MADUBI
©AYEESH CHUCHUBABI NA SHIDA
***
"Halimatu Ibrahim Liman ita ta zo ta ɗaya a cikin 'yan hizib arba' in, ta fito ta amshi kyautarta daga hannun mai girma ciyaman (chairman) Alhaji Habibu Umar".
Aka hau kabbara,ta fito ta amshi kyautarta.
Hakoranta buɗe har su ka isa gida ita da kannenta da Sa'a su na take ma ta baya.
"Gwaggo Yaya Ammah ce ta zo ta ðaya, har da ita za a Katsina za ta wakilci Bakori". Faɗin Mubarak
"Kai Madallah da wannan ɗaddaɗan labarin".
Inna da ke jin kamar ta rungume ɗiyarta gudun a ce tayi abin kunya ya sa ta kawar da kai, fuskarta kadai za ta nuna annurin da take fitarwa.
Nan su ka taru su na taya Ammah murna.
"Mairo kira mun Ammah".
"Toh Innani ba ta ma san kin zo ba".
***
"Halimatu kin girma, wa zai kalle ki ya ce ba ki kai sha huɗu ba".
"Kai Innani, dan ba ki ga Sa'a ba ne, ta fi ni gwabin jiki ma".
"Ai kuwa da a ce Karofi ki ke da yanzu ki na ɗakin mijinki duk sa'oinki ai wasu har da ya'ya".
"Chab! Duka-duka shekara ta nawa? Sha biyu kacal fa".
"Toh ni ina da shekara goma akai mun aure, kuma ba abinda ya same ni".
"Ai da daban Innani, yanzu da ina boko da fa yanzu ina makaranta".
"Ke ni kyale ni da wata boko can, masu yinta ma ba kaunar su nike ba, wannan boko ba abinda take sa mutane sai shaidanci, shiyasa kaf! Zuri'ata babu ɗiya macen da za ta yi boko, ta kara janyo man abin kunya".
"Wane abin kun....".
Kukan da Innani ta barke da shi ne ya dakatar da Ammah.
"Innani mi aka yi ki ke kuka?".
"Ba komi je ki kira mun mahaifinki"."Ammah wannan kakkarwa da jikinki ke yi na lafiya ne?".
"Gwaggo, Innani ce ke kuka, zan je in kira Baba".
"Toh yi maza ki hanzarta".***
KATSINA
"Mukhtar na kagara ka gama IT ɗin nan ka dawo gida, the house is empty without you". Faɗin Momi (Dakta Saudah mahaifiyar Mukhtar)
"Momi ji na ke kamar kar in bar Bakori, akwai ɗadin zama Hajja na kula da ni sosai kamar baby".
"Dan gatan Hajja. Shiyasa tun farko na so ka yi IT ɗinka a asibiti na".
"Gara dai ya je can inda be saba ba, that's part of learning. Kuma zai fi sanin matsalolin mutane". Faɗin Prof. Usman (mahaifin Mukhtar).
"Farfesa (professor) ai Shikenan tunda kun haɗe mun kai. Anyway field ɗina MK yake ba zan ji haushi ba".
Dariya suka yi dukkansu
"Faɗa mun in ji ni da ke da yara biyu duk a fanni education, and nan gaba kadan za ki ji ana kiran Dakta Habib da Professor, daga nan sai Sadiq. Ku kam daga Daktan nan ba ku kau ba".
"Dadi ka daina ban so".
"MK my boy na daina, yanzu dai wuce mu tafi ban so mu yi tafiyar dare, idan son samu ne in je yau in dawo".
"Dadi gara ka kwana Hajja za ta ji daɗi ai ka rabu da kwana".
"Toh hakan za a yi".
Gabadaya su ka fito daga gidan, bayan Mukhtar ya saka masu kaya a bayan boot ɗin motar.
Momi ta bi su da addu'a
***
BAKORI
Tafiyar awanni biyu ya kawo su garin Bakori daga Katsina.
Hajja na ta hiɗimar saukar ɗanta da surukarta.
"Na ji dadin ganinku, ai kun kyauta da ku ka zo tare".
"Hajja duka yaushe mu ka zo, nayi-nayi ki dawo wajena da zama kin ki, Yaya Umar ma yayi na shi kokarin duk kin ki".
"Usmanu idan ka ga na bar gidan nan gawata aka fitar kamar yadda aka fitar da ta mahaifinku, na fi kaunar in mutu a gidan aurena".
Sai kuma ta rushe da kuka.
"Ki yi hakuri Hajja in Allah ya yarda ba'a kara tada maganar".
"Allah albarkaci zuri'arka Usmanu".
"Amin Hajja".
"Ya maganar auren Sadiqu?".
"Ta na nan da ya dawo za a yi, yarinyar ma wannan watan take kammala bautar ƙasarta (National Youth Service Corp NYSC) ".
" Da kyau ai haka ake so, ina son ganin mata na karatu abin na burge ni".
"Hajjata ke ma ai sai ki koma makarantar".
"Ka ga Muntari ka kiyayeni, sai dai ka sa budurwarka Ammah".
"Kai Hajja wace irin budurwa, ni fa kanwa ta ce, kuma ma ki daina kirana Muntari salon ki ja mun raini wajen abokai na".
"Ashe har budurwa ka yi MK?".
"Dadi ba budurwata ba ce, kanwa na dauketa, ita ma Hajja ta sani".
Nan ya ke Daddy labarin Ammah.
"Lallai zan so iyayenta su ba ta damar yin karatu irin waɗannan yaran baiwa garesu, amma saboda son zuciya da wani dalili mara tushe na iyaye su hana ya'yansu mata neman ilimi".
"Sosai fa Dady, yarinyar na da talent, yanzu haka ita za ta wakilci Bakori a gasar Al Qur'ani ta jaha".
"Ba komi gobe kafin in tafi sai mu je gidansu yarinyar, in ji ta bakin mahaifinta kila ya yarje ma ta".
"Thank you Dad".
"Halinka na taimako Mukhtar ya biyo Usmanu".
Murmushi yayi irin na dattijan kwarai.
***
GIDANSU ASMA'U
"Asma'u maza amshi wannan maganin ki shanye ki shafe jiki da fuskarki, maganin farinjini da kwarjini ne na amso ma ki yanzu, wannan kuma turare jiki za ki yi da shi na tsarin jiki ne".
Ta yi galala da baki tana kallon mahaifiyarta, tabbas biri yai kama da mutum.
"Umma dama akwai maganin tsarin jiki da na sa farinjini banda wanda annabin rahma ya koyar da mu?".
"Ke ban son iskancin banza, kiyi abinda na sa ki".
"Kiyi hakuri Umma amma ba zan iya ba, tsarin jiki babu abin da yafi yin azkar na safe da maraice, farinjini kuwa duk wanda ya kyautata tsakanin shi da mahaliccinsa, ya aikata kyawawan ayyuka ya gama samun farinjini".
Wani irin haske ta ji ya gifta a tsakanin idanunta sakamakon marin da mahaifiyarta ta kai ma ta.
"Har zan haifi ɗiyar da za ta yi jayayya da ni, bari ki ji ko Gyatuminki be isa ba, bare ke".
"Ki gafarce ni Umma, Allah ya gani shi ne shaidata ba zan saɓe shi ba dan in faranta ma ki, addu'ar da nike yi kadai ta wadatar".
"Ooh dan kin ga ina lallaɓa ki, Toh wallahi ba ki isa ba, aurenki da Imrana ba fashi sai dai idan an kai gawarki gidan ki faɗi kass ki mutu, burina ya cika".
Cikin kuka ta ruga da gudu zuwa ɗakinta.
Muryar mahaifinta ya sa ta saurin fitowa,gaban shi ta zuɓe tana kuka.
"Abba ka taimake ni ka tsayar da Umma kar ta aikata abinda take son aiwatarwa, ban kaunar Imrana ni Mukhtar ni ke so ka taimaka mun Abba ku bani zaɓina".
"Kiyi hakuri Asma'u ki bi umarnin Ummanki, ki cigaba da addu'a. Ta riga ta kafe akan Imrana bani da ta cewa, tunda yaron nan Mukhtar be nuna yana sonki ba ki hakura ki bi zaɓinta, ba za ki taɓa taɓewa ba".
"Shikenan Abba zanyi abin da ka ce, ko da hakan zayyi sanadin rayuwata".
"In Allah ya yarda ba abinda zai faru".***
GIDANSU AMMAH
"Innani don Allah ki bar kukan nan haka, ba ki san cewa zubar da hawayen iyaye akan ya'yansu ukuba ba ne?".
"Shikenan Iro, duk inda take Allah ya cigaba da kare ta. Shiyasa na tsani bokon nan,ina amfanin mace ta yi ta yawo ta na cakuɗa da maza. Ba abinda yafi mace ta zauna a gida ta kyautata ma mijinta".
"Sosai ma Inna, Shiyasa duk nacin Halima da Ammah akan karatun boko naki yarda sanin irin tsanar da kika yi masa".
"Yauwa dama so nike mu yi wata magana, dalilin zuwa na kenan".
"Toh Innani ina jin ki".
"Iro yanzu haka za ka bar Halimatu a gida? Tana goga kafaɗa da iyayenta mata wadanda gab! Ta ke ta isko su tsawo, kamar Ammah zankaɗeɗiyar budurwa ai ya isa a ce tana gidan mijinta".
"Miji kuma Innani? Kamar Ammar? Duk tsararrakinta fa ba wanda aka yi ma aure, ai tayi kankanta da aure yanzu, na fi so ta maida hankalinta akan karatun islamiyya da take. Yanzu haka fa ita za ta wakilci karamar hukumar nan".
"Ai Shikenan so ka ke har in mutu banga tattaɓa kunnena ba?".
Sai ta rushe kuka har da shashshekaHehehe.. This is just the beginning
Shower shower shower me with your votes and comments.
chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...