MADUBI
AYEESH CHUCHU“Cause, honey your soul could never grow old, it’s evergreen and, baby, your smile’s forever in my mind and memory” ~Ed Sheeran (Thinking Out Loud)
ƘARSHE
***
ABUJABAYAN SATI UKU
10:45pm
Kwance su ke, Ammah ta juya baya ta na gyara rufarta da bargo saboda sanyin da ake.
"Ammah!".
Ya faɗa can ƙasan maƙoshi.
"Na'am Roohiey".
"Matso ki ji".
Ba ta ce komi ta matsa kusa da shi, ya janyo filonta. Shi ya gyara ma ta zaman kanta a filon.
Ya sumbacin goshinta. Ta lumshe ido tare da jin faɗuwar gaba.
"Uyooniey ki na sona?".
Murmushi ta yi, ta saki ajiyar zuciya.
"Yes Roohiey, ina son ka, ban san yaushe na fara ba, amma na tsinci kaina a cikin so da ƙaunar ka. Roohiey did you also feel the same? "
" Yes Uyooniey! I love you so much that I can't even know how to express it. I felt like without you I'm nothing Uyooniey. You complete me. I don't like you anymore ".
Ga murmushi ga zaro idanu.
" Ehen! A da birge ni ki ke, amma a yanzu so da ƙaunar ki na ke".
"Meyasa yasa ka ke so na?".
"Well! Saboda ki na Son Allah".
"Ban gane ba?".
"Saboda kina kiyaye dokokin Allah, Son Allah ya sa ki ke taka tsantsan wajen bin umarninSa. Kyawawan dabi'un ki da kuma ilimin ki, yanayin huldarki da jama'a, yanda ki ke sadaukar da lokacin ki da rayuwar ki ga jama'a. Alkhairanki na da yawa Uyooniey. You're different".
"You're also different among them. I'll forever love you".
"Daga yau kinga wajen baccinki".
Ya nuna ma ta kirjinsa tare da rungume ta, su ka lula can wa ta duniyar amma ta masoya.***
Khalifa na can wajen Mami an bar ma ta shi. Ta ce shi na ta ne, su haifi wasu su rike.
Duk hutu yana zuwa Bakori ya yi sati ɗaya ya gana da mahaifinsa wanda har sun saba tun Khalifa na jin tsoronsa. Sun rabu da matarsa yaƙi ƙara aure yana ta gararamba a cikin gari ba sana'ar yi.* * *
"Mtseeeewn! Wannan ai sakarci ne, how comes ki ka cika yaji abincin nan, i told you i didn't like pepper".
"Yaa Allah! Roohiey ka yi hakuri ban san yana da yaji ba tarugun kadan na sa. Bari in sake ma wani".
Ta faɗa jikinta na rawa.
"Karfe nawa ki ka sani? Kullum kina abu be kamata a ce kin san measurement ɗin da za ki sa ba. Ku fa mata matsala gare ku,ku yi ta shirmen banza da wofi".
"Ka yi hakuri".
"Ban ce ki fita ko da nan da ƙofar waje ba ".
" Roohiey zan kai report ɗina MHS aikin da manager ya sa ni, sannan muna da meeting da states Co-ordinators fa yau ka sani".
"Na riga na faɗi kalamai na. Idan kin so ki fita".
Ya dau jakkarsa ya fita.
Hawaye ke ta bin fuskarta.
Ta zuba farfesun ta sha, ita sam harshenta ba ta ji yaji ba.
Hakan ya sa ta sake rushewa da kuka. Ta dawo kan kujera ta kwanta.
Tayi ta kuka har kanta ya fara ciwo. Zazzabi mai zafi ya rufe ta.
"Yanzu wannan abin har ya kai abinda Roohiey zai ta faɗa akai. Ko da yake be haɗa abinci da komi ba.
Yau ni ya hana zuwa wajen aiki, ya hana ni attending meeting ɗin da ns ci buri akan shi".
Ita kadai ke magana da zuciyarta.
Da kyar ta tashi ta dauko wayarta da laptop, ta tura ma Sa'a duk abinda za'a tattauna akai ta email dan ta wakilce ta.
Sannan ta tura ma ta SMS
"Ba zan samu zuwa meeting ba, I'm seriously sick. Kiyi handling komi, ki duba Email dinki na tura duk abinda ake buƙata".
Ta na ganin saƙon ya tafi ta kashe wayarta.
Aikin ofis ɗinsu da take service ma dama ta na da documents ta tura ma su report ɗin komi. Tana aiki ta na kuka.
"Men are always men".
Ta faɗa a fili.
Ko kashe laptop ɗin ba ta yi ba, zazzabi mai zafi ya rufe ta. Ko gani ba ta iya yi. Ta na ta kyarma ita kadai.***
Tunda ya shiga ofis ya kasa aikata komi, ko da suka shiga meeting haka ya fito sukuku.
Agogon hannunsa ya kalla yaga har sha biyu ta yi, ga yunwa yana ji.
Wayar shi ya daga ya kira ta ya ji wayar a kashe, ya gwada gudan Layin shi ma a kashe.
Ya dafe kansa cikin ruɗu.
"Kodai ta tafi wajen meeting ɗin ne? Ammah za ta iya komi amma banda wajen aikinta da NGO ɗinta. Ba ta wasa da duk al'amuran da su k shafe su".
Kada kafada ya yi. Ya yi ordering Aims Natural Drinks da Bugger, ya ci. Dan ya daina cin abincin waje.
Ya so zuwa wajen da ake meeting din, jin haushin Ammah ya hana shi zuwa. Shi ma ya kashe wayarshi dan kada a kira shi ma.Be dawo gida ba sai karfe shida.
Ya yi sallama ya shige dakinsa.
Babu ita a falon ƙasa. Wanka ya yi, ya fita zuwa masallaci.
Be shigo ba sai wajen karfe tara.
Dinner table ya wuce, mamaki ƙarara a fuskarshi, tun kayan abincin safe ba'a kauda su ba. Su na nan yanda ya bar su.
Laptop ɗinta ya gani ta na haske a kunne a ƙasa kafet da wayoyinta a ajiye.
Wayar shi ce ta yi ƙara, lambar Aunty Ayeesha ya gani.
"Ya ARK ya jikin Ammah? Kar dai ya yi zafi har haka? Tun dazu nake neman wayoyinta a kashe. Sa'a ma ta zo ta ce ta so ta duba jikin Ammah ba su taso meeting da wuri ba.
Kaima kuma ba ka je ba meeting din ba, wayarka kashe ".
Zufa ta keto ma sa.
" Zazzabi ne, amma ta sha magani ta ji sauki".
"Ku je asibiti dai a duba a ga me ke damunta".
"Okay toh".
Jikinshi duk ya yi sanyi ya haye sama, ɗakinta ya shiga kwance ya iske ta ta lullube da bargo tana rawar sanyi.
A sukwane ya isa bakin gadon ya taɓa jikinta ya ji shi rau."Ni ne koh Uyooniey Please forgive me. Ba da son raina haka ta faru ba".
Kuka ya kwace ma ta.
Ya rungumeta tsam yanda ba ma saka tsinke. Zafin jikinta na ratsa shi.
"Ba zan ƙara ba kin ji Uyooniey. Kin ci abinci? Kin sha magani?".
Ta shi yayi ya shiga bayi ya zubo ruwa a roba da towel ya tsoma yana shafa ma ta a jiki.
Ya sauka ya hado ma ta tea mai kauri, yana ba ta a hankali, da yake tana jin yunwa tsab ta shanye shi, ya kwantar da kanta saman cinyarsa ya na shafa kanta.
"Kin yafe min?".
Murmushi ta yi na karfin hali.
Ya sumbace ta.
Amai ne ya taso ma ta ta ruga da gudu bayi ya biyo bayanta. Ya riƙe ta tana aman har ta gama ya gyara ma ta jikinta su ka fito.Alhamdulillah!
Anan zan dasa aya sai Allah mai kowa mai komi ya nufe da sake haduwa a wani labarin.QUESTIONS
One word for Ammah
One word for Ya ARK
One word for Ya MK
One word for Laila
One word for Salisu
One word for the entire story.
What are the lesson learned?
What are the mistake written?
Suggestions for improvements?
Advice!
What kept you reading this story?
How did you enjoy this journey?
If you were ask to rate this story from 1-10, what will be your rate? Be sincere
What is your favorite chapter?
Did you like the continuation of MADUBI as in epilogue? I've many things running in my mind (after sallah)
Be sincere in answering your questions.
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
+2348068069242
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...