MADUBI
©AYEESH CHUCHUBABI NA ASHIRIN DA SHIDA
"I believe in memories
They look so, so pretty when I sleep
Hey now, and when I wake up,
You look so pretty sleeping next to me
But there is not enough time,
And there is no, no song I could sing
And there is no combination of words I could say
But I will still tell you one thing
We're better together."
—Better Together by Jack JohnsonMAFARKI
A hankali ta duƙa ta dauki wayar da ta faɗi ƙasa ƙirar Samsung Galaxy s8.
Ba ta ko kalli mai wayar ba ta miƙa ma sa "we're so sorry please".
"Khalifa ka ga abinda ka janyo ko? Da wayar ta fashe ba da ka zanyi a tafi da kai ba ruwana".
Harɗe hannayensa yayi a ƙirji yana kallonta, ya gaza dauke idanunsa a kanta.
Ko a cikin MAFARKI, ko a farke ko da a cikin maye yake ba zai taɓa manta fuskar nan ba. Da ita ya ke kwana yake tashi.
"Maama toli (sorry) na daina".
"Sai kayi laifi ka dami mutane da toli".
"Bari in je in ce ma Ankul toli".
"Khalifa".
Ina har ya isa wajen da MK ke tsaye.
"Ankul toli kada ka bari Maama ta buge ni, ba za ta siya man iysh kiyim ba".
Nan ta ƙaraso wajensu.
Bugun zuciyarta ya ƙaru, tana jin kamar za ta faso allon ƙirjinta.
Bakinta na rawa, ta runtse idanunta ta sake budewa, a hankali ta furta "Ya MK?". Tare da nuna sa da hannunta.
Murmushin nan ya sakar ma ta, tana jin kamar ta narke a wajen a saka ta a freezer ko ta dunƙule ta dawo dai-dai.
Ta kasa koda motsi ne. Wasu irin abubuwa take jin suna sukarta tare da fizgarta.
Shekara shida ba wasa ba.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ". Ya ke ta maimaitawa a cikin zuciyarshi.
Yanzu ya ƙara tabbatar da cewa Ammah ta ma sa nisa. Yaron da ya gani mai kama da ita ya tabbatar da cewa ɗanta ne, sai dai idan ba sani kayi ba za ka yi zaton ƙaninta ne.
Ya daga Khalifa sama.
" Ya sunanka?".
"Khalifa sunana. Amma a School Ahmad Salis Ahmad ake kirana".
Sakato ta yi tana kallonsu. Idan akwai abinda ba ta so a tattare da Khalifa be wuce surutunsa ba cikin yamin baki.
"Nice name. Ina Daddynka?".
"Abbu? Ankul Deeq? Abba? Baban Ihsan?".
Murmushi ya yi.
Dan Khalifa ya kasa tantance mi ma ake nufi da mahaifi. Abu daya ya sani Ammah ce mahaifiyarsa. Ita ma saboda ya taso da irin yadda ake nuna ma sa.
Mahaifi kuwa duk wani namiji uba ya dauke sa, ba kamar Ya ARK da jininsu yafi zuwa ɗaya.
Idanu MK ya kafa ma ta, ya na neman amsoshin tambayoyinsa.
A hankali ta furta "Mun rabu da mahaifinsa".
Sai kuma hawaye suna neman tona asirin da ta binne a cikin zuciyarta.
Ganin zasu iya tara mutane a wajen ya sa, tayi saurin amsar Khalifa daga hannun sa, ta ja cart ɗin da ta yi siyayya ta wuce inda za ta biya kudi.
Ta biya aka juye ma ta a leda, suka fito.
Tsaye ta iske shi gaba kadan daga bakin ƙofa ya kafa ma ta idanunsa masu rikitarwa.
Kallonta yake ya kasa dauke idanunsa, yana jin duk duniya babu wanda ya kai Ammahrsa kyau.
Alamun ƴan matanci sun gama bayyana a jikinta. Kyawunta ya fito.
Fatarta ta ƙara murjewa ta yi haske, ba za'a kirata fara tas ba, hakanan ba ta a cikin rukunin baƙaƙe.
Sanye ta ke da doguwar rigar yadi mai taushi, multicoloured. Yasha adon fulawowi.
Dinkin ya matukar dacewa da jikinta,ta yafa mayafi a saman kanta kalar ruwan bula. Takalminta da jakarta kalarsu ɗaya.
Tana riƙe da hannun Khalifa har suka iso inda MK yake tsaye.
Malam Iliya ya ƙaraso wajen ta.
"Uwar ɗakina kawo ledar a sa a cikin motar".
"Ai da ka bar shi Baba mun ƙaraso".
"A'a ba komi".
Ya amsa.
Ta kasa jure irin kallon da MK ke yi ma ta, a hankali ta furta "Za mu tafi, kar Mami ta ga mun dade".
Murmushi ya yi..
Wayar da ke hannunta ya karɓa ya zuba lambarsa a ciki ya kira ta shi.
Ya miƙa ma ta.
"Zan kira ki".
Ta gyada kai.
Su ka shiga cikin mota har sai da su ka bace ma ganinsa tukunna ya tafi, siyayyar da be yi ba kenan.
***
Tunda ta dawo take kwance kan gado, da yake tana fashin sallah. Tarkacen Ya MK ne a kan chest drawer da ke gefen gadon.
Gabadaya ta sukurkuce. Ta kasa karatun da za ta yi. Ta na da jarabawa Washegari da safe, da yake sun fara NECO.
Laila ce ta shigo ita da Khalifa ta ajiye jakarta da gyalenta saman gado "Washhh! Yau na gaji wallahi. Mugun mutumin nan ya wahalar da mu".
Hankalin Ammah baya gareta ba ta ma ji shigowarta ba, hankalinta baya jikinta.
Ta dau jakarta ta ajiye a ma'adanar ajiye jakkunansu.
Bayi ta shiga ta tube kayanta ta saka a inda suke zuba kayan wanki.
Har ta fito wanka, ta tada sallah Ammah na nan inda ta barta.
Khalifa ya fita daga dakin, ta idar da sallarta. Ta haye gadon Ammah.
"Twinie! What happened?".
Ta dan girgiza kafar Ammah.
A lokacin ta dawo da hayyacinta.
Ta saki ajiyar zuciya.
"Yaushe ki ka dawo?".
Layla ta zaro ido.
"Ina za ki sani bayan kin zurfafa cikin tunani".
Murmushi ta yi.
"Yau na ga Ya MK".
Wani uban tsalle Layla tayi a saman gadon.
"Yeeeeeeeeeeeeyyyyy! Love in the air. Yau an ragargaza soyayya".
"Ke fa matsalata da ke kenan".
Nan ta labarta ma Layla yanda su ka hadu.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...