MADUBI
AYEESH CHUCHU"Ina za ki je haba haba amarya, bikin na ku ne, ki bar ma su zarya. Ki dau shawarar iyaye amarya. Ki mance zigar ƙawaye a baya, haba haba amarya mai ladabi biyayya, ki bi sahun mijinki amarya ki yi ɗoki, dan aljannarki tana kafar mijinki, riƙe hannun mijinki amarya ku tafi tare".
Amarya By Ado GwanjaKOMI YA YI FARKO...
Murmushi ya sakar ma ta, tare da lumshe ido.
Su ka cigaba da magana da Gwaggo. Ɗakin su Mubarak a ka shigar da shi.
Ta shige ɗaki.
"Ga Ya ARK nan ya zo ".
" Ya ARK?"
"Eh miye na zaro idanu".
"Ke ya biyo kawai".
"Ke kam anyi kilibabba. Ni Ya ARK zai biyo ko a mafarki".
"Wai dan be faɗi cewa yana son ki ba ko me?".
"Shi fa na daban ne. Dan haka salon soyayyar sa ma ta sha bambam. Hajiya action kawai za ki duba".
"Ko a action koma adventure ne ban gani ba".
"Tunda dai ke kina son Yayanah ai shikenan ".
" Allah ya isar min".
Dariya Laila ta yi.
"Ammah ".
" Na'am Gwaggo ".
Ta fito.
" Kai ma Abdurrahman abinci da furar nan".
"Amma dai Gwaggo kin san cewa furar mu ce koh? Shi fa be ce yana shan fura ba".
"Yau naga Ikon Allah! Yaushe ki ka koyi rowa Ammah?".
"Ni fa ba rowa na yi ba".
"Gidanku ki ka yi. Watau haka za ki riƙa yi a gidan ki, sai kin tambayi baƙo idan zai ci ko sha abu. To bari ki ji tayin rowa ne".
"Uhmmm.. ".
Haka Gwaggo ta miƙa ma ta tray ta shiga dakin su Mubarak da ke zaure.
Tayi sallama aka amsa ta shiga.
Ajiye tiren ta yi za ta juya.
" Malama ki yi serving ɗina".
"Ina ga dai haka ka ke cin abincinka?".
"Yanzu ai ga ki kuma aikin ki ne".
Hararar shi ta yi. Ta zuba ma sa dafa dukan shinkafa da wake ta sha alayyahu da kifi. Sai ƙamshi ta ke.
Ta zuba ma sa fura, ta jefa ƙanƙara ciki da aka fasa.
Ta fita daga ɗakin kamar ana korarta.
Murmushi ya yi.* * *
ABUJAAmmah ta fara aikin bautar ƙasarta a Management Sciences For Health (MSH) a matsayin Operations Assistant.
A gefe guda kuma ta na gudanar da NGO ɗinta.
Bikin su ya rage saura wata ɗaya.
Zaune ta ke a ofis ɗinta ta na aikin da Operations Manager ya ba ta a na'ura mai kwakwalwa. Ta gama komi ta yi compiling ta sa ka a fayil, ta fita daga ofis ɗin ta kai ma sa.
Matashi ne da be wuce shekara talatin da uku ba. Baƙi ne amma baƙinsa mai kyau, ƙaƙƙarfa ne.
"Mr. Ahmad ga shi na gama". Ya amsa
ya hau ƙura ma ta ido yana ma ta kallon ƙurilla. Ta ƙara daure fuska tsam.
Ya ɗan duba fayil ɗin sannan ya ce "Ya yi kin yi ƙoƙari".
"Thank you Sir".
"Idan ba za ki damu ba, ko zan samu rakiya fita lunch?".
"Nah! Akwai aikin da aka turo zanyi so na ke inyi shi in time, yau ban son kaiwa 3pm".
"Ba wani nisa za mu yi ba, Just abinci za mu ci. I really want your company ".
" I'm so sorry please".
Ta juya za ta fita.
"Wai ke ba ki waye ba ne ba? Mata nawa ki ka san su na so in fita da su lunch a wajen nan. Dan ma kin ci sa'a na ce zan fita da ke. Kuma dai kina da qualities ɗin da nake so ga mace, ga ki Full option".
"Dan Allah in daina cin sa'ar, na ji ban waye ba in dai wayewar da ka ke nufi kenan. Miye haɗi na da kai da zan bika fita? Ta nan ka bullo kenan?
Let me tell you ko fiance ɗina ba zan iya fita da shi ba wani lunch ko dinner. A da ina ganin mutuncin ka, ka ɓarar da wannan mutunci.
How will you feel wani ƙato can ya ce ma ƙanwarka ta fito su je cin lunch ya faɗa ma ta makamanciyar maganar ka? ".
Shiru ya yi, ya kasa magana.
" Ta Allah ba taka ba. Ko kallo na ka kara yi ban yafe ba. Idan ka so ka daina abinda ka ke yi wannan tsakanin ka da Ubangijinka ne. Amma ka sani cewa duk abinda ka yi ma ƴar wani sai an ma taka, ko ƙanwarka kai koma wani naka. Irinku ke jawo mana duk masifun da ƙasa ke ciki wallahi. Ga dokokin Allah a bayyane saboda son zuciya da nuna wayewa ku kauce ma sa.
Ko kuwa arziƙin da ya ba ka ta haka za ka gode ma sa? Maimakon kuɗin da ka ke kashewa mata da amfani ka yi dasu wajen gyara lahirar ka yanda zasu ma ka amfani a gobe ƙiyama.
Allah fa da kansa ya ce ya ba ma su kuďi mabuɗin aljanna. Ka ga kenan ya rage na ka kayi aikin nemo makullin da dukiyarka.
Haka a zamanin Annabin Rahma talakawa sun zo sun sami Annabi SAW cewa ma su kudi fa sun kwashe lada,suna sallah kamar yadda mu ke, suna fita jihadi, suna azkar masu daga darajar ɗan Adam, suna bada zakka da sadaƙa mu kuma ba ma yi.
Kadan fa kenan daga cikin falalolin da Allah ya yi ma ka. Kar ka yi tunanin ina ƙasa da kai na ci ma fuska, a'a I'm just telling you the truth as a Muslim sister.".
Ta fita daga ofishin.
Dafe kansa ya yi, yana mamakin ƙarfin halin Ammah. A tarihin shi be taɓa tunkarar mace ta ƙi shi ba. Jikin sa ya yi sanyi sosai,ya matukar girgiza da kalaman Ammah.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...