KUSANCIN JUNA

2.2K 183 75
                                    

MADUBI
   AYEESH CHUCHU

   "A so da ƙaunar juna zan so a ce kin tausaya min, ko min wuya da dadi ni da ke a ce ba za mu rabe ba. So da ƙauna da amana zuciya ta na son lallashi kawalwalniyar soyayya ta shige mani ruhina".
~~Kawalwalniya By Sa'eed Nagudu

KUSANCIN JUNA

Cikin rashin kuzari ta dau kiran.
"Assalamu Alaikum ".
Daga can bangaren
" Wa alaikumus Salam. Yanzu Halimatu kin kyauta kenan ki haɗa mutane biyu a soyayya. Duk abokan juna. Kin ma kanki adalci kuwa? Idan kin san Ahmad ki ke so tun farko da ba ki karɓi soyayyar Abdul. You disappointed me, ashe haka ki ka iya yaudara ?". Ya faɗa cikin faɗa-faɗa da ɗaga murya.
"Ni mi nayi? I never  did anything wrong. I'm confused please. Ni ban ce ina son kowa ba. I'm busy going on with my life to make my dreams come true. Dan Allah malam ka yi hakuri ba ni bace ba".
Dariya kawai ta ji, wadda cikin jikinta sai da ta ji ta.
"Matsoraciya kawai. Kina magana da Abdurrahman Kabir ".
" Yaa Allah! Ya Abdul you scared the hell out of me. Ashe haka ka ke?".
"I just feel like teasing you. Kin san nayi dariyar da ban taɓa ba, kin cancanci kyauta. Ya shirye-shiryen ki?".
"Toh gashi nan dai, sai gobe idan na koma can In Shaa Allah sun bada sunan, I'll go on with publications and office. Akwai Yayanah da zai handling komi".
"That's great gaskiya ya kyauta. He'll help my little Ammah".
"I'm surprised fa. He's such a different person. Ba zan iya misalta shi ba".
"Ina ga ƙila dai ba ki fahimce shi ba ne. Kin san a lokutta da dama sai ka zauna da mutum ka ke fahimtar waye shi".
"Hakane! Amma dai akwai bambanci tsakanin mutane ".
" Eh sosai ma. Zan turo ma ki format na mission, vision da aims and objectives na kungiyar".
"Nagode kwarai ".
" Kar ki damu, zan tsaya ma ki wajen baki goyon bayan aikata wannan aiki na alkhairi".
"You're such a nice person ".
" Ki bar koɗa ni. Sai da safe".
Ya kashe wayar ta saki ajiyar zuciya.
Nan bacci ya kwashe ta.
  Sai lokacin tashi tayi sallar dare ya yi ta mike. Ta latse alarm ɗinta taga akwatin saƙo.
Ta bude ta karanta. Nan taga abinda yace zai turo ma ta ne. Ta karanta tare da yabawa da kalamansa.
Tashi tayi ta yi alwala, ta kabbara sallah tare da miƙa dukkan natsuwarta da ikilasi ga Allah mai kowa da komai. Tare da miƙa ma Sa zabin rayuwarta.
Ranar ba ta koma bacci har aka kira sallah. Sai bayan sallar asuba ta gama azkar ɗinta na safe bacci ya ta so ma ta. Ko Amaal ba ta tsaya tadawa ta koma bacci.

   ***
Hasken ranar da ya fara shigowa ta jikin labulen ɗakin ya sa ta farkawa, ta kalli agogo tara har ta wuce.
Cikin azama ta yi saurin tashi ta faɗa banɗaki ta yi wanka, cikin sauri ta shirya cikin baƙar abaya mai ratsin fulawowi ruwan ƙasa, ta nannade kanta da gyale mai ruwan ƙasa. Ta fashe kayanta d turaren kaya. Ta dau Jakarta da duk abinda za ta buƙata duk ta cusa ciki.
  Ta fito zuwa falon, gidan tsit ba kowa. Ta leka kicin sai Ladidiya.
"Ina kwana Ladidiya? Banga aunty Ayeesha ta na ina?".
"Ina ga ta koma bacci ne bayan su Amaal sun tafi makaranta. Yau dai kin makara".
"Wallahi ko bacci na koma. Bari in rubuta takarda ki ba ta".
Ta yago daga cikin jotter da ke Jakarta ta yi rubutu ta miƙa ma Ladidiya.
"Ga abincin ki nan fa".
"A'a sai na dawo sauri na ke".
Ta dau makullin mota saman center table ta tafi.
Gidansu Sa'a ta biya suka tafi tare.
Ya ARK ta kira a waya.
"Gani nan na iso wajen".
"Ki shigo ciki ina can inda muka je jiya".
"Ok gani nan".
Ta fito daga cikin motar ita da Sa'a.
Can ta iske shi wajen Director, har an ba shi sunan da su ka zaɓa.
"Ga sunan da su ka zabar ma ki wanda aka duba babu masu irin shi".
A fili ta karanta "Northern Girls Empowerment Initiative (NGEI)".
"MashaaAllah! Wannan ma ya yi ".
Daga nan su kayi abubuwan da su ka dace su ka fito.
" Mu je ki ga office ɗin da nace za'a kama idan ya yi ". Ya faɗa ba tare da ya kalli inda take ba.
Ta shiga mota suka bi shi a baya.
" Ammah wannan hadadden gayen fa?".
"Kai Sa'a kin shiga tara. Yayan Laila ne".
"Naga kama, amma fa yafi su kyau dukka".
"Shiyasa yake dagin kai ai".
"Ni birge ni ya yi. Na sha ganin fuskarsa a social media, ko ba ɗan jarida ba ne?".
"Shi ne ina ga ".
" Ke shi ne fa. Matashin ɗan jaridar da ke tashe. Mutum mai aƙida da nusar da matasa".
"Ke ina ki ka san shi haka?".
"Fuskar kawai na gani, na gane sai ina tantama ko shi ne. A Facebook nake ganin shi, ina following posts ɗinsa. Ana ƙaruwa sosai ".
"Uhmm! A social media yake abin arziki nan a gida yanda ki san dodo haka yake. Ke har fargabar ganin sa na ke, yanzu ne ma da yake taimako na nake dan sakewa".
"Ni kuwa ina ganin shi mutum mai saukin kai, sai dai tsume fuska ko kallona be yi ba fa".
Ammah ta yi dariya.
"Gashi nan kin faɗa ai. Ai naga matarshi za ta yi fama. Har na tausaya ma ta".
Ta faɗa muryarta a karye.
"Anya Ammah kuwa? Wadannan idanun ki fa uhmm".
"Ke dai kin iya munafurci".
Suna hira har su ka iso wajen.
Yana tsaye ya harde hannayensa a ƙirji.
"Ki hau 3rd floor ɗin can, lamba huɗu makulli na nan jiki ki duba idan komi ya yi".
Ta girgiza kai tare da bin umarninsa su ka hau sama ita da Sa'a.
  Sun isa wajen, sun buɗe ɗakuna uku ne a ciki, guda daya babba ne mai kamar falo da bayi a ciki, haka sauran ma. Sai dai su ba su kai shi girma ba.
Sun yaba da kyawun wajen sosai. Sannan su ka sauko.

MADUBI Where stories live. Discover now