MADUBI
AYEESH CHUCHUAisha Sheik, Halima Wasagu and Fatie Babajada (Qawas) this one is for you guys.
BABI NA SHA TARA
ANA KUKAN TARGAƊE* * *
09:34am
"Amma kin yi wauta ba ƙarama ba wallahi, su can asibitin ba su duba ki bane?".
"Gwaggo a gida na haihu".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yau na shiga uku ni Halimatu yanzu saboda tsabar rashin imani gida kika haihu ".
Fuuu ta fita daga ɗakin, ranta ya mugun ɓaci.
Cikin azama ta ɗaga labulen ɗakin, ba ta ko ganin gabanta.
" Yanzu tsakaninki da Allah Hajiya amanar da aka baki kenan? Ashe Ammah gida ta haihu ba asibiti. Kamar ta dai ai yaci a ce an kai ta asibiti, ko a asibitin ma na san ba ƙaramar wuya za ta sha ba. Haihuwar fari kuma yarinya kamarta. Kun ci amana".
"Dakata! Dakata!! Ba za ki zo ki tara mun jama'a a gida ba, mu nan gidan ba'a zuwa asibiti kuma yarinya ta haihu lafiya".
"Toh bari ku ji a da nayi shiru yanzu kam ba zan yarda rayuwar Ammah ta gurbace ba. Yan sanda za su raba mu da ku. Yarinya na can ta na fama da yoyon fitsari, ina kyautata tsammani ma har da ƙari ta samu".
Matan da ke ɗakin su ka hau salati, kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Duk suka fito aka nufi ɗakin da Ammah ta ke.
Kuka take bilhakki dan tana jiyo maganganun Gwaggo da Hajiya.
Hannunta tasa ta ji wajen sharkaf da lema.
Gwaggo ta fizgo hannunta.
"Sanya hijabinki mu tafi asibiti".
"Gwaggo jaririn?".
"Dalla can mu tafi, ina jin dai ba da shi ki ka zo ba. Ki ajiye masu ɗansu mu tafi".
"Gwaggo kiyi hakuri dan Allah a sasanta abin nan". Fadin wata mata.
"Dama ai na faɗa ma ta ta nemawa ɗanta uba. Allah ya gani ba zan iya zama da mai lalura irin ta ta ba. Dan haka idan ta tafi kar ta dawo, ta kuma tafi da ɗanta".
Yana gama furta maganarsa ya fita daga gidan.
Shiru ne ya ratsa gidan, dan maganar da Salisu yayi tamkar saukar aradu haka su ka ji ta.
Gwaggo da Ammah kuka suke,mutane na rarrashinsu.
A zuciye ta tashi ta goya Khalifa, ta kama harhaɗa kayansu da ke ɗakin.
"Asabe dan Allah je ki nemo man tasi (taxi)".
Jama'a aka yi tsiru-tsiru kowa na mamaki da al'ajabin abin.
"Ammah tashi mu tafi, sun gama cutar da ke".
Hajiya da ke tsaye ta kasa magana.
"Halima dan Allah ku yi hakuri,ba a biyewa ɗan yau. Ki bar yarinya ta zauna ɗakin mijinta ta cigaba da haƙuri".
"Eh lallai dole ki ce haka da yake ba ɗiyarki bace ba. Na tabbatar da cewa dibar da ɗanki ke ma Amma abin baya tonuwa, damma yarinya na da hankali. Sannan sai in bar ta a cigaba da zaluntarta. Kina ji yace baya buƙatar ganinta da jaririnta. So kike in bar ta mu dawo mu isko gawarta? Na tafi da Ammah ina jiran takardar sakinta wajen azzalumin ɗanki da ya gaza tausaya ma halin da Ammah ta shiga wanda duk a dalilin auren su ne".
"Dibar albarkar ya isa haka. Nima na goyi bayan ɗana".
"Kukam ku sasanta kanku mana, ai maganar aure ya wuce wasa. Maza ya kamata su shigo maganar, dan ta hula da hula ce".
"Gwaggo ga mai motar nan".
Ba ta jira komi ba, ta dau kayansu suka fita.11:15pm
BAKORI
"Gaskiya Hajiya ba zan yarda sai an wanke mun kujerar motata, ji uban fitsarin da ke jiki".
"Bawan Allah yi haƙuri faɗi kudin wankin in biya ka".
"Dari biyu ne".
Ta fiddo kuɗin ta ba shi a yayin da Amma ke tsaye tana kalle-kalle hawaye na kwaranya daga kwarmin idanunta.
Mubarak ne ya fito cikin sabbin kayansa suna shirin tafiya Karofi suna. "Yaya Ammah".
Sai kuma ya ruga cikin gida
"Inna ga Yaya Ammah nan da Gwaggo".
"Kar dai nan za a yi sunan?".
Sallamarsu ta jiyo, ta kasa gasgatawa.
"Gwaggo lafiya dai koh?".
"Lafiyar kenan Mairo".
Malam Ibrahim ya fito daga turakarsa,ya bi Gwaggo da ido.
Kafin yayi magana har ta ce "Asibiti za mu wuce. Kun kyauta dama haka kuke son rayuwarta ta tagayyara". Ta bar Malam sake da baki.
Daga haka ta wuce ɗakin da Innani ta ke, ranta a ɓace.
"Innani yau ga abin da nake gudu ya faru, yau ga Ammah da lalurar yoyon fitsari ga kuma korar karen da mijin da kike tunanin mijin kwarai ne ya ma ta". Kuka ya kuɓuce ma ta.
Amma ta dafa kafaɗarta.
"Gwaggo hakan ƙaddara ta ce ".
Fitsari ne ya biyo ta ƙafafunta ya sauka ƙasan simintin ɗakin.
Innani ta kasa magana duk da jikinta da karfi.
" An cuci rayuwar Ammah wallahi".
Inna da ke tsaye ta rungume Ammah tana kuka.
"Ammah ki yafe mun, na san ban kyautawa rayuwarki, ba ki samu kulawar da ya kamata na ba ki ba. Ki gode wa Allah da ya baki uwa kamar Gwaggo, a yau na ƙara tabbatar da ƙaunar da ke tsakaninku".
Kukan Innani ya cika ɗakin, ta kasa magana.
Malam ya shigo ɗakin.
"Halima wai me ke faruwa ne?".
"Duba nan ka gani ".
Ta ma sa nuni da wajen da Ammah ke tsaye da ya jiƙe da lema.
" Ki mun bayani mana".
Tiryan-tiryan Gwaggo tayi bayanin abinda ya faru.
Malam ya kalli Ammah "Ammah faɗa mun tsakaninki da Allah irin zaman da ki ka yi a gidan Salisu kar ki boye man komi".
Ta fara ba su labarin tun daga ranar da aka kai ta har zuwa isowarsu gida da Gwaggo.
Zufa ce ke keto ma Malam.
Innani kuka take ba sassautawa, kowannensu fuska cike da tashin hankali.
"Mu tafi asibiti kawai".
"Ibrahim ka ne ma mun yafiya wajen Amma ".
Ba su wani ɓata lokaci ba Gwaggo da Amma suka wuce asibiti.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...