Page 18

780 49 11
                                        

Ustaz ya bi Ridayya dake kwance a ƙasa tana juyi da mummurɗewa zuciyarsa na ƙoƙarin tsinkewa ganin kumfa na fita daga cikin bakinta ta abu kamar bugun jinnu "Ustaz ya haka ka zubawa yarinya ido cikin wannan hali, haba babban mutum" Umma ta furta tana ƙoƙarin kai hannunta jikin Ridayya. Ya furzar da iskar bakinsa ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ya ce "Karki taɓa ta"

  "Kamar ya?" Ya ɗan marairaice fuska kamar an yi masa dole ba tare daya kalli Umma ba ya ce "Hausa fa na yi, da gaske Hausa ce Umma" Ta girgiza kai ya juya a hankali tare da ɗakko hiraminsa ya rufe jikin Ridayya da shi, bakinsa na motsa wa a hankali yana mai yin addu'a tare da tofa mata.

Can ta saki fitsari a saman carpet yana bin cibiyoyinta. Ustaz dai na tsaye haka Umma na kallon abin al'ajabi domin ba'a taɓa yin farfaɗiyya a gabanta ba sai yau. "Ikon Allah, Allah ya sauwake daman haka take yi kenan? Baiwar Allah" Tausayin Ridayya duk ya mamaye mata zuciya bayan matsalar gidan uba gata zubin halitta, gata gorin kalar munin da ake mata, ga makarantar babu daɗi. Uwar data haifeta ma sam bata damu da ita ba, balle kuma uba, wata sabuwar ƙaddarar na lalura ita kanta ba ko wanne namiji ne yake ƙaunar mace mai farfaɗiyya ba, ga shi ƙanwarta Zainura kamar ba jini ɗaya ciki ɗaya suka fito da Ridayya ba haka take nuna mata.

Da ƙyar ta buɗe idanu saboda tsananin kunyar Umma da Abbiey wanda yake tsaye har yanzu, ita bata san lokacin data faɗi ba gashi duk sanda ta yi hakan sai ta yi fitsari a kwance. Basu san ta dawo hayyacinta ba sai sautin kukanta suka ji wani irin raunataccen kuka bai taɓa zuciya. Ustaz ya runtse idanunsa saboda wani irin dokawa da zuciyarsa ke masa, a hankali komai na jikinsa yake sage wa kansa ya fara sara masa da wani irin ciwo. Ya saka hannu yana dafe kan tare da furza goshinsa.
Can ya juya a ɗan fusace kamar zai yi faɗa sai kuma ya tausasa murya, daga ƙarshe ma ya rufe bakin ya fasa faɗar abinda ya yi niyya.

Yatsu ya kaɗa mata yana gyaran murya ta miƙe da sauri tana bin bayansa da sanyin jikin daya zame mata jiki komai nata a sanyaye yake yadda take tafiya kamar bata so haka take yi ko gudu bata iya ba, muryarta kodayaushe a ƙasa ba hargagi so silent, innocent gril. Ta yi jim tana leƙen bedroom ɗin can kuma ta shiga tana furta "Assalamu alayka"

Babu tabbacin ya amsa kawai tana da yaƙi nin dole zai amsa idan har ba ta yi sallama ba baya kula ta duk kalar zancen da za ta yi masa. Ganin yadda ya yi tsaye a bakin wardrobe bai kula ta ya saka Ridayya ƙara fashewa da kuka tana yarfe hannunta
"I am sorry Abbiey, ban san na faɗi ba, ban san na yi fitsari ba Allah"

Ustaz ya juya ya kalleta idanunsa duk ya shige ciki sai ya girgiza kai a hankali ya ce "Yaushe Ustaza za ta girma?" Da sauri ta ce "Yau Abbiey" Sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ai ba zan girma ba, ai dabbobi basa hankali ni ma ba zan yi ba" A rikice Ustaz yana riƙe jarumarsa ya juya ya kalleta da kyau kana ya yi baya a taushashe ya ce

"You said that?"
"Zainura ce Abbiey" Ya yi shiru tana shassheƙar kuka sosai ta kama hannun Ustaz ta ce "Abbiey da gaske wai tsinto ni a kai ba nan ne gidanmu ba? Abbiey you're my father ko? Ammi ce Ya haife ni ko?" Ustaz ya rasa wacce amsa zai bawa Ridayya wacce za ta yi daidai da tunaninta ya fahimtar da ita ƙaddarar ta ce ta zo a haka? Ya nuna mata babu wanda ya isa ya ja girman ƙaddara, komai lokaci akwai sanda za ta shige. Bai dawo daga tunanin da yake ba ya ji ta saki ajjiyar zuciya.

"Abbiey mene kwaila kuma? Yau da muna yin final exam ina murna wata ce mini wai na daina murna jss 1 a dawo dani saboda ni kwaila ce kuma Kangaroo basa zuwa University. Abbiey mene kwaila kuma mene Kangaroo?" Ustaz ya yi shiru yana son Ridayya ta fahimci abubuwa da dama amma babu mai faɗa mata, babu mai nusar da ita shi ya sa wani lokacin idan ta yi magana yake girmama wawtar ta, da tunanin har yanzu ita ɗin yarinya ce gata ƴar'fari ga lalura abin ya yi mata yawa. Jin ya yi shiru ta sake marairaice fuska ta ce

  "Abbiey mana, please"
Ya kama hannunta tare da janta saman kujera bayan ya zauna ta, zauna a ƙasa wajan ƙafafuwansa kan ta a ƙasa shi kuma ya zuba mata ido, yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da ƙarfin gaske abubuwa da yawa na farmakar shi. "Ustaza" A sanyaye ta ce "Abbiey"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now