Page 10

807 43 7
                                        

*Ta ina zan fara ne? Ta haɗuwar Ridayya da Zameer a jami'a ko kuma ta amintarta da ƙawarta Mardiyya? Ko dai na fara ta riƙon da Ustaz Bilal ya yi mata, girman ƙaddarar nada faɗi, al'ajabinta na da girma, dafin ƙaddarar kan iya harbar kowa, babu kuma wanda akai wa shamafiki da zubar hawaye.  lissafin ƙaddarar zai fi tafiya daidai, idan muka fara da tubalin ginin, ya sanya zan fara da sanda Ridayya Bilal Mansur Rano ta zo duniya!*

Gabaɗaya suna tsaye sun yi carku-carku yanayin sauyin fuskokin kowa zai labartawa mai kallon su akwai lauje cikin naɗi, abu biyu ya sanya zuƙatansu cikin halin da suke, dukda bai cancanci ace akwai damuwar da kan iya hana fara'ar fuskarsu bayyana ba, duba da tagomashin abin alherin daya samu zuri'ar Mai ran ƙarfe a safiyar yau ta juma'a. A kuma unguwar Darmanawa dake Jihar Kanon Nigeria.

Ciwo ɗaya idan ya samu mutum ɗaya a familyn, to kamar ya shafi kowanne daga cikin ahhalin ne kasancewar su, marasa yawa da girma, kowa a hargitse yake idan ka ɗauke Alhaji Mansur Rano, wanda ko zuwa cikin asibitin bai yi balle a san halin da yake ciki. Shekaru aru-aru bai taɓa nuna rashin kulawa akan jininsa ba sai yau, ranar da kowa ya girgiza ya kuma ji a jikinsa tare da shakkar Alhaji Mansur Rano, jinkimarsa da ainahin ɓoyayyiyar siffarsa ta bayyana, wacce ta nuna asalin halinsa wanda inuwarsa ta lulluɓe tare da yi wa jama'a katanga da ita. Reception ɗin asibitin a cike yake idan ka ɗauke wanda baya garin ma. Dr ya fito da sauri yana goge zufar data yanko masa, cikin sauri kuma Hajiya ta miƙe tare da tarar shi tun kafin ya ƙarasu.
"Likita ya ake ciki? Yarinyar nan har yanzu, ba amo ba labari wacce kalar naƙuda ce wannan?" Dr ya yi jim sai kuma ya ce "Sai haƙuri Hajiya..,"
Jikin Hajiya ne ya fara rawa nan da nan ta nemi rikicewa zuciyarta na bugawa ta ce "Ka...ka.. kamarya sai haƙuri? Kada ka kuskura ka ce mini Fatima ta rasu, kar ka ce mini na rasa surukata da abinda ke cikinta?" Ƙoƙarin yi mata bayani yake amma bashi da zarafi da ƙarfin qiwwar yin haka, shi kansa bashi da tabbaci wacce ake magana tana raye ko ta mutu ne. Amma ce ta share hawayen dake gudana a idanunta ta miƙe da ƙyar ta nufi inda Hajiya ta cakume Likitan tana surutai.

"Hajiya ki sake shi please, ki bari mu ji me ya zo da shi, allow him to talk" ta rarrashi Hajiya kana ta dubi likita ta ce "Dr meke faruwa? Ya jikin Fatima?" A karo na wajan uku ya ƙara girgiza kai ya ce "Tsakani da Allah tun yaushe ne ta fara naƙuda?" Amma ta yi jim ta ce "Bana ce ba gaskiya, Fatima ai zurfin ciki gare ta, kodayaushe cewa take lafiya lou take meke faruwa?"

"Follow me Maaa"
Amma ta ce "A'a batun na biyo ka bane, bani da kuzarin hakan ma kawai ka faɗa mini halin da ƴar'uwata ke ciki" Dr ya yi jim sai kuma ya ce
"Har yanzu bata sauka ba tun jiya da kuka kawota, maganar da ake mun fidda rai da ita, wasiyya take bayar wa kuma tana buƙatar ganin mijinta, don Allah ku kira shi tana cikin wani hali" Amma ta yi baya tana shirin zubewa Zuhura ta yi saurin tare ta ta ce
"Subuhanallahi,  take it easy Amma In sha Allah babu abinda zai faru sai abinda Ubangiji ya ƙadarta" Da dugu Amma ta nufi Emergency room hankalinta baya jikinta, kai tsaye ta hankaɗe likitocin da suke wajan tare da faɗawa cikin ɗakin. Abinda idanunta suka gani ya yi matuƙar gigita ta, ta nufi gadon tana cewa

"Ba mu yi haka dake ba Fatima, kar mu fara ba ki taɓa ce mana mutuwa za ki ba, mata nawa suke aure su ɗauki ciki, su yi rainonsa kuma su haife lafiya su shayar da abinda suka haifa? Ba za ki mutu ba, da gaske ba za ki mutu ba Fatima" Amma kuka take sosai domin bata taɓa ganin naƙuda irin ta Mami ba, jijjiga take idanunta ya zazzaro waje harshenta ya zazzago sai fisga take kamar mai aljanu, likitoci ne suka fitar da Amma ta nufi reception hankali tashe, Junaid ya tari Ammi da cewa.
"Ammi ya kike kuka haka? Kar ki ce mana wani abu ya samu Mami don Allah" Ammi ta dake ta share ta ce "Junaidu kira mini Baffanku kada ƴar mutane ta rasu na shiga uku"

"Kamarya ki shiga uku Ammi?" Amma ta kalli Zuhura ta ce "Wallahi idan Fatima ta mutu na shiga uku, ba za a taɓa ganin laifin Alhaji ba nawa za a gani, duk duniya gani ake kishiya azzaluma ce, ban san meke damun mahaifinku ba Zuhura wallahi ban sani ba" Hajiya rai ɓace ta kalli Junaid ta ce
"Wa kake da suna? Mu je can wajan uban naku" Ya yi sururu sai kuma ya bi bayanta, mota ya buɗe mata ta shiga, shi ma ya shiga ya nufi gida da ita.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now