kamalar daya sake mamaye gangar jikinsa ga wata Ilham ta musamman. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci da ransa da lafiyarsa hankalinsa kwance yake gudanar da mu'malarsa babu damuwa da tunanin yarinyarsa bata tare da shi bai san hali da ƙuncin data shiga ba.

Baya kallonta a zahiri sai sai dai da idanun zuciya yake kallon yanayinta shi bai ma san yaushe ya riƙe ta taɓa ɗazo kawai yasan ba zai zuba Idanu ta fita riga a buɗe ba. Duk suka yi shiru kowa ya kasa magana sai bugun zuciyarsu dake aiki so yake ya tambayeta ina mijin nata? Ya akai ya neme ta ya rasa.

Mahmah ce ta shigo ɗauke da Little dake kuka sosai tana faɗin "Mimi gashi ya addabi jama'a da kuka kin san halinsa idan ya fara kuka sai kin bashi ya sha hankalinsa yake kwanciya"

Ridayya ta kasa amsar Little ita kunyar Abbiey take yaga wai wannan ita ta haife shi kenan ya san me ta yi ta samu ɗan?

"Ina magana kina jin yaro zai fasa kunnen mutane?"

A marairaice ta ce "Mahmah ki riƙe shi zai yi shiru fa"

Daƙuwa ta yi mata ta ce "ungu wannan dan gidanku idan ke ba ki sha nonon uwa ba sai aka ce shi kar ki bashi? Saboda wa Allah ya hallici nonon banda yaranki? Bafa don a do aka mallaka miki su ba. Naga kullum kina bashi yanzu iyayi ne ko san a sani? Karɓe shi ni"

Idanunta tuni ya yi raurau hawaye ya cika su wacce kalar mafisa ce Mahmah ke shirin janyo mata don abin kunya?
"Don Allah Mahmah wallahi....,"

Ustaz dai da kunne yake ji ko ɗaga kai bai yi, he just pretend kamar bai san mene faruwa ba.

Ajjiye mata shi ta yi a cinya Mahmah na fita da halin yaran yanzu ta yi waje abinta don ita har zuciyarta bata ɗauka ta yi wani laifi ba.
Little ya dinga kuka yana zura hannunsa cikin rigar Ridayya alamar dai a matse take har da haura ƙafa kukan ya yi wa Ustaz wani iri a ka domin har ƙasan zuciyarsa yake jin kukan na Little ya ɗago kai yana haɗe fuska ya ce

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now