MADUBI
©AYEESH CHUCHUBABI NA TALATIN
"And when you smile, the whole world stops and stares for awhile, cause you're amazing, just the way you are."
~ Bruno Mars (Just The Way You Are)AMINCI
"Gwaggo Halima wannan zakwaɗi haka? Allah yasa zagi ne inga ta iyayi".
"You're wicked girl. Bari in karanta ma ki ki ji".
"Assalamu Alaikum fountain of knowledge and wisdom. Na yaba da kwazonki kwarai da gaske, kin cancanci a yaba ma ki. Samun mace irin ki a wannan kafa sai an tona, Allah yasa har a fili haka ki ke Malama Halimatu? Ki cigaba da bada himma, da kuma taimakawa ƴan uwanki mata da naga kin fara. Ina yawan bibiyar rubuce-rubucenki ma su dauke da tsantsan hikima da basira. Allah ya saka da alheri akan irin fadakarwan da kikeyi, kuma ina yiwa your proposed maigida murna wallahi, he is lucky to have you as a life partner. Allah ya kara karfin gwiwa"."Wow! Toh ke kuma mi za ki ce ma sa?".
"Godiya kawai zanyi".
"A'a ke ma kin ɗan yaba ma kwazonsa kin ga sai ki ja maganar".
"Ce maki nayi fira nake son yi da shi? Kawai dai yana birge ni ne".
"Yi hakuri Gwaggo Halima maida wuƙar ina nan zaune ai zan ji komi".Nan ta maida masa amsa, tayi kamar yadda Laila ta ce tayi.
Tun daga ranar suna gaisawa sama-sama, wata ran su kan tattauna batutuwa da su ka shafi rayuwar yau da kullum.***
KAROFI"Hajiya ɗan Allah ki karɓo man yaro na in gan shi na sa shi a idanuna in ga gudan jinina. Kinga Abida ba ta son haihuwa da ni, duk ta gama zubar da cikkunan. Likita yace ba za ta ƙara haihuwa ba".
"Ni yanzu ko giyar wake na sha ai bana tunkari mutanen nan ba da maganar amso yaro. Da bakinka ka ce ɗa ba nake bane Salisu, ɗibar albarka iri-iri ka yi ma yar mutane. Sai yanzu in je in same su da magana ai ba ma zasu saurare ni ba".
"Ni dai ki ƙoƙarta Hajiya".
"A'a ka je da kanka ni ba inda za ni ina fama da ƙafafuna".
"Zan je Bakorin in ga".
"Da ya fi maka. Allah yasa su gane ka, irin yanƙwanewa da ka yi ai sai wanda ya yi ma farin sani tukunna".
Murmushin yaƙe yayi.
"ya na iya Hajiya. Rayuwa kenan. Ita Ammah har yanzu bs ta yi aure ba ne?".
"Ina zan sani ance dai kwanakin baya karatu take".
Ya gyada kai tare da fita daga gidan.Washegari ya tafi Bakori.
Da kyar ya gane gidansu Ammah saboda an ƙara gyara shi, anyi sabon fenti.
Ya aika yaro a kira masa Malam.
Ya fito suka gaisa.
"Wa nake gani kamar Salisu?".
"Ni ne Baba".
"In ce dai lafiya?".
"Lafiya lau. Dama zuwa na yi a taimaka a ban dama in riƙa ganin ɗana ɗan Allah".
"Babbar magana. Ina ga ai mun wuce wannan babin tun tuni koh? Shekaru nawa yaro har ya zama saurayi ".
" Taimako na za'a yi Baba".
"Maganar da mu ke ma yaro be anan Bakori gabadaya rayuwarshi tana Kano, idan ka gan shi nan to da mahaifiyarsa su ka zo. Ni rabon da insa Khalifa a Idona ai nayi shekara saboda yanayin karatunsa da ita Ammah".
"Toh ko za'a yi man kwatancen inda suke a can Kanon sai in je".
"A'a kar ma ka fara dan ba za ku daidaita da Ammah ba. Ka bari dai zanga yanda za'a yi".
"Toh nagode Baba".
Malam ya shiga cikin gida. Yana zaune yana cin abinci, Gwaggo da Inna na gefensa.
"Yau na ga abin mamaki. Rayuwar nan ba a bakin komi take ba, yanda ka dauke ta haka za ta bi da kai".
"Miya faru Malam?" faɗin Gwaggo
"Salisu tsohon mijin Ammah ya zo yana roƙon a ba shi dama ya riƙa ganin ɗansa".
"Ai kuwa yayi kadan. Dama ai ni na haɗa auren. Karya yake, ɗa na Ammah ne ba na shi ba".
"Yi hakuri Innani ai abin bai kai haka ba. Ya ban tausayi zan kira Ammah, a samu ko da cikin hutu ne Khalifa ya riƙa zuwa ganin mahaifinsa. Dan na san dai yanzu ya isa ya fara tambayar waye ubansa? Kinga kuwa gara ya san cewa shima yana da uba".
"Yanzu Malam duk wulaƙancin da yaron nan yayi mana ai be cancanci afuwa ba,yarinyar nan irin wahalar da ta sha ".
" Haka Allah ya ƙaddara ma ta, matsala da ku mata kenan ƙaramin tunani. Duk wanda ya ga yaron nan ya san rayuwa ta bi da shi".
"Ai shikenan Malam".
Inna kuwa ba ta ko tanka ma su ba.
Innani ta gama bambamin fadanta Malam ya nace akan batunsa.
"Da Mubarak na nan shi zan sa yaje har Kano ya dauko Khalifan. Yaro ya lula can uwa duniya da sunan wani abu wai sabis".
"Sai kace masu sabis ɗin mashin". Faɗin Innani
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...