MADUBI
AYEESH CHUCHU
BABI NA TALATIN DA DAYA"A haggu da dama kai naka dubi, na fadawa iyaye kai ne zaɓi, littafin so ciki babi-babi, Sunanka yana ciki fannin hubbi. Kowa ka gani cikin littafin galibi dole asalinsa mai mulki ko ko Sarautar soyayya".
~~~Rariya - Umar M ShariffThank you so much for your comments and votes, I really appreciate it.
The match name suggestions for Ya ARK and Ammah really sound sweet.... RUWAN ZUMA
Cikin siririyar muryarta ta ce "Ina wuni?".
"Lafiya lau".
"Ku tashi mu tafi, kai ka bi mu mu je park ɗin".
Ya gyada kai. Ya mike tare da kama hannun Ajwad.
Sun fito harabar gidan.
"Ya ARK bari Ammah da Amaal su bika tunda kai kadai ne".
"No! Ni da Ajwad za mu tafi".
Aunty Ayeesha ta ɗan maraice fuska.
"Su taho mu tafi".
Ammah da ke ta hararar sa kamar idanunta za su faɗo ƙasa.
Ta buɗe gaban motar ta shiga, Amaal ta zauna baya. Ya tada motar.
Aunty Ayeesha, Ajwad da Hameed a mota ɗaya su ne a gaba.
Waƙar Beyonce ce ke tashi a cikin motar mai taken crazy in love.
Tuƙi yake yana bin waƙar a hankali, murmushi dauke a saman fuskarshi.
Ammah na ta satar kallonsa ta gefen idanunta, kamar tayi dariya dan mamaki yake ba ta.
"Bana so ana satar kallona. Idan kallona za ki yi just turn your face and stare at me".
Idanu ta fito waje, muryarta na rawa.
" Ni fa ba kallonka nake. To ma mi zan kalla?".
"Na sani. Na ji kina son buɗe gidauniya. Abu ne mai kyau, idan ana buƙatar taimakona I'm ready to assist. All the best ".
" Nagode kwarai ".
"Ina son irin wannan aikin. Idan kin shirya zuwa CAC register ki kira ni, zan haɗa ki da abokina".
"Toh shikenan. Thank you ".
Murmushi ya yi
" Anytime".
Nan su ka sha kwanar shiga Abuja Garden da ke kallon F.S.P Hospital.
Sun sayi ticket sun shiga.
Ice-cream aunty Ayeesha ta je ta siyo ma su.
"Ya ARK ga naka".
"Kin manta ban shan Ice-cream".
"Ka cika ƙa'ida".
Murmushi ya yi.
"Ammah ga shi ".
" Thank you. Ki haɗa mun da ɗayan can".
Ta faɗa ƙasa-ƙasa.
Ta hau sha ba ƙaƙƙautawa. Ta na daukar hotuna.
Datan wayarta ta kunna, saƙona suka yi ta shigowa har su ka daina.
Facebook messenger ta shiga, nan ta iske saƙon Abdul Kabir har guda biyar, wanda kwana biyu ba su yi hira ba. Ta fara karantawa.
"Duk da an kore ni ban yi zuciya ba na dawo ".
" Fushi ki ke dani koh?".
"I'm so sorry, ba zan ƙara ba".
"Kin sa Yayanki ya kasa sukuni".
"Miya hanaki posting kwana biyu? I'm missing everything about you?".
Murmushi ta yi wanda ya bayyana fararen haƙoranta.
Ta maida ma sa amsa.
"Toh ba kai ne ba daga na ce kar aunty ta kama ka, ka daina mun magana".
"A'a ya zanyi fushi da Yayanah ".
" har ka sa na ji kunya da ka ce ba za ka ƙara ba".
"My phone was at faulty, shiyasa ban hau ba. I miss your posts".
Ta tura ma sa.
Kamar yana jira, sai ga amsar shi."Just tell me you're missing me.
Hope ba za ki ƙara guduwa ba?
Why did you hide everything about you? "." Lol! Nah! I didn't miss you 😉.
I'm back bazan ƙara gudu in bar Yaya Abdul ba.
Ummmm saboda tsaro".
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...