ƘADDARA TA RIGA FATA

2.5K 165 50
                                    

MADUBI
   ©AYEESH CHUCHU
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

I never dreamed
I'd love somebody like you
I never dreamed
I'd lose somebody like you
—Wicked Game by Chris Isaak

ƘADDARA TA RIGA FATA

***
KANO

  Bayan Wata Biyar

"MashaaAllah! Best friend an sami abinda ake so. Result ya yi kyau, tunda kin samu WAEC miye na ɓata rai dan ba ki ci Mathematics a NECO ba, ai ba'a ɓari a kwashe duka".
"Ya Deeq na so dai ai in kwashe dukan".
" Ba komi ai, na ji BUK sun kusa fara screening exercise ɗinsu. Koda yake ke da ga Mami ma ai sune abin".
"Ai ba fanninta ba ne. Ka ga dai kos ɗin da nake so ba su yinsa, zan yi maneji da Computer Science ɗin. I'm planning for something".
"Inyee! Ka ji manya. Saura biki koh?".
"You're wicked Ya Deeq. Ni yaushe na ce ma zanyi aure yanzu, sai nayi nisa da karatu na".
"Ku ji min yarinya. Bayan kin sa an amshi kayan auren na ki. Yanda nake ganin yaron nan ai ba zai iya haƙura ba har sai kin ƙare bokon".
"Ka tafi Ya Deeq na gaji da ganin ka. Ka ce ma aunty Maryam ina nan zuwa ma ta wuni gobe ".
" Marar kirki kawai. Ai fushi take da ke. Na kuma ƙara zugata".
"Sai ka isko ni muna rakashewa za ka gane".
Daga nan ya fita daga gidan.
Wayarta ce ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo.
Ta kwanta saman kujerar da ke falon sannan ta buɗe sakon.
"Habibty you just cross my mind. I miss your presence".
  Ta maida masa reply
"Qalbie you're always in my heart. A kowane motsi ina jin ka a tare da ni. So i didn't miss you".
"I didn't love you. I'm here in this world because of you. To stand by your side, to give you a shoulder to lean on at any moment, till my last breath".
Murmushi ta yi tare da ƙanƙame wayarta tana jin wata irin zazzafar soyayyar MK na ratsa dukkan sassan jikinta.
  Duka ta ji a cinyoyinta.
"Wayyo Allah. Evil woman".
"Sai an sace ki garin soyayya. Kina nan soyewa mutane na ta sallama kin lula wata duniyar".
"Ina tausaya ma ki ranar da soyayya za ta ma ki wawan kamu, za ki tantance mi ake ji. Qila ke sai abin da hali yayi".
"Uhmmm ni fa har yanzu banga namijin da ya kwanta mun a rai ba. Shiyasa har yanzu ba wanda na ba dama. Duka ma nawa nake da zan fara wata soyayya i'm Just 18 years. Kuma ma karatu na ba zai hadu da soyayya, aji biyu fa kawai na ke, saura na shekara uku".
"Sai ki faɗa mun ni ɗin nawa nake. Ina jin kin ban wata biyu ma. Nima idan ba Ya MK ɗin ba da shi na fara so, shi ya koya mun soyayyar sa ai da har yanzu banga saurayin yi ba".
"Ni mu bar zancen nan ma. I hate love stories".
"Rigimar ki yawa ne da ita. Ina Khalifa? Tun ɗazu ya kamata a ce ya dawo".
"Sai yanzu ki ka tuna. Ya Hashim ya dauke shi, mun biya AKTH gaida Hajja mu ka shiga ofis dinsa ya ce idan ya taso zai taho da shi".
"Ooh da kayan makarantar a jikinsa. Ni ma dai gobe zan je daga nan mu biya gidan Ya Deeq in huta gori".
"Wasa ya ke ma ki ai ya san cewa karatu ke hana ki leƙawa".
"Bakori ma nake son zuwa, na yi missing din Gwaggota. Inga Sa'ata tace ta zo gida. Kin san ta Abuja gidan kawunta can take karatu".
"Ba dan ba mu yi hutu ba da na ba ki. Ki ma Mami magana ba za ta hana ki ba. A'a lallai ta caɓa. Allah dai shi bamu sa'a. Amin".
  ***
"Sannu Hajja ".
" Yauwa Halima. Ki yafe mun duk abinda na yi ma ki. Sharrin zuciya ne. Ni tawa ta zo ƙarshe".
"Ki daina faɗin haka Hajja. Ai cuta ba mutuwa ba ce".
"Ni kadai na san yadda na ke ji a jikina".
   Ɗakin cike yake da iyalan Alhaji Kabir, ciki kuwa har da Ammah.
Jikin Hajja yayi tsanani ciwon suga gareta.
  Duk mai imani dole ya tausaya ma halin da take ciki.
  Washegari ta ranar Laraba, Allah yai ma Hajja cikawa.

***
BAKORI

"Gwaggo dambun nan yayi dadi, cikina ya koshi amma baki be gaji da taunawa ba".
"Sai ki zauna kiyi ta ci har ki kasa tashi".
"So ki ke in sai kun kama ni wajen tashi?".
"Eh! Ai naga baki son cin abinci ne. Maimakon ki taho man da ɗan mijina".
"Yana can makaranta".
"Wannan ɗan yaron har an saka shi makaranta?".
"Gwaggo shekara biyar fa har zai shiga ta shidda".
"Eh lallai an girma. Ga Mubarak nan ma".
"Ai na so ya cike BUK da na cike. Ya je ya cika Al-Qalam".
"Da Hajiya ta ce ƙasar waje za ta fitar da shi. Innani ta hana".
"Innani yar baƙinciki".
"Ubanki na ce. Ni ce yar baƙincikin?".
"Kai Innani nifa bance ba".
"Ai da yake an ce ma ki na kurumce ne. Toh na hana ɗin, hakanan yaro ya tafi ƙasar da ba uwa ba uba. Sai abinda yaga dama. A'a ban yarda ba gara yayi karatunsa kusa da gida".
"Hakan ai yafi".
"Ja'ira da kina kirana da yar baƙinciki".
Nan suka cigaba da raharsu, ana ta dariya.
Ta je har gidansu Sa'adatu ta yi rashin sa'a ba ta same ta, a ranar ta koma da safe. Sun dade suna fira da Mama, sai gab da maghrib ta dawo gida.

MADUBI Where stories live. Discover now