TSUGUNNO BA TA ƘARE BA

1.8K 167 21
                                    

MADUBI
     ©AYEESH CHUCHU
BABI NA SHA SHIDA

I dedicated this chapter to all CHEMIST (Chemistry recreate nature)

TSUGUNNO BA TA ƘARE BA

   "A'a Yallabai kai ne da kanka, yanzu fa muka rabu".
"Eh amanar Allah na kawo ma ka". Faɗin Hameed.
Ido biyu ya yi da Ammah da ke tsaye jikinta na kyarma dan tsoron Salisu take sosai.
  "Ku shigo daga ciki".
Ayeesha da ke ta galla ma sa harara tana jin kamar ta shaƙesa kowa ya huta.
  Su ka zauna, falon yayi tsit.
"Salisu ashe kallon da nake maka ba haka bane ba. Ina maka kallon mutumin kirki, wanda idan aka damƙa ma amana zai riƙe tsakaninsa da Allah amma sai na same ka da cin amanar da Allah ya dora ma. Na ji duk abin da ke faruwa tsakaninka da matarka, ka kuma kyauta".
"Ba dan ka ci albarkacin matarka ba wallahi kotu za ta raba aurenku. Kuma ka yi zaman gidan yari na cin mutuncin yarinya ƙarama da ka yi ba tare da ka duba halin da take ciki ba".
"Hajiya a yi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba. Sharrin shaidan ne wallahi".
"Dama ai da shi ku ke fakewa ana cutar ƴaƴan al'umma".
  "Yanzu dai kashedi zan ma ka ko da wai kada in kara jin ka muzguna ma yarinyar nan, idan ba haka ba a bakin aikinka".
"In Allah ya so ya yarda ba zan kuma ba Yallabai na tuba".
  Ammah tunda aka soma magana take hawaye.
  Ayeesha ta dafa kafaɗarta "Ammah ki cigaba da haƙuri watarana sai labari. Ki ma mijinki biyayya".
" In Shaa Allahu aunty".
"Sannan kai kuma Salisu likita ya sa doka, ba ka kara kusantarta har sai nan da watannin uku".
Ya gyada kai "Nagode kwarai". Ya fada jiki na kyarma.
Da haka suka tashi suka tafi.
   
                       ***
BAYAN WATA BIYU

Tun daga ranar da aka yi ma Salisu kashedi kan Ammah ya fita harkarta, be ma ta magana sai dai in abinci zai ci, duk wani abu da za ta buƙata na gida sai da ya ajiye.
  Ammah ta cigaba da sana'arta ta saida kayayyakin amfani a cikin gida, wanda Ayeesha ta ƙara ma ta jari.
Da yake ba cuta a cikin zuciyarta, tana samun nasara a cikin sana'ar dan mutane sun fara gane ma ta.
   Yau kwana uku da tafiyar Salisu Lagos, ya bar ma ta duk abin da za ta buƙata. Zaman gidan ya isheta, hijabinta ta dauko ta sa, ta rufe gidan.
Gidan sirikarta (mahaifiyar Salisu) ta nufa.
  "Inna ina wuni?".
"Lafiya lau Halima. Ya gidan in ji dai ba wata matsala?".
"A'a babu Inna".
"Toh barka. Shiru dai ba wani motsi ɗiyar nan inga jikana. Watanku bakwai fa kenan da aure, ina son ganin jinin Salisu kafin in koma ga mahallicina. Na san kina haƙuri ki cigaba da yi kin ji Halima".
"In Shaa Allahu Inna".
"Allah yayi maku albarka".
"Amin. Ba wani aiki da za a yi ma ki Inna?".
"A'a, Uwani ma kafin ta tafi makaranta sai da tayi komi".
"Toh Inna ga wannan asa mana albarka".
"Kai har da dawainiya Halima. Nagode kin ji. Allah shi kara buɗi".
"Amin Inna, ni zan koma dama zuwa na yi in gaida ki".
"Toh Nagode kwarai".
   Da haka Ammah ta tashi ta tafi.
Har za ta shiga gida, ta ga dacewar ta shiga gidan Ayeesha.
  Ta kwankwasa kofa mai gadi ya buɗe ma ta, suka gaisa ta wuce ciki.
Da sallama ta shiga, sai da ta tabbatar an amsa ma ta sannan ta shiga falon da ƙamshi mai sanyin ɗadi ya bugi hancinta.
Ta lumshe idanunta,ta ƙara shaƙar ƙamshin.
Ta yi ma kanta mazauni a ɗaya daga cikin kujerun falon.
  "Ammah fushi nake dake, ai na yi tunanin kin yanke zumunci ne".
"Wace ni Aunty, ai na san hukuncin mai yanke zumunci. Na ga ne dai kada in takura ma ki".
"Lallai yarinya, ashe dama baki dauke ni yayar ba?".
" Ke ce babbar yaya ma".
"To tashi mu shiga kicin ki tayani aiki".
"Yauwa dama ina son in koyi girki na yan gayu".
"Kina yi ma Salisu ko?". Ta ɗaga gira sama.
"ka ji Aunty, ni dai in koya kawai".
"To shi kenan, kin kuwa zo gidan girki. Kin ga shi na karanta a jami'a digiri dina na farko a jami'ar Oxford da ke London. Na karanta Food & Nutrition. Inda yanzu nake masters dina wato digiri na biyu a Jami'ar Bayero Kano ina karantar Catering, shi ya kun shi girke-girkene zalla".
"Lallai Aunty ashe har Kasar wajen kin yi karatu?".
"Eh can muka taso har yanzu ƴan uwana kaf suna can, amma sun kusa dawowa Najeriya gaba daya. Aure ya maido ni nan, mu yan Kano ne,dangin Abbanmu duk suna Kano, Hameed dan abokin Abbana ne. Mamita kuma yar Katsina ce, amma ban san ina a Katsina ba".
  "Wai Allah! Shiyasa Hausarki ta yan gayu ce".
Ta yi dariya" Dan baki ga yayye na ba ne. Bari in nuna ma ki hotunanmu ki gani. Amma mu tafi kicin hotunan na cikin waccan wayar".
  Suka shiga kicin Ayeesha ta miƙo ma Ammah wayarta ƙirar Google Pixel XL, ta buda ma ta inda hotunan suke da yanda za ta kalla.
"Aunty wannan ƙatuwar wayar haka".
" Ammah kenan, ni ma ba komi nake da ita ba sai daukar hotuna da video. Da yake ina da channel a YouTube wata kafar sadarwa ce da ake daura hotuna masu motsi (video) wanda duk duniya za ta gani ".
" Duniya ta cigaba. Muna ƙauye ba mu san komi ba".
"Wata rana kema za a dama da ke Ammah".
Nan Ammah ta cigaba da kallon hotunan wayar. Ayeesha na fada ma ta wadanda ke ciki.
  Gabanta ya faɗi a sakamakon hoton matar da ta gani, wadda ke yanayi da Innani.
"Aunty kalla wannan hoton".
"Mami kenan ai Ammah".
"Suna yanayi da Innani, kakata da ta haifi Babana".
"Ikon Allah, bari in kira Mami in ce naga mai kama da ita. Ko da yake kema ai nace ma ki kuna yanayi da Laila".
Nan ta cigaba da kallon hotuna tana kallon yanda Ayeesha ke haɗa festive spaghetti.
  Sai da ta kammala komi ta kai kan dinning table, Ammah ta taimaka ma ta wajen wanke kwanonin da ta ɓata da goge kicin din. Sai da ta tabbatar da cewa kicin ɗin yayi ma ta tsab-tsab.
   Wanka ta wuce ta faɗa, yayin da Ammah ke wasa da Ajwad da ya tashi bacci, kayan wasa zagaye da shi.
  Can Ayeesha ta fito sanye da doguwar English gown mara hannu (armless) mai adon fulawa a jiki da jacket mai dogon hannu da ta matseta samfurin Tommy Hilfiger, tayi headwrap da  dankwalin kalar ja da ya bada ma'ana. Jambaki kadai ta shafa sai tozali (eyeliner) da mascara da suka kara ƙawata kyawun fuskarta.
  Flat shoes na DC ta saka ma ƙafarta kalar ja (red) shi ma.
Sai ƙamshin ma bambamtan turaruka ke fitowa daga jikinta.
   Ammah ta daga kai tana kallon yanda tayi matuƙar yin kyau.
"Wallahi kin yi kyau sosai Aunty".
"Nagode Ammah. Mu je mu ci abinci".
  Ammah tabi bayanta, ta matuƙar birgeta tana jin ina ma ita ce.
  Ayeesha ta buɗe food warmer ƙamshin da tururin abincin ya bugi hancin Ammah, a take ta ji cikinta ya hautsina.
Ta daure ta zauna,ta zuba dai-dai yanda ta san za ta cinye. Tana kai cokali a baki ta tauna abincin, ta ji zuciyarta ta tashi. Kafin ta ce mi amai ya taso ma ta.

                 ***
BIRNIN BONN

Sanye yake da material na maza kalar navyblue, an yi masa ɗinkin boda. Sumar kanshi da ke ta kyalli ta sha gyara tayi kwance luff! Abin ka da farin mutum sai ya haska yayi sharr!.
Tsintsiyar hannunsa daure da agogo samfurin Mykita, ya sha bakin tabarau na Persol, takalmin sandals ne sanye a kafarsa.
"Ya MK you look more than handsome. I'm jealous".
Murmushi yayi wanda ya bayyana fararen haƙoranshi.
"Kin faye rigima Yusie. Thank you ".
" Ba wani rigima kawai yan mata su yi ta kallonka. Allah yau tare za mu yi lectures din. Ina gani rannan wannan banzar Lauren ɗin ta ba ka wani abu a bag ai".
"Toh aku uwar magana, za ki tafi ku surutu zaki tsaya yi".
"Kyaleta Hajiya tayi ta surutu ita za ta makara".
   Da sauri Yusie ta yafa ƙaramin gyalenta wanda ya shiga da three quarter gown din da ke jikinta sai faded blue din jeans trouser.
Jakarta ta dauka tabi bayan MK da gudu, wanda har ya tada mota.
Tana shiga motar ta kwada ma shi littafin da ke hannunta, ta shagwabe fuska "shi ne ba za ka jira ni".
Murmushi yayi, tare da shafa sumar kan shi.
"I wish she's the one beside me". Ya furta a hankali.

"I know they say believe in love 😍 is a dream that can't real".
     Justin Bieber

   You can now send your Playlist to me via my email ayeeshasadeeq2010@gmail.com with your name and the singer name, then your Favorite quote in the song whether it's English, Arabic or Hausa music 🎶.

   Thank you guys for always being there for me, I love you like no tomorrow.
  Ku cigaba da haƙuri dani, ina da tests from next week Monday, so zan dauke ƙafa, idan na samu chance I'll update a chappy for you guys.
   Better days are coming In Shaa Allah.
#Madubi2017

    Kar na cika ku da surutu..

Bye
Shatu Kwankiyal ♥ 😘 😍 ♥
Social Media platforms all @ayeesh_chuchu
Don't forget to
Vote ❎
Comment 💭
Share &
Recommend.
It really means a lot to me.

MADUBI Where stories live. Discover now