MADUBI
©AYEESH CHUCHUThis page is for you #AuntySisTeam (Deeylerh Aa Rasheed, Hawwy In-law, & Maryam Aqeel) & Xarah B_B you guys are amazing.
MADUBI is now #186 in MYSTERY/THRILLERBABI NA GOMA
Ihu Ade ta rusa "na shiga uku shikenan mota ta kaɗe man ɗiyata, ita kenan na mallaka".
Da gudu mai motar bus ɗin ya ƙara gaba ba tare da ya tsaya ba.
Nan aka samu wasu masu babura su ka bishi a baya. A yanda yake gudun ba'a tsammanin za su isko shi.
Mutane ne su ka yi dafifi a gefen da aka yi haɗarin motar.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Wannan ai ba ta ma numfashi".
"A'a a kai ta asibiti dai".
"Ai ga mahaifiyarta can ma, Asma u ce ta gidan Mal. Lawal".
Ade dake tsallaken titi, sai iface-iface take a haka ta tsallaka titin.
"ku matsa inga ɗiyata".
Girgiza Asma'u take yi, amma ina. Ta sake rushewa da sabon kuka.
"Kiyi hakuri Ade yanzu dai a tafi asibiti da ita".
Mota aka samu a saka Asma'u ciki, suka nufi COMPREHENSIVE HEALTHCARE (CHC) dake bayan gari.
Bayan gwaje-gwaje da aune-aunen da ma'aikatan jinya su ka gabatar ya tabbatar ma su da mutuwar Asma'u.
Kuka Ade ke yi, tana maganganu masu kama da sambatu.
"Na shiga uku, na kashe ɗiyata da kaina. Ki dawo Asma'u ba za ki auri Imranan ba. Malam ya cuce ni da ya duba yace akwai alheri tattare da aurennan, miyasa be duba man cewa mota ce za ta kaɗe ki ba".
Rizgar kuka ta ke,da kyar Mal. Lawal mahaifin Asma'u ya taushe ta, aka samo mota ta dau gawar Asma'u dan a yi ma ta sutura.
***
KATSINA
"MK jiki ya yi kyau sosai, yau kai ne harda fita gari".
"Ai na warke Daddy, Bakori nike son zuwa".
"Haka nike son ji. Bakori ka bari sati mai zuwa sai mu je akwai ɗaurin aure da zan je ,ya maganar School? Kaga dai duk an wuce ka, amma nasan banda matsala da ɗana".
"Ai Prof ba ni tunanin MK zai cigaba da karatu a ƙasar nan, kana gani har yanzu be gama warware ba. Kullum cikin tunani yake. Wata uku ai yaci A ce ya warke garas. Maganar shi ba ta wuce ta wannan yarinyar, sai kace jinin mayu, Inaga dai kurwarshi su ka lashe. Daga samun sauƙin shi zai wani ce za shi Bakori, to wallahi ba da yawuna ba".
"Haba Dakta! Ya za ki riƙa irin wannan maganar dama can haka Allah ya ƙaddaro. Na fahimci MK yana son taimakawa yarinyar ne".
"Duk son taimakon shi ya kai iyayen da suka haifeta ne?".
Ƙarar buga ƙofa suka ji, wadda yanayin da aka rufe ƙofar zai tabbatar da cewa an buga ne cikin fushi.
"Kinga irinta koh? Bani son kina irin wannan maganar a gaban MK".
"Shiyasa nace gara ya tafi can wata ƙasar ko ya manta da ita".
Farfesa be saurari Momi ba, ya bi sahun MK. A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe.
Kwance ya iske MK ya yi matashi da hannayensa, idanunsa a lumshe, shi kadai ya bar ma kan shi sanin tunanin da yake. Mazauni ya nema kan shi akan lounge chair da ke kallon king size bed da MK ke kwance.
Ɗaki ne na alfarma wanda aka ƙawatashi da furniture na alfarma. Komi na ɗakin ash color ne.
"Mukhtaar".
"Na'am Daddy".
"Tashi zaune".
Ba musu ya tashi ya jingina bayanshi jikin gadon.
"Mukhtar ina so duk tambayar na maka ka bani amsa".
"In Shaa Allahu Daddy".
"Tsakaninka da Allah son yarinyar nan ka ke, ko kuwa kawai taimakonta ka ke son yi".
"Daddy ni kawai ban san mi ke damuna ba,abinda na sani ina jinta kamar 'yar uwata, kamar wata part ta rayuwana".
Murmushi Daddy ya yi.
"Na fahimce ka, sai magana ta gaba. Mahaifiyarka ta nuna bata son cigaba da karatun ka anan, ka amince ko kuwa?".
"Daddy duk abin da ku ka yanke dai-dai ne".
"Good boy, Allah Shi ma ka albarka ".
" Amin".
Daddy na fita, MK ya hau nushin katifa yana faɗin "why? Why? Why???".
Ya rasa mike damunshi game da Ammah. Wayarshi ya dauko, ya bude gallery inda yayi tozali da hotunan da ya dauki Ammah, wadanda duk ba ta san da su ba. Yawanci duk a lokacin da ya ke koya ma ta karatu ne.
Anan yaci karo da wani hotonta da ya dauka tana dariya, fareren haƙoranta da suka jeru ras, sai wushirya.
A haka har bacci ya yi awon gaba da shi.
* * *
BAKORI
Kuka take ba ƙaƙƙautawa tamkar za ta shiɗe, idanunta sun yi jajir! tamkar garwashi,saman hancinta ya yi ja, ga majina dake tsiyaya. Tana ajiyar zuciya kai-da-kai.
"Ammah idan ki ka cigaba irin wannan kukan ba ƙaramin lahani za ki yi ma kan ki ba, ki sawa zuciyarki salama. Allah be ƙaddaro da ke za a je Katsina gasar nan ba. Kina ganin duk irin ban baki da ake ma Malam amma ya yi kunnen uwar shegu da batun. Nan har Maigari da chairman sai da su ka kira shi amma yaƙi,tunda har Innani ta hana babu wanda ya isa ya sa shi".
Wani sabon kukan ta barke da shi, tana jin wani irin zafi a ƙirjinta, ga wani ƙululu da ya tsaya ma ta a wuya.
Cikin kuka ta furta "Shikenan ba zan ga Ya MK ba?".
Daga kukan bacci ya dauketa wanda zazzaɓi mai zafi ya rufeta.
Tunda ya shigo gidan yayi sallama, suka amsa, sai sannu da zuwa da su ka mashi kamar sun haɗe baki har matanshi, ba wanda ya ƙara bi ta kan shi har da ðan ƙaraminsu Abdullahi wanda ya saba zuwa ya ðare shi ya amsar ma su tsarabar su.
Turakarshi ya shige, fuskarshi dauke da mamaki ƙarara.
"Ki tashi ki kai ma sa abincinsa" In ji Gwaggo.
"Bari in aiki Mubarak".
"A'a tunda dai ke ce da girki ki je".
Haka Inna ta dauki kanukan abincin Malam ta kai ma sa, ya na zaune yana sauraren BBC Hausa a cikin shirin su na dare da su ke gabatarwa 08:30pm. Tana ajiyewa ta juya ta fita, ba tare da ta jira ya ci abincin ba, kamar yadda su ka saba ma sa.
Ya yi jim! Kafin daga bisani ya buɗe kwanon silba da aka zubo ma sa tuwon shinkafa da miyar kuɓewa busassa da ke ta kamshin daddawa da man shanu. Hannunshi ya wanke sannan ya yi Bismillah ya fara ci.
Da kyar ya kammala cin abincin sa, saboda kaɗaicin rashin ðaya daga cikin matanshi a kusa.
Fitowa ya yi, inda ya iske ya'yanshi maza suna cin tuwonsu cikin faranti guda. Daga gefen su kuma Gwaggo da Inna ne ke ci.
"Ina Ammah? Ita ba ta cin abincin ne?".
"Ta na ɗaki, zazzabi ke damunta". Faɗin Gwaggo, ta cigaba da cin abincinta. Babu wanda ya damu da tsayuwarsa a wajen, saɓanin sauran lokuta da zai zauna cikin iyalinshi su yi fira.
Ɗakin Gwaggo ya nufa, numfashinta da ke fita da ƙarfi, ya ƙarasa bakin gadon. Ya yaye zanin da ta rufa da shi, jikinta zafi rau! A gigice ya dauke hannunsa.
"Ammah!".
"Halimatu". Nan ma shiru ba amsa, a gigice ya kwala ma su Gwaggo kira.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka wuce da ita asibiti in da aka ba ta gado.
* * *
BAYAN KWANA BIYU
Har yau matanshi sun kasa sakin jikinsu da shi, wanda hakan ba ƙaramin damunsa ya ke ba. Rashin jituwa irin hakan be taɓa giftawa a gidan ba sai wannan karon.
Wanda hakan har ya soma taɓa sana'arshi wadda be maida hankali sosai wajen kwastomas (customers) ɗinsa.
Yayi zurfi wajen tunani, inda ya tuno dalilin da ya kawo hargitsi a gidanshi.
KWANAKI TAKWAS DA SU KA WUCE
Innani ce ta zo gidan suna zaune a tsakar gidan.
"Wai ni tunda na zo ban ga Ammah ba, yanzu da tare da saurayin na ta na zo haka ze ta jira?".
"Innani Ammah na can wajen Maigari, su na shirin tafiya Katsina inda zasu je musabaƙa jibi".
"Daga nan har Katsina?".
"Eh Innani ki ka sani ma ta taho ma ki da kujerar hajji".
"Rufe man baki Iro, idan ba rashin hankali ba yaushe za ka bar kamar Ammah ta tafi can wata duniyar, babu kowa na ta. Ina ai ba zan yarda ba".
"Kiyi haƙuri Innani naga karatun Al-Ƙur'ani ne".
"Haba Iro! Ya za ka bari son ƴaƴa ya ma ka illa haka? Har ka kasa tantance tsakanin gaskiya da ƙarya. Yanzu sai ka bar Ammah ta tsallake ƙafa ta tafi ba uwa ba uba, idan wani abin ya same ta fa? Dan haka ba inda za ta, wanda ta yi ma Allah shi amfana".
Zuciyarsa sam! Ba ɗaɗi babu yanda ya iya da Innani, mahaifiya ce dole ya ma ta biyayya.
"Shikenan Innani, duk yanda kika ce haka za a yi".
Su Gwaggo da ke sauraren Innani su ka yi shiru, kowa da abin da yake ƙissimawa a ranshi.
Gwaggo za ta buɗe baki ta yi magana, Inna ta girgiza ma ta kai.
"Assalamu Alaikum".
"Wa alaikumus salam".
Su ka shigo ita da ƙannenta su na murnar ganin Innani.
Ammah a ɗarare ta gaida Innanin, za ta tashi Innani ta ce "Zauna, daga yau kar in sake ganin ƙafarki ta taka waje ba, na gaji da yawace-yawacen nan".
"Innani jibi za mu tafi gasar Al-Ƙur'ani fa".
"Eh! Na sani ba inda za ki ji, kuma ki jira mijin da na zaɓa ma ki na nan zuwa ya je Lagos ne jiya ya dawo".
Cikin kiɗima, hawaye masu zafi su ka tsiyayo ma ta.
"Innani dan Allah ki bar ni in je, ki taimaki rayuwata". Kuka take bil haƙƙi da gaskiya.
Hakan be sassauto da zuciyar Innani ba. Har ta tafi iyalan gidan ba su yi maraba da zuwanta ba.
Ganin irin kukan da Ammah ke yi ya sa Malam Iro ya buga ma ta tsawa "Idan ki ka bari na sake jin sautin kukanki sai na sassaɓa ma ki". Daga haka ya fita daga gidan shi ma.
***
Ya sauke ajiyar zuciya, ya na jin rashin kyautawa da ya yi ma ɗiyarsa, aƙalla da ya lallasheta har ta fahimce shi. Sai kuma ya ƙara ma ta zafi.
Rufe shagonsa na siyar da kayan masarufi ya yi, ya kamo hanyar gida saman babur ɗinsa.
Jajjaje Ammah ke yi na abincin rana, gidan shiru duk suna makaranta.
"Sannu da zuwa Baba".
"Yauwa Ammah,Ina iyayen na ki?".
"Sun je barka gidan Mal. Habu".
"Zo nan Ammah ".
" Toh Baba".
Ta zauna ƙasan tabarmar daga gefe.
"Ammah". Ta ɗago ta kalle shi.
"Na san ba'a kyauta ma ki ba, ki cigaba da haƙuri wata rana sai labari. Innani mahaifiyata ce, banda yanda zanyi da ita. Ki bi umarni na In Shaa Allahu ba za ki taɓa dana sani ba. Ki cigaba da haƙurin da na san ki da shi. Tashi ki je Allah shi ma ki albarka ".
" Amin Baba".
Fuskarta dauke da murmushi, ta na jin kaso saba'in (70%) na damuwarta ta yaye. Ba abinda yafi ma ta ɗaɗi irin a sa ma ta albarka.
Ta gama jajjajen da take ta dora ma su taliya ƴar Hausa. Ta tsaka da sanwar ne su Gwaggo su ka dawo.
Bayan sun gama cin abinci, ta sami Gwaggo a ɗaki tana son yi ma ta magana ta kasa.
Gwaggon na sane da yanayin na Ammah.
"Ammah ya aka yi ne?".
"Mm.. Mmm.. Da ma cewa zanyi ki ma su Mubarak magana idan dan ni su ke fushi da Baba su yi haƙuri su daina, haka Allah ya ƙaddaro man".
Gwaggo ta jinjina kai, ta san ba da su Mubarak kadai ta ke ba, har da su.
"Shikenan Ammah, ki ta haƙuri har zuwa lokacin da al'amura za su daidaita".
Ta gyada kai, idanunta su ka sauka akan zoben da ke yatsan, murmushi ta yi na musamman wanda ke zuwa ma ta a duk sa'in da ta kai duba ga zoben.
"Allah shi kare ka a duk inda ka ke Ya MK". Ta furta a hankali.
* * *
KATSINA
Daga matattakalar bena ya ke safkowa, sanye da polo shirt samfurin Ralph Lauren kalar sararin samaniya (Sky Blue), da baƙin wandon jeans. Idanunsa manne cikin bakin gilashin RAY BAN,tsintsiyar hannunshi na ta kyalli da agogon da ke daure. Duk inda ake neman haɗadden matashi mai jini a jika ya kai. Cikin sassarfa ya safko downstairs.
"MK har ka shirya?".
"Eh Daddy".
"Ok! Mu je ka ci Last lunch ɗinka kafin ka dawo".
Ya ja ɗaya daga cikin kujerun da su ka kewaye dinning table ɗin, ya zauna ya na kallon mahaifansa.
Khadija (matar Yaya Habib) ce ke serving ɗinsu.
"Aunty Khadija ina kike so in kai wannan abincin?".
"So nike ka ci har ka kasa tashi".
"Koda ya ci har yayi missing flight ɗinshi". Faɗin Yaya Habib, su ka ɗan Dara sannan su ka fara cin abinci.
Gabadaya suka fito in da Daddy da Momi na a mota ɗaya, sai MK, Yaya Habib da Aunty Khadija a mota ɗaya, cikin 'yan mintuna su ka isa tamfatsetsen filin jirgin sama na UMAR MUSA YAR'ADUA.
Su ka fito, anan Daddy ke ƙara ja ma MK kunne.
"Ka kula da addininka Mukhtaar, banda wasa ka ga dai can ba uwa ba uba. Ka tuna duk abinda za kayi Allah na kallonka".
Hawaye su ka tsiyayo ma sa, Momi kuwa kasa magana ta yi, shi ma Daddy'n dauriya ya ke yi.
Suna nan aka yi duk abin da za a har jirgin su MK ya ɗaga zuwa birnin Bonn na tarayyar Jamus (Germany), inda ya samu gurbin karatu (admission) a UNIVERSITY OF BONN, zai karanci EDUCATIONAL SOCIOLOGY.
* * *
BAKORI
"Ance ana sallama da Ammah a waje"
Ammah ta dafe ƙirji tare da zaro ido.
"Je ka ce wanene?", ya fita ya dawo.
"Ya ce Salisu ne, Innani ta turo shi".
"Gwaggo sh sh shine wanda Innani ta ce ".
" Eh! Bari in fita, ai baya fara zuwa wajen ki kai tsaye ba. Ya fara neman izini".
Gwaggo ta yi hanyar wajen gidan.More dramas 😉 are coming.
#Ammah&Salisu (love 😍 birds). LolKu yi haƙuri da wannan, ƙila gobe In yi Update ƙila kuma sai Monday In Shaa Allahu.
Vote, Vote and Comments.
Show that love 😍 please.chuchungaye.wordpress.com
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...