MADUBI
©AYEESH CHUCHU
(NWA)1st January, 2017.
BABI NA DAYA
Rakuɓe ta ke jikin kofar ɗakin, ruwa ake tsugagawa kamar da bakin kwarya. Jikinta na ta kyarma kamar ana kaɗa mazari, ji ka ke hakoranta na ba da sautin gab-gab-gab!
Gajiya ta yi da tsayuwar, ta zauna dirshan saman simintin da ke zauren, hawaye su ka tsiyayo daga kwarmin idanunta.
Sanyin simintin da iskar da ke hurowa ya tashe ta, a hankali ta bude manyan idanunta wadanda su ka rine zuwa kalar ja (red) alamar ta sha kuka har ta gode ma Allah.
Ji ta yi ta kasa motsa sassan jikinta saboda tsabar daskarewa da su ka yi dan sanyi.
Kamar daga sama ta tsinkayi muryarta "Subhanallahi! Ammah mi ki ke yi kwance kasa haka?".
"Gwaggo na dawo daga makarantar allo na iske dakin ki rufe, na shiga ɗakin Inna ta koro ni, shi ne ina nan zaure aka fara ruwa".
Girgiza kai ta yi cike da jin haushi.
"Yi hakuri taso mu shiga cikin gida ni da Innar ta ki".
Da taimakon Gwaggo ta tashi saboda jijiyoyinta da su ka rike tamau.
Dakin Gwaggo su ka shiga, Ammah ta kwanta.
"ki cire wadannan kayan jikin na ki, ki canza wasu ina zuwa ".
Kai ta kada ma ta.
Dakin da ke kusa da na ta ta yi sallama ta shiga.
"Gwaggo barka da dawowa, ya mai jikin?".
Gwaggo da ke tsaye ta ce "ba shi ya kawo ni ba. Yanzu tsakani da Allah abinda ki ke ma yarinyar nan Ammah kin kyauta kenan? Kina sane da cewa hadari ne garin ki ka korota daga ɗakin ki, ina da shakku akan kaunar da ki ke ma gudan jinin ki Ammah!".
"Gwaggo ni dai dan Allah in dai magana ce da ta shafi Ammah ki daina kawo min, ba zan iya abin kunya ba".
"Muna ga rasulu mata sun ki maza! Mairo hankalin ki guda kuwa? Ai shikenan ki yi duk abinda ki ka ga dama. Har da laifin Malam wallahi da ya zuba ma ki ido kina wannan sakarcin".
Ita dai ba ta tanka ba, kanta a kasa har Gwaggo ta gama bambaminta ta kara ma bujenta iska.
***
"Gwaggo ina son yin karatun boko, yaran gidan Mal. Mati na burge ni, bare in gansu cikin kayan makarantar su kore da fari (green & white) kamar in kwace".
"Ki yi hakuri Ammah kin san halin Malam sarai ba kaunar karatun nan na boko ya ke ba, tun yaushe ni ke mitar ya sa ki makarantar ya ki, har mai gari da kan shi sai da na je na same shi kan maganar amma abin ya ci tura. Ki cigaba da addu'a kin ji ni ma zan taya ki Allah ya cika ma ki burinki ki zama TAURARUWA a kasar nan ba ma a kauyen nan ba".
Murmushi ta yi tare da gyara kwanciyarta, ta yi matashi da kafar Gwaggo. Ta na jin kaunar Gwaggo har cikin ranta, har bacci ya kwashe ta.
***
Garin ya yi shar! Iskar damina mai sanyi da kamshin kasa na kaɗawa. A gefe guda Ammah ce wanke-wanke ta na bitar karatun littafin AHLARI da akai ma su a makarantar islamiyya.
Inna da ke madafi (kitchen) tana taya Gwaggo dama kokon safe. Murmushi dauke a fuskarta, Gwaggo na lura da ita.
Gwaggo ta ce "Ammah akwai kokari da wuya ka ji ta shiru ba ta bitar karatu".
Inna ta yi shiru ba ta ce komi ba, ta na jinjina abin a ranta.
Har ta idasa wanke-wanken ba ta daina bitar karatunta ba.
Gwaggo ta ce "Ammah, Mubarak, Yusuf, Abdullahi ku zo ku dauki abincin ku".
Kowannen su ya dauki kofin kokon shi.
Ammah ta ce "Mubarak dauko langar tuwon can ga tabarma can na shimfiɗa ma na".
A tare su ka zauna, sun zagaye langar tuwon su na ci tare su hudu. Haka su ka kammala karin kumallo.KARFE BAKWAI DA MINTI ARBA'IN DA TAKWAS (07:48am)
Ammah ce ta fito sanye da hijabinta, ta rataya jaka a kafadarta.
Ammah ta ce "Mubarak ku fito mu tafi kada a tare mu mun yi latti Malam Habu ya tare mu".
"Gwaggo mun tafi sai mun dawo".
"Toh Ammah Allah shi bada sa'a,ki dage da karatu kin ji".
"Toh Gwaggo tah".
Ta yi murmushi su ka kama hanyar tafiya islamiyyarsu.
Akalla sun yi tafiyar mintuna biyar kafin su isa makarantar islamiyyarsu, wadda ta kasance makarantar firamare (primary) ce ta gwamnati wadda akai ma lakani da MODEL PRIMARY SCHOOL. Kowannen su ya shiga ajin da ya ke.
Ammah ta wuce ajinsu.
"Ammah ga waje nan na ajiye ma ki, ki zo mu yi bitar haddar da aka ba da kafin Malam ya shigo".
Ammah ta ce "Sa'a kar dai ki ce mun ba ki yi haddar da aka bada ba?".
Sa'a ta ce "Na yi ya ki zama ne, ki zauna mu maimaita ba ni son wannan dorinar ta shiga jikina".
Nan su ka fara maimaita karin Al-Qur'ani da a kai ma su, har sai da Malaminsu ya shigo su ka dakata. Ya amshi haddar su daya bayan daya. Ya bulale wadanda ba su kawo haddar ba. Bayan an gama amsar haddar ne aka kara ma su wasu daga cikin ayoyin Al-Qur'ani mai girma su na ta maimaitawa har lokacin tashin su yayi.
KARFE GOMA NA SAFE (10:00AM)
"Ammah sati mai zuwa zan zana jarabawar shiga makarantar gaba da firamare".
"Na taya ki murna Sa'a, da ma ni ce ke".
"Za ki yi karatun nan ke ma Ammah ki kara tambayar Babanku".
"Sa'a ba zai bari ba, Gwaggo har mai gari ta faɗa ma wa, amma ya ki yarda". Tare su ka jero su na tafiya, kannensu na gaba su na biye da su a baya.
***
Tun bayan maganar da Ammah su ka yi da Sa'a akan makaranta abin na ta damunta, ta na son ta yi karatun boko sosai.
Tire (tray) ta dauko na silba (silver) dauke da kwanon abinci da kofin ruwa, ɗakin mahaifinta ta shiga ta ajiye ma shi, ya na kwance ya na lazimi.
Ta gaida shi tare da zama.
Ta ce "Baba". Ya dago ya kalle ta.
"Ammah lafiya?".
"Baba dan Allah kara rokon ka zan yi ka bar ni in yi karatun boko".
"Ina tunanin mun rufe wannan babin Ammah, kin dade da sanin cewa ba zan bar ki ki yi wannan karatun na nasara ba, ba ni son tarbiyyar ki ta lalace, ki je ki koyo wa su al'adu can wadanda za su sa ki watsar da ta ki al'adar. Ba zan so hakan ta faru da ke ba, na fi son ki yi auren ki, ki zama mace ta gari wadda ya'yanta za su yi alfahari da ita. Amma bokon nan na tsane ta Ammah, ta yi ma na tabo a cikin zuri'ar mu".
Tashi ta yi ta nufi ɗakin Gwaggo,ta na jan kafa da kyar saboda tsabar sanyi da jikinta ya yi.
Kwanciya ta yi ta na tunanin tabon da Babanta ke cewa boko yai ma su a cikin zuri'ar su da har zai zama sanadin hana ta karatun boko, zuciyarta ta ayyana ma ta cewa Gwaggo ce kadai za ta amsa ma ta tulin tambayoyin da ke cunkushe cikin ranta.
Kamar daga sama ta ji muryar Gwaggo na cewa "Ammah lafiyar ki kuwa? Ina ta magana shiru".
"Ban san kin shigo ba Gwaggo".
Gwaggo ta zauna gefen gadon ta ce "akwai abinda ke damun ki Ammah ki faɗi man in ji damuwarki".
"Gwaggo da ma ɗazu ne na kara ma Baba maganar makaranta, shi ne ya ce ba zai bar ni ba saboda tabon da boko tayi ma zuri'ar su."
"Tunda kika ji haka ki hakura Halimatu idan Allah yayi da rabon ki yi sai kiga kin yi, yanzu dai ki dage da ilimin addini da ki ke nema shine ginshikin kowacce rayuwa, idan kika same shi rayuwarki za ta saitu, ta dalilin shi kiga buɗi da rahamar Allah baibaye dake. Ki zama mai juriya Halimatu, tunda ya nuna bai so kar ki sake ma sa magana, ban son ki zama cikin jerin mutane masu nacin magana".
"Toh Gwaggo In Shaa Allahu na daina ki cigaba da yi mun addu'a".
Ta girgiza kai tausayin Ammah ya kamata, tana jin a ranta kamar tayi gaban kanta ta sa Ammah makaranta. Sanin halin mijinta yasa ta wofintar da maganar, tunda ta gama nacin ya ki amincewa da bukatar su.04:56PM (KARFE HUDU DA MINTI HAMSIN DA SHIDA NA YAMMA)
Karatun Al-Qur'ani mai girma da sauran karatuttuka na addini ke fitowa daga cikin islamiyyar.
Ajinsu Ammah ne sautin Al-Qur'ani mai girma ke fitowa daga cikin suratul Nisa'i {04:79} Inda Allah SWT yake cewa "Abin da ya same ka daga alheri, to daga Allah yake, kuma abin da ya same ka daga sharri, to daga kanka yake.......".Bayan sun gama ne biya karatun ne a ka fara amsar hadda.
Har aka zo kan Amma da Sa'a sun bayar da haddar tiryan-tiryan, gyara kadan aka yi ma su.
Bayan an tashi su ka taho ita da kannenta, suna gaba, ita da Sa'a a baya suna firarsu ta aminan juna.
"Ammah kin gane wani sabon dalibi dan ajin Uthman Bin Affan (ajin hadda), mai kyau dan gayu?".
"Kai Sa'a yanzu har kin san sabon dalibin da aka kawo, harda kare ma sa kallo".
"Ke ba ki ga kyan shi ba, ina jin Ameera na maganar shi, yana da kyau daga gani dan gayu ne".
"Idan Ameera tayi maganar shi ai ita ta san abin da ta taka, yar gidan masu kuɗi ce, kin san ko magana ba ta taɓa haɗamu ba".
"Ai ke halinki Ammah sai ke ba ki son shiga mutane, duk islamiyyar nan ba zance ga kawarki ba".
"Toh Sa'a so kike in shiga inda za a wulakanta ni? Kin san halin mutanenmu, babu mai son ya raɓe ni dan ni ban waye ba, banyi karatun boko ba. Ke kadai ce ke deɓe mun kewa, idan kika tafi makarantar kwana ban san yanda zanyi ba".
"Ba komi Ammah, wata rana sai labari, In Allah ya yarda wata rana mafarkinki zai cika".
"Allah shi tabbatar Sa'a".
Da haka suka isa bakin kofar gidansu Ammah, Sa'a ta wuce gida.I'm back with another story.. Shower me with your votes and comments.
I so much love you..
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...