"Ammah's gift 🎁 box from MK".
MADUBI
©AYEESH CHUCHUBABI NA TAKWAS
A hankali ya ƙaraso gabanta, ya ciro handkerchief daga cikin aljihunsa ya miƙa ma ta.
"Share hawayenki kin ji Ammah ta,ko so ki ke kiyi muni? ".
Ta girgiza kai, ta share hawayenta.
" Ko ke fa, har kin kara kyau".
Murmushi ta yi, "Bayan ka fi ni kyau Ya MK, kamar Balarabe fa".
Haƙoranshi farare tas! Suka bayyana, ya naɗe hannayenshi a ƙirji, tare da jinjina jikin bango yana kallon Ammah.
"Ko a Islamiyya haka ake cewa, bakin Sa'a da wasu 'yan ajinmu na fara ji".
"Ki ka ji me?"
"Wai ga wani mai kama da Balarabe, kuma shi ne Ameer ɗin Islamiyya. Kasan Sa'a ita ce kunnen gari, duk abin da ke faruwa za ka ji a bakinta. Wai Asma'u ma sonka take, da ban yarda ba sai daga baya idan mun haɗu islamiyya tayi ta zagina ko ta harare ni".
Fuskarshi ta yalwatu da fara'a. Yana jin ɗadin kowane furuci na Ammah, har baya son ta tsinke da magana.
"Don mi za ta harare ki?".
"Dan kawai kana zuwan gidanmu, tayi zaton kai saurayina ne, shi ne Sa'a tace wai kishi take da ni. Ni kuma nace wane irin kishi kamar wasu kishiyoyi, ko Gwaggo da Inna banga suna haka ba".
Be san sa'ar da ya kyalkyace da dariya ba.
"Ammah!".
Ta dago da fararen idanunta ta duɓe shi "You look so cute,ina son waɗannan idanun naki, they drives me crazy".
"Idanuna kuma?". Shi kadai ta fahimta a cikin bayaninshi.
Sumar kanshi ya shafa, tare da sakin ajiyar zuciya, ya basar da zancen.
"Zuwa nayi muyi bankwana na koma Katsina, ba zan iya zama Bakori ba. Idan ina ganinki Halimatu ba zan iya jurewa ba. Kin zama wata bangare ta rayuwata, Innani tayi katanga a tsakaninmu, ba zan iya taimakawa wajen ganin cikar burinki ba. Kiyi haƙuri, ki dauka hakan wata ƙaddararmu ce, Allah yayi inzo Bakori mu haɗu, in shigo rayuwarki, amma abubuwan da zasu faru Allah ya bar ma KanSa sani, Shi mai juya al'amura ne yadda ya so, Allah be yi mu zama cikin inuwa guda ba. Ki cigaba da haƙuri Ammah, na san ƙaddara bata yi mana adalci ba".
Idanusa suka kaɗa suka yi jajir! Ji yake kamar ƙasa ta cika masa idanu.
"Ya MK kar ka tafi barni dan Allah, idan ka tafi babu mai sake koya mun karatu, kuma Innani aure ta ce Baba ya mun".
Sautin kukanta ya ƙaru,har da shashsheƙa.
"Ammah ki bar kukan nan haka, ko so kike nima ina fara?".
Ta girgiza kai.
"Yauwa my Halimatu". Hannu yasa cikin aljihunsa ya fiddo da wata 'yar batta, "Rufe idanunki". Ba musu ta rufe idanunta.
Zuciyarshi na bugawa da karfe, kamar za ta ɓalla allon ƙirjinsa, ya kamo yatsun hannunta na dama, ya buɗe battar ya fiddo da zobe (simple and unique) ɗan ƙarami yana ta kyalli, ya saka ma ta a yatsanta mai kusantar ƙarami, zoben yayi alama faɗowa, ya maida ma ta shi a yatsanta na tsakiya. Sannan ya ce "buɗe idanunki".
A hankali ta buɗe idanunta tana kallon zoben da ke maƙale a yatsanta. Hannu ta sa ta shafa yatsan da ke haske da kyalkyali.
"Ya MK kar Gwaggo ta mun faɗa idan ta gani".
"Ki ce ma ta ni na ba ki".
Ledar da ke ƙasa ya dauko ya miƙa ma ta,ya fiddo wani gift 🎁 box mai kalar ja (red) "Amshi wannan ki ajiye,kar ki bari kowa ya gani, ki ɓoye shi da kyau Ammah. Bance ki buɗe shi yanzu ba,har sai ranar da ki ka tabbatar da kin iya karatu da rubutu, ban son ki tambaye komi, ki mun alƙawali hakan, kin ji Ammah?".
"Toh Ya MK, na maka alƙawali, zan je in ɓoye shi ƙarƙashin gadon Gwaggo, inda babu mai gani".
" Good girl! Kar ki yarda ki cire zoben da ke hannunki". Ya miƙa ma ta gift box da Ledar da ke cike da kayan kwalam da maƙulashe.
Ya juyar da kan shi gefe, yasa hannu ya goge kwallar da ke gangarowa.
"Saduwar alheri Ammah".
Ya juya cikin sauri, ba tare da ya kalli inda take ba.
A sukwane ya ja motarshi wadda tayi sanadiyyar tashin ƙura sama tamkar guguwa ta taso.
Tafiyar da take za ta tabbatar da cewa jikinta a sake yake,yayi sanyi. Da kyar take jan ƙafafunta, takalmanta na fidda sauti "Shararaf-shararaf".
Ganin su Gwaggo a tsakar gidan yasa ta ruga da gudu ta shige ɗakin, gift box ɗin da Ya MK ya bata ta fiddo cikin hijabi, ta tura cikin fantimotin Gwaggo. Ta kalli zoben da ke hannunta, ba ta yi aune ba ta ji kuka ya taho ma ta.
Ta kwanta saman gadonta da ke ɗakin Gwaggo, ta cigaba da kukanta.
Hankalin Gwaggo sam ya gaza kwanciya, "Mairo bari in je in dubo halin da Ammah ke ciki".
"Toh Gwaggo", ta faɗa muryarta na rawa.
Tagumi tayi tana tunanin wane irin yanayi rayuwar ɗiyarta za ta faɗa, dan kar a ce ba ta da ta ido da ko sama da ƙasa zasu haɗe ba za ta yarda da auren da ake son laƙaba ma ɗiyarta ba. Ko ada can da ke take hanƙilon Ammah ta isa aure, tana yi ne dan ta tsokani Gwaggo, yau ga shi magana na neman tabbata.
Anya kuwa ba ita ta yi ma ɗiyarta baki ba? Anya Ammah za ta yafe ma ta kuwa? Abubuwan da take ta ayyanawa a cikin zuciyarta kenan.
Kamar wani abu ya ja ta, tayi saurin tashi ta nufi ƙofar ɗakin Gwaggo. Ba ta kai ga shiga ba, ta jiyo muryar Ammah da ke a shaƙe alamar ta ci kuka ta ƙoshi, "Gwaggo ki ce ma Ya MK ya dawo, ke da shi kadai ke son ganin burina, Gwaggo yanzu ya tafi kenan? Ba zan ƙara ganinshi ba? Ƙila ma har in mutu koh? Yanzu da gaske aure za a mun? Mafarkina ya datse". Ta sake fashewa da kuka.
Da sauri Inna ta juya ta koma ɗakinta, hawaye take zubarwa na tausayin ɗiyarta.
A yau ne ta ji wani connection dake tsakanin Uwa da Ɗa.
"Ammah duk tsananin yana tare da sauƙi, ki dau hakan tamkar a mafarki ya faru, ki tashi ki cigaba da rayuwarki. Ba zan iya jure ganinki cikin wannan yanayin ba, zan yi duk wani ƙoƙarina inga cewa ba a yi wannan auren ba. Kema kina da gatanki.
Share hawayenki, Kinga har zazzabi na neman kama ki, bari in je in dawo".
Gwaggo ta sa kai ta fita daga ɗakin.
***
Gudun da yake shararawa da motar ya wuce tunanin duk wani mai hankali. Tuƙin yake yana hawaye, wani sa'in be ma ganin abin da ke gabansa.
Ƙatuwar motar trailer da ke gabanshi ya dumfara ba tare da ya san inda motar ta nufa ba, jin ƙarar motar shi ta gogi wani abu, yasa yayi saurin taka burki, amma ina.. Fizgarshi motar ta yi, ta bugi gaban trailer sannan ta wulwular da shi gefen titi inda ya bugi wata bishiyar kanya.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un" shi ne kadai abinda yake furtawa.
Ya kai kusan mintuna ashirin yashe a bakin bishiyar, a yayin da motar ta yi gefe guda.
Wannan trailer sun ƙara gaba, ba tare da sun tsaya ba. Da yake titin beda yawaitar ababen hawa ba, sai tsirarun motoci da babura da ke wucewa a wasu lokuttan.
A yau ma titin ƙamas.
"Subhanallahi! Kamar haɗari ne nike hangowa? ". Faɗin direban motar KSTA (Katsina State Transport Authority).
Hakan yasa fasinjojin da ke cikin motar buɗe gilasan motar.
Direban ya gangara gefen titi tare da kashe motar.
Al'ummar cikin motar su ka fito cikin sauri suka tunkari wajen da aka yi haðarin.
Cikin gaggawa su ka tallaɓo kansa, "yana numfashi". Wani daga cikinsu ya furta.
Nan suka hau binciken jikinshi ko Allah zai sa a samu wani bayani tattare da shi. Daya daga cikin fasinjojin ya nufi motar da ke jirkice inda ya ci karo da wayoyin dake zube ƙasa tare da wallet. Anan ya buɗe ya ci karo da passport, and tare da National ID card, Student ID card na jami'ar Ummaru Musa Yar'adua(UMYUK), voters card duk suna dauke da sunan MUKHTAR USMAN.
Cikin hanzari ya ƙaraso wajensu "Sunanshi Mukhtar Usman,mazaunin Katsina, ɗalibi a jami'ar UMYUK".
Wani saurayi da ke cikin tawagar ya amshi ID cards ɗin, "Na gane shi ɗan gidan Professor Usman ne,Sabuwar unguwa su ke zaune".
"Ok! Yaron Dakta Sauda ne, mai AL'UMMA COMPREHENSIVE HOSPITAL".
Duk iya kokarin su na buɗe wayoyin sun kasa, suna tsaye mota za ta wuce zuwa Bakori suka tsaidata, direban ya nemi alfarmar a wuce da Mukhtar asibiti mafi kusa. Ɗan matashin da aka kira da "Umar", ya bi motar da ta dau Mukhtar shi da wani bawan Allah.
***
"Malam ina magana nike son mu yi ta fahimtar juna".
"Ina jin ki Halima, uwa ga Halimatu".
Murmusawa ta yi da Be wuce fatar baki ba, "dama kan maganar Ammah ce".
"Toh, toh, Toh ina jin ki ".
" Malam ka yi ma Allah, ka dubi yarinyar nan da idon rahama ka janye batun aurenta. Idan aka ce ayi ma Ammah aure a wannan zamanin ba ƙaramin tauye ma ta hakkinta aka yi ba, haƙƙoƙi nawa aka danne ma ta, sai yanzu kuma a ce za a kuma haba? Laifin wani na shafar na wani ne? Yarinyar nan an hanata neman ilimin boko wanda da shi ake ci a zamanin nan, sannan kuma rana guda a ce za a ma ta aure dan dai kawai anƙi gaskiya".
"Dakata! Dakata! Halima, ina jin dai Ammah bake kika haifeta ba, baki da ikon a kanta, saboda wani banzan dalilinki ba zai sa in kasa bin umarnin mahaifiyata ba. Auren Ammah ba fashi, ɗiyata ce ba taki ba, ki bari sai ranar da kika ajiye naki kwan a duniya sai ki nuna man isa".
"Ni ka ke ma gorin haihuwa yau?".
"Ammah bata da uwar da ta wuce Gwaggo, ita ta sha fitsari da kashinta, haihuwar Ammah kadai nayi amma ban san wahalarta ba. Idan ba dan halacci irin na Gwaggo ba da Ammah bata kai yanzu ba, idan ta hadu da muguwar kishiyar uwa. Na ba Gwaggo Ammah halak malak, koda bayan raina ne, Ammah ɗiyar Gwaggo ce".
Hawaye suka zubo daga kwarmin idanunta.Huh! How did you feel about this chapter?
Show me some love 😍 by voting and commenting. U know I love you mush, yes! So so mush..
How is you? Mama, papa, yara, nd ebiribodi? Hope Kowa fine?.
Ehemmm I'm just passing by.
See you tomorrow In Shaa Allahu, i promise U another chapter, just pray for my well-being.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...