MADUBI
© AYEESH CHUCHUBABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
"In the fire of my transgressions
I am not all I hoped I would be
Search for life in the fathoms of the sea
In the heart where darkness lives
She forgives"
—She Forgives by ShadowboxersBA'A ƁARI...
Ta koma ta zauna kanta a ƙasa, saboda idanu da suka haɗa da matar da take ma ta kallon sani.
"Ga surukar ki nan ta zo ganin ki. Mahaifiyar Mukhtar".
Zuciyarta ta harba da karfi, ta na jin ƴan cikinta na ƙugi da juyawa saboda firgita.
Cikin dauriya ta tattara dukkan hankalinta ta sake gaida matar.
"MashaaAllah! Cute in-law".
"Kinga Halima Ammah".
"Na ganta. Shiyasa MK ya dage sai Ammah shi ya san abinda ya gani ba tare da ya duba wacece ita ba".
"Nayi mamaki ko ni, dan wannan zamanin da mu ke ciki a ce namijin da be taɓa auren fari ba ya fara da bazawara mai ɗa kuma da mamaki".
"Gaskiya ko ni a da ban goyi baya ba. Kasancewar Dakta mutum mai fahimta shi ya ƙara fahimtar da ni. Ya nuna man cewa auren mace bazawara ba laifi ba ne, abu ne mai kyau a addinance. Al'ada ce dai ta maida abin bai-bai".
"Hakane kam! Mukhtar ya taka rawar gani sosai".
"Ai sai yanzu na ƙara tabbatar da ya yi mata. Na ga wani passion a tattare da ita".
Murmushi suka yi, Ammah dai kanta a ƙasa.
"Tashi ki tafi".
Kamar dama jira take dan a takure take ga gajuya. Ta nufi ɗakinsu."Inyeee! Wata taga mother in-law ɗinta yau".
"Bari kawai! Wuyana har ya sage saboda ladabi. Na kusa zama matar MK".
Ta yi juyi.
"Ammah ba ki da kunya".
"Ki ji min yarinya in ƙi yin murnar mana".
"Ai da a gabansu ki ka yi ".
" Wannan ne ma mai sauki".
Wanka ta shiga ɗan ta warware gajiyar da ta kwaso a makaranta.***
"Ya MK ashe gado kayi? Banyi zaton Momi fiye da yanda na ganta ba. She is so nice".
"Ummm! Kin fara koh?".
Murmushi ya subuce a saman fuskarshi a yayin da ya danna madannan wayarsa (keypad).
"Mi ka ke yi ne a wayar?".
"Nothing! Wani saƙo ne ya dau hankalina".
"Kai da Laila ban san gwani ba. Kun faye ba ma waya muhimmanci".
"Na ce ma ki ki buɗe ko da WhatsApp ne, muna firar mu hankali kwance".
"Na buɗe Facebook da Twitter ai rannan, ban iya komi ciki ba sai rubuta what's on your mind . Ina da friends amma basu da yawa, ni fa sai na tantance na ke amsar tayin abota da mutum, nima kuma wadanda na duba furofayil ɗinsu na tabbatar da ingancinsu na ke turawa mawa. Kada in zo in haɗa abota da bara gurbi ".
"Yayi kyau! Ni Facebook be wani dame ni ba, kamar su Snapchat, Instagram, Skype da WhatsApp nafi yin su".
"Duk miye amfanin su?".
"Duk amfanin su ɗaya da Facebook da Twitter amma dai ya danganta da yanda mutum ya dauke su".
"Mmmm! Lallai. Nuna man su".
"A'a dauko wayarki in buda ma ki a ciki ki gani".
"A'a ni taka na ke so".
"Oou! Habibty rigimammiya".
Wayarshi ce ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo, yayi saurin dannawa dan maida amsa.
Yana duƙar da kai, ta sa hannu ta fizge wayar. Kafin ya ce mi har ta shige cikin gida.
Ta na shiga ɗaki ta wuce. Ta kwanta kan lounge da ke ɗakin. Ta latsa makunnin wayar har ta shiga key.
Ya MK tsaye, ya kasa ko motsawa daga inda yake. Tunanin sa be wuce kada Ammah ta bude ma sa waya ba.
Da ya tuna cewa zuwa lokacin da ta wuce wayar ta shiga security key, kuma ba ta san Password ɗinsa ba.
Ya saukar da ajiyar zuciya.
Gudar wayar yasa hannu ya dauka daga cikin dashboard ya danna lambobin Ammah.
"Habibty ki kawo man wayar zan tafi".
"So! Shikenan sai gobe. Take care Sweetheart".
Ya girgiza kai tare da murmushin rikicin Ammah.
"Drama Queen".
Ya furta a hankali, tare da shigewa cikin motarsa ya ƙara gaba.***
Ta yi duk wani bakin ƙokarinta wajen canke-canken Password ɗin wayar.
Tayi ta gwadawa har sau biyar, su ka ce ta jira tsawon minti uku kafin ta sake gwadawa.
A gwaji na shida tana sa qalbie wayar ta buɗe. Wani irin tsalle ta yi.
Abinda bata taɓa yi ba, ba ta taɓa riƙe wayar Ya MK ba. Hotuna ta shiga, ta na ta kallo. Har ta kai wata folder da aka sa ma "Memory".
Hotunanta ne birjik a ciki, tun daga lokacin haɗuwarsu har zuwa yau waɗannan ba ta ma san an dauke su ba.
Kan study table ta tafi, ta jona wayar USB cable ta haɗa su. Nan ta tura dukka hotunan da ke a faldar.
Ta cigaba da dubawa nan ta ci karo da falda mai suna Moments.
Suma ta duba su,ta tura wadanda za ts tura.
Ta buɗe whatsapp ɗinsa da yake suna da wireless ta kashe data ɗin wayar ta kunna WiFi.
Ta cigaba da bincikenta, ta shiga Instagram da Snapchat. Ta gama duk abinda take buƙata ta tattara bayanai ta tura a wayarta. Sannan ta kashe ma sa waya ta sa a chargy.
Ana kiran sallar maghrib ta yi shirin sallah.
Sai da ta yi isha'i ta shiga kicin, ta dau abincin Mami da Abba ta kai falon Abba. Da yake Laila da Khalifa sun je gidan Ya Deeq ya yi tafiya. Ya ARK kuma yana wajen aikinsa.
Ta kwashi sauran ta kai ma Mai gadi.
Kacaniyar haɗa pancake take,ta haɗa sukari da bota a mixer, sai ta tabbatar da sun hade da juna, ta fasa kwai ta zuba, ta zuba fulawa. Ta dauko madara a fridge ta zuba sai ta ga sun haɗe da juna komi ya yi. Sannan ta juye a kwano.
Ta kunna wuta, ta daura non-stick frying pan ɗinta ta yi greasing ɗin shi da bota. Ta na zubawa a kaskon. Idan yayi ta juya har ta gama.
Ruwan shayinta ta daura bayan ta saka ganyen na'a-na'a, lemon grass, cinnamon, citta, kaninfari, kimba da ganyen shayi a ciki ta rufe. Sai da suka dahu kamshin ya fito sosai ta tace tare da matse lemun tsami tasa sa zuma.
Sauran pancake ɗin ta adana. Ta dau wanda za ta ci ta sa a ɗan ƙaramin tray ta zuba Nutella a saman pancake ɗin da butar shayi ƙarama da kofi ta shige ɗaki.
Kan teburin karatu ta wuce ta ajiye tare da jan kujerar ta zauna.
Ta dukufa aiki ka'in da na'in tana kurɓar shayinta da pancake.
Ta leƙa Facebook ta dan yi rubuce-rubucenta a bangonta (timeline), ta leƙa Twitter ta yi abinda ya dace tayi.
A hankali tana maida ma masu tsokaci (comments) a rubutunta amsa akan tsokacinsu, hakan na daya daga cikin abin da ta ke so a Facebook, wato bayyana ra'ayi tare da wanzar da muhawara mai amfani yakan dauki lokacinta sosai, haka a bangaren Twitter ma.
A hankali ta fara samun tayi daga mutane mabambamta saboda yanayin rubutun da ta kan sadaukar da lokacinta wajen rubuta su dan ta isar da sakon da ke cikin zuciyarta ta kuma ankarar da wayar ma da jama'a kai musamman matasa.
Shafin Gotham Writers (GW) ta shiga in da take daukar darasi a duniyar gizo a fannin rubuce-rubuce (online writing class).
Anyi durussa biyu da safe wadanda ba ta samu damar duba su ba, ta fara karantawa ta bi tambayoyin da yan ajinsu su ka bari da kuma amsoshin tambayoyinsu, ta ba su awa ɗaya cur akan kwas ɗin da suke kai Creative Writing 101.
Sha daya saura ta kashe kwamfutar, ta ida shanye shayinta da pancake ta wuce bandaki.
Ta fito ta sanya pj ɗinta, ta kashe wutar dakin.
Wayarta ta janyo ta kira Laila.
"I missed you Twinie. Please ku dawo hakanan. Gidan babu dadi wallahi. Nima zan gudo in bar Mami idan ba ku dawo ba".
"A'a naƙi wayaun ki. Gobe - gobe za ki ganni".
Bayan sun gama ta ajiye wayarta, ta runtse idanunta dan tayi bacci amma ina, a lokacin ne abubuwa da dama suka bijiro ma ta.
Abubuwan da take tunanin ba za ta bari su dame ta ba bare har su hanata sukuni.
Zuciyarta ce tayi nauyi, hawaye masu zafi suka zubo ma ta.
"Why Ya MK?".
Kamar daga sama ta ga kiransa har wayar ta tsinke ba ta daga bisani aka sake kira.
Ta yi karfin halin dauka tare da seta kanta.
"Qalbie ba ka yi bacci ba?".
"A'a banyi ba, ina ta tunanin ki".
"Ko dai tunanin wayarka? I know how addicted you're with phone".
"Amma ai na fi zama addicted to you my habibty".
"Duk yanda ka ce. Ina ta Missing din Laila da Khalifa ".
" Yaa Allah! Habibty ba kunya yanzu har ki buɗi baki ki ce kina Missing Khalifa ".
" Ba ka san yanda yake da shiga rai ba ne. Ko daya ke kai ba ka da son yara".
"Ba wai bani da son yara ba, rigimarsu ce ban so. Kin san I'm planning for something Idan munyi Aure ".
" That means ko ni ba za ka iya hakuri da ni ba kenan, dan akwai lokuttan da har gara yaro da ni ".
" Habibty ke ta daban ce".
"Uhmm! Ni ka daina mun sweet mouth. Mun ma bata".
"Idan mun bata in bi ta ina inga haske? Ba ki san ke ce haskena ba?".
"Ya MK you're killing me. Stop it ban son mutuwa yanzu".
"Ni kuma in dai mutuwa a cikin soyayyarki ne I'm ready to die. Ammah kill me softly".
Dariya ta yi.
"You're wicked! Ba Yanzu za ka mutu ba. We need you in our lives ".
" We? Fa ki ka ce ".
" Yah! Ni da su Momi da sauran jama'a".
"Smart you ".
Sun ɗan jima suna fira kafin daga bisani ta cillar da wayar kamar mai iskokai. Ta rushe da kuka.
Ta tofe jikinta da addu'o'in bacci ta kwanta akan damarta tana fuskantar gabas!
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...