MADUBI
©AYEESH CHUCHU
BABI NA TARA***
Aisha Memorial Hospital suka wuce da Mukhtaar, inda ma'aikatan jinya suka fara ba shi taimakon farko.
Umar ya ciro layin Mukhtar ya sa shi a wayarsa, ya fara bincika contacts ɗin wayar dan ya samu lambar waɗanda su ka fi kusanci da Mukhtar.
Lambar Yaya Habib ya fara cin karo da ita wadda aka adana da "Big Bro".
Ya ɗanna kira, ana dauka yace "An kwantar da Mukhtar mai wannan wayar AISHA MEMORIAL HOSPITAL dake nan Bakori, ya samu accident ne".
Ya datse kiran ba tare da ya jira komi ba, ya zare layin.
Ya zauna kujerar da ke kallon Mukhtar wanda be san a wace duniyar yake ba.
***
"Joni Malam min ngad'anta wajore dou danyuki ? Ko a koid'ul mi tammaki nyandere nde'e warai. Hande mi tabbitini Mairo d'um bandam na d'um laulirawo am". Faɗin Gwaggo kenan ganin idon Ammah a wajen, fuskarta cike da firgici, a yanda ta ji muryar Iyayenta na tashi sama.
"Ammah koma ɗaki gani nan zuwa". Ba musu ta juya.
Gwaggo da Inna su ka mara ma ta baya, kowanne zukatansu dauke da batutuwa, suka bar Malam Iro tsaye ya rasa tudun dafawa.
Tagumi Ammah ta rafka, ta rasa abin da ke ma ta dadi a rai. Tunda ta kwanta ta ke mafarkin Ya MK.
"Gwaggo gabana ke ta faɗuwa, raina duk ba ɗaɗi".
"Ita addu'a kin ji Ammah". Ta gyada kai cike da gamsarwa.
Da taimakon addu'ar da take ta ji zuciyarta wasai, hakan yasa ta tashi dan kamawa iyayenta aikin gida.
Tsintsiya ta dauko ta fara share tsakar gidan ƙal!, sannan ta cika botoci da ruwa ta ajiye ma kannenta.
"Ammah!".
"Na'am Gwaggo".
"Zo nan ki zauna, magana nike son yi da kai".
Kujera ƴar tsugunno ta dauko ta zauna, ta tattara dukkan hankalinta ga Gwaggo.
"Ina so ki kwantar da hankalinki ki dau duk abin da ya faru a matsayin ƙaddara, dama can Allah ya rubuto hakan. Ki dauka mafarki ki kayi kika farka, sai ki shafe duk abin da ya faru. Bani son wannan sukukun da kike yi, kinga tun bayan musabaƙar da ku ka yi baki ƙara zuwa Islamiyya ba, kina son ta dalilin wani abu mara tushe ya zama sanaɗin rushewar ginin da aka fara?".
"A'a Gwaggo".
"Toh ki maida hankali wajen karatunki, tunda Allah beyi zaki yi wancan na bokon ba. Ba ni son kina nuna damuwarki, ki bar komi a hannuna babu abinda zai gagara da izinin Allah".
"In Allah ya yarda zan kiyaye Gwaggo".
"Tashi ki cigaba da hidimarki, Allah shi ma ki albarka".
Murmushi ta yi ta amsa da "Amin".
Inna da ke saurarensu ta maye kujerar da Ammah ta tashi, ta ce "Gwaggo ba ni da bakin da zan goɗe ma ki sai dai addu'a a tsakaninmu, kin ba wannan yarinya duk wata tarbiyya da gatan da uwa ke bama ƴaƴanta. Kinyi abin da ni da na haifeta ban ma ta kwatankwacin haka ba. Kin kyautata ma ta fiye da tsammani na, ki yi haƙuri da abin da Malam yace, tuntuɓen harshe ne. Ba ta da uwar da ta wuce ke, ke Ammah ta sani, kece uwarta. Na mallaka ma ki Ammah duniya da lahira, a yau saboda Ammah Malam ya goranta ma ki, zaman shekaru ashirin da bakwai ba wasa ba, tare na ganku ban taɓa jin magana makamanciyar wannan ba, ki yafe mana".
"Nagode Mairo, kin biyani da komi. Duk wanda zai dau jininsa ya baka ai ya wuce komi. Allah shi cigaba da haɗa kawunanmu".
"Amin".
***
BAYAN AWANNI UKU
Motace ƙirar TESLA MODEL S ta ja wani wawan burki a harabar asibitin, ma tuƙin motar be gama saita parking ɗin motar ba,dattijo mamallakin zati da kamala ya fito cikin azama, yanayin shi kadai zai nuna yana cikin damuwa. Professor Usman Bakori kenan (Mahaifin Mukhtar).
"Daddy ka bi a hankali", muryar matashin da ya biyo Prof. Cikin sassarfa, kamanninshi sak! Da MK sai dai bambancin fata da yanayin jiki.
Ofishin Likita su ka nufa inda su ka masa cikakken bayani dangane da MK.
Har ɗakin da yake ciki suka shiga da Likita inda Umar ke zaune. Bayan gaisuwa da godiya da su ka masa, Daddy ya koma ofishin Likita.
"Dakta idan ba damuwa zan wuce da ɗana gida, ba wai dan na raina kulawarku a gareshi ba, a'a sam! Mahaifiyarsa ma Likita ce, tana da asibiti na ta na kanta".
"Ba komi Alhaji, Allah ya bashi lafiya".
Su kayi musabaha.
Da taimakon Umar aka shigar da MK mota, wanda be san mi ke faruwa ba, saboda allurar da aka yi ma sa.
Yaya Habib da Umar ne ke a gaba, yayin da Daddy ke a baya yana kula da MK.
Basu isa Katsina ba sai bayan sallar isha'i. Asibitin Momi (Al'umma Comprehensive Hospital) suka wuce. Ma'aikatan jinya (Nurses) dake on duty suka taimaka wajen ceto rayuwar MK.
Anyi masa duk abinda ya kamata.
Gida Daddy ya wuce dan sanar da Momi abin da ke faruwa.
Yana shiga gidan falo ya isketa sai safa da marwa take.
"Assalamu Alaikum ".
" Prof! Ina ku ka tafi? Hankalina duk a tashe. Miya faru? Hajja ce? Ko MK ne? Please talk to me ". Ta faɗa cikin sarƙewar murya.
" Calm down Dear, duk kin bi kin tada hankalinki. Nothing bad happens".
Ya kama kafaɗunta tare da zaunar da ita akan daya daga cikin kujerun alfarma dake kewaye da falon.
Ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, yana shafa kanta a hankali tamkar wasu sabbin amare.
"Now tell me what happens".
"Kinyi mun alƙawalin ba za ki tashi hankalinki ba?". "Eh".
"Kin gane ko, komi mukaddari ne daga Allah, mutum ba zai iya kaucewa kaddararsa ba. A hanyar dawowar MK daga Bakori ya samu haɗari, amma jikinsa da sauƙi yana asibitinki".
"What? My one and only MK got accident,it can't be possible".
"Haba Saudah yanzu ba za ki yarda da kaddarar ba?".
Ta fashe da kuka "Prof ka fadamun gaskiya, MK ya rasu koh?".
"Be rasu ba, idan za ki dauko duk abinda mara lafiya ke buƙata ki dauko. Ban san miyasa wani lokacin kike behaving kamar ƙaramar yarinya ba".
Ya faɗa cikin daga murya.
Tashi ta yi ta dauko duk abin da ta san za a buƙata ta fito, har ya fita daga falon, bakin mota ta iske shi.
Suna isa asibitin ta har matar Yaya Habib ta iso. Ta taso ta amshi kayan da ke hannun Momi,ta gaida su tare da yi masu "ya me jiki?".
Tare suka shiga ɗakin da aka kwantar da MK, yana kwance an saka masa iskar oxygen a hanci saboda matsalar shaƙa da fitar da iska da yake fama da ita. Kanshi da kafarsa ta dama nannaɗe da bandeji (bandage).
"Malam Umar mun gode kwarai da gaske, Allah shi saka da alheri".
"Ba komi yallaɓai ai taimakon juna ne".
"Ga wannan ka sha ruwa".
"A'a nagode ".
" karɓi nan, nima Babanka ne". Da haka ya karɓi kyautar kuɗin da Daddy ya masa, ya tafi.
Momi da ke zaune gefen gadon, hawaye ke ta ambaliya daga kuncinta, wani na korar wani.
A hankali ya fara motsa ƙafafunshi, bakinsa na motsi, a hankali ya furta "Ammah".
Daddy ya ɗaga hannayenshi sama ya ce "Alhamdulillahi!".
"Prof kana jin mi MK ke cewa?".
Bai ko kalle ta ba, ya matso jikin gadon yana tofa ma MK addu'a.
Momi tayi kwafa, tare da jinjina kai.
***
BAYAN WATA BIYUGIDANSU ASMA'U
Ta dubi kayan lefen da aka kawo ma ɗiyarta, akwatina ne guda goma sha biyu, na yayi. Kowanne danƙare da kayan kyale-kyale na mata.
" MashaaAllahu! Ade ɗiyarki ta yi goshi wadannan irin kaya haka?".
"Kai ai Naira ta sha kuka kam".
"Ina ma Sauluba ke da wannan kayan, Allah shi maidamu danshinku".
"Yarinya za ta yi aure gidan hutu".
"Wake son wahala".
"Ina dalili? Ka saida akuyarka ta dawo tana ci ma ka danga".
Ire-iren wadannan maganganunne ke fitowa daga bakunan matan da su ka zo ganin lefe.
Bayan kowa ya watse, Ade ta fito daga ɗakinta.
"Asma'u fito kiga irin kayan arziƙin da aka kawo ma ki, yarinya Kinyi goshi. Ai ni nasan kyawu da surar da ke gareki sai mai mota, keda auren talaka har abada".
Shiru ba ta ji Asma'u ta fito ba. Ta leƙa ɗakin Asma'u bata ciki.
"Asma'u! Asma'u!! Asma'u!!! ".
A sukwane ta fito waje ko mayafi ba ta tsaya dauka ba.
" Dan Allah ba ku ga fitowar Asma'u ba?".
"Ai kuwa yanzun nan na gan ta da akwati tana ja". Faɗin Isah mai tireda dake gab da gidansu.
Sauri take tamkar za ta tashi sama, hankalinta idan yayi dubu ya tashi.
Tafiya take tana magana ita kadai.
"Na shiga uku! Ban lalace ba, kar dai Asma'u guduwa tayi? Da na shiga tara, tana neman tona man asiri".
Kamar daga sama ta hango Asma'u za ta tsallaka titi.
Da ƙarfi tayi magana "Ku taimaka ku riƙe mun ita kar ta gudu".
Jin muryar mahaifiyarta, yasa ta saki akwatinta, ba tare da ta duba titi ba ta ruga da gudu.
Hakan yayi dai-dai da giftawar wata bus wadda tayi awon gaba da mutum, sai dai ji ka ke "ƙeeeeeeeeeeeerrrrrrrrrr".Kai na bisa wuya! I know this chapter is kinda boring, anyway I promise you sweet, sour and bitter chapters coming in to your ways. Lol 😁
Don't mind me, I mean sweet chapters.
Ok! Please vote, click on that orange star 🌟 and comments as much as you can.
#226 in MYSTERY/THRILLER#AuntySisTeam i do love 😍 you with all my heart ♥ Allah Hafiz.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...