MADUBI
©AYEESH CHUCHU
One word for the chapter please
BABI NA SHA HUDUWUYA BA TA KISA
BAKORI
"Wai lafiyarki kuwa Sa'a? Tun da kika dawo yanayin ya sauya. Mi ke damunki ne?".
"Mama tausayin Ammah nike ji. Tana son karatun boko, ba yanda za ta yi an hana ta. Da ina da dama da sai Ammah ta yi karatun bokon da take son yi".
"Ki cigaba da ma ta addu'a mutum baya wuce ƙaddararsa Sa'a. Idan Allah ya yi sai kiga tayi".
"Hakane Mama".
Mama na tashi, ta dan murmusa. Hawaye suka gangaro saman fuskarta da tuno yanayin da ta baro Ammah.
"Allah ya isar ma ki Ammah". Ta furta a hankali.
"Sa'a ki je gidansu Ammah ki gaida Innani ba ta lafiya an dawo da ita daga Karafo".
"Eh haka Ammah ta ce mun".
Hijabinta da ke samun kujera ta dauka.
Da sallamarta ta shiga gidan.
Inna da Gwaggo ne zaune saman tabarma suna fira.
"Lale marhabun".Murmushi ta yi.
"Gwaggo kamar dai wata baƙuwa".
"Ai murnar ganinki nake. Kamar na ga Ammah haka na ji".
"Wannan ƙauna ta ku ba algus Gwaggo".
"Ja'irar gaske. Ya kika baro Ammah?".
"Lafiya lau take, tana gaishe da ku".
"Toh Madallah".
"Ashe Innani jiki ba dadi?".
"Wallahi kuwa, tana ɗaki ki shiga".
"Allah shi ba ta lafiya ".
" Amin ya rabbi ".
Tare da Gwaggo suka shiga ɗakin da Innani ke kwance tana bacci. Ta dan zauna na yan mintuna suka fito.
" Jibi zan koma makaranta Gwaggo".
"Allah shi bada sa'ar karatu. A dage sosai Tunda kin samu damar da za ki yi karatun ki. Aji nawa ki ke?".
"Aji biyu (J. S. S 2) zangon karshe (3rd term) zamu shiga da mun dawo hutu aji uku zan shiga".
"Gaskiya na ji dadi sosai. Kwanakin ja suke. Allah shi bada sa'a ".
" Amin Gwaggo na gode".
Gwaggo ta kwance ƙullin zaninta ta fiddo kudi.
"Amshi nan ba yawa ki ƙara".
"Allah ki bar shi Gwaggo, hidimar ai tayi yawa".
"Uwaki da hidimar. Ke da Ammah duk daya kuke a wajena".
"Toh Nagode Gwaggo, Allah shi kara buɗi".
"Amin".
Ta sa kai ta fita daga gidan bayan ta ma su sallama."Gwaggo yarinyar nan akwai hankali. Ina ji ina ma Ammah ce".
"Sa'a akwai natsuwa shiyasa abotarsu ta zo daya da Ammah. Gogewa kadai za ta nuna ma Ammah. Kin san shi ilimin zamanin nan, idan ka haɗa shi da na addini sai ki ga mutum gwanin ban sha'awa".
"Hakane kam. Allah ya sa mu dace".
"Amin! Ina kyautata zaton wata rana Ammah za a dama da ita in Allah ya yarda".12:16pm
"Abubakar ka taimake ni dan Allah ka je Karofi gidan Ammah kafin Mama ta dawo. Ka ga yanzu ta fita gidan bikin nan, zuwa sanda za ta dawo ka dawo".
"Toh bari in kira Mubarak muje tare".
"A'a ban son tonon silili, wannan sirri ne tsakanina da kai. Kar ka bari kowa ya ji zancen nan dan Allah Abubakar, ko Mama bance ka faɗama wa ba idan ban nan ".
" An gama Aunty Sa'a. Ki ba ni kuɗin mashin".
"Yauwa ɗan gari. Tsarabarka daban take ta wannan term ɗin".
Ta ƙulle bakin bacco ɗin da zare ta mika masa.
"Ungo ɗari uku nan kayi kudin mashin sauran ka dauka. Banda wasa dan Allah".KAROFI
01:05pm
"Assalamu Alaikum".
Jin sallamar da ake yasa ta dauraye hannuwanta daga cikin ruwan wankin da take yi.
"Wash! Bayana".
Hijabinta da ke sagale jikin igiyar shanya ta dauka.
"Wa alaikumus salamu".
Ta buɗe ƙofar.
"Ikon Allah! Abu kai ne da rana tsakar nan shigo".
Ta masa iso har cikin madaidaicin falonta.
"Ni ne Yaya Ammah, Aunty Sa'a ta aiko ni".
"Sa'a manya. Jiya ta bar gidan nan, ko sallama ba ta bari munyi ba".
"Hala faɗa ku ka yi?".
"Wane irin faɗa? Ka san Sa'a da daukar zafi. In ji dai ba ta faɗi wata magana ba".
"A'a ban ji komi ba".
Ta tashi ta kawo masa ruwa a kofin silba.
"Ga ruwa nan, ban samu na daura sanwa ba ina wanki".
"Kar ki damu ai yanzu zan juya sauri nake ".
" A'a ka jira in daura abincin mana".
Ta faɗa cikin rawar murya.
"Kinga tashi na, tun Aunty Sa'a ba ta mun Masifa ba".
"Sa'a manya, hali na nan ba za ta canza ba".
"Ai sai ƙaruwa ma da yayi".
"Kai Abu ban son sharri fa".
"Allah kuwa Yaya Ammah. Ni zan koma".
"Wai tun yanzu ko ruwan ba ka sha ba, ga ba Yan aike rana tayi da ko lemu nasa an sayo ma ka".
"Ba komi ai ni na gida ne".
Ta shiga ðaki ta fito.
"Toh Ungo wannan ka sayi wani abu a hanya. Ka gaida mun da Mama. Kace ma Sa'a na gode".
"Ki bar kudinki Wallahi ".
" Ai ni nayi niyya".
Dole ya karɓa tare da ma ta godiya ya tafi.
Ta raka shi har bakin ƙofar gidan, ta juyo.
Ganin tulin wankin da ke gabanta yasa tayi saurin cire hijabinta.
"Na shiga uku ko rabi ban yi ba, ga rana ta yi tsaka".
Ɗakinta ta shiga, za ta buɗe baccon da Abubakar ya kawo ma ta.
Ta jiyo muryar Salisu daga ƙofar gida.
Da sauri ta ja baccon ta kai ðakinta ta tura karkashin gado.
Ta dawo ta cigaba da wankinta,zuciyarta na bugun tara-tara, goma - goma.
Ba ta ko ji sallamarsa ba sai saukar dundu da ta ji a tsakiyar bayanta.
"Watau ke ba ki ji kasheɗin da na yi ma ki ba koh? Ince ki gama wankin nan kafin in dawo shi ne za ki nuna man isata".
"Ka yi hakuri dan Allah bayana ke ciwo shiyasa".
"Iye! Har kina da bakin cewa bayanki ke ciwo ko?".
"Za ki ci ubanki kuwa yau a gidan nan".
Hawaye suka fara zarya a idanunta,tana hada shi da Allah. Hakan be sa Salisu ya saduda ba.
Kafa yasa yai ta haurinta a ƙasa ta na kuka. Yayi mai isarsa ya shige daki tare da ba ta kashedi.
Zafin simintin da take kwance ya sa ta rarrafa zuwa baranda ta kwanta da kyar jikinta na ma ta radadi da zafi.
Ta kai kusan mintuna goma sha biyar a kwance kafin daga bisani ta miƙe da kyar jikinta na ma ta tsami.
Ta ci gaba da wankin da take ga yunwa da ke azalzalarta.
Ana kiran sallar la'asar ta na idar da wankin, ta kwashe wadanda suka bushe ta shigar da su.
Kwance yake saman kujera ya miƙe ƙafafunsa yana waya tare da kashe murya kamar mace.
Wani miyau ta haɗiya "muƙut" a sakamakon doya da kwai da ta gani a cikin takarda, wanda daga gani an ci an bar saura ne.
Dariyar shi ta ankarar da ita.
"Haba dai Sarauniya, ai nayi kewarki sosai wallahi. Kwana biyu kawai ji na nake kamar maraya. Gadona yayi faɗi ya zama tamkar dokar daji idan na waiwaya babu ke".
"A'a ki bari dai zanyi tunani akai".
Ammah da ke tsaye ta kasa motsi saboda kalaman da ke fita daga bakinshi.
Ta zube kayan saman kujera.
Za ta fita ya kira ta.
"Dauki sauran doyar nan ki ci, kar ki sake ki daura sanwa yau ban son almubazzaranci".
Kai ta girgiza ta dau doya ta samu waje ta fara ci tana hadawa da ruwa dan cikin ya dauka.
"Idan kin gama ki shiga gidan da ke kallon namu babban gidan can, uban gidana ne sun zo shi da iyalinsa ganin gida".
"Toh".
***
Sallah ta yi, ta gyara gidanta tsab! Ta kunna tsintsiyar kamshi gida ya dau kamshi, ta fada bandaki.
Riga da siket na atamfa ta saka, kayan sun zauna das! A jikinta. Duk da ba wata kwalliya a fuskarta sai zunzurutun natural beauty wanda babu mis (mix). Kwalli ta zizara ma idanunta, sai powder da ta shafa da labbanta da ke ta kyalli cikin man leɓe (lip gloss).
Falo ta dawo ta zauna. Baccon da Abubakar ya kawo ma ta, ta zazzage. Jakar alawa mai tsinke (lollipop) ce, sai ledar magi mai tauraro da farin magi (ajino motor), sai cabin biscuit da cingam (chewing gum) kwali ɗaya. Kowanne da kuɗinsa a jiki a manna da takarda.
Murmushi ta yi hade da hawaye da suka zubo ma ta.
Mutane biyu suka fado ma ta a rai.
Ta kasa boye farincikinta, sallamar da ta ji daga waje yasa tayi saurin tashi.
Ta buɗe ƙofar.
"Ki shigo".
Tayi ma su iso cikin gidan.
Suka gaisa da kyakkyawar matashiyar matar da ba za ta wuce shekara ashirin da biyar ba, sai yaron da ke riƙe a hannunta tamkar Bature.
"Ba ki sanni ba ko?"
"Eh gaskiya da yake ban dade da tarewa ba".
"Allah sarki shiyasa ba za ki sanni ba, ai waccan shekarar na zo ina da cikin Ajwad".
"Eh shiyasa, amma ba nan kauyen kuke ba?".
"Yes! Mijina ne dan nan, shi ma kakanninsa ne. Amma iyayensa duk suna Kano. Na manta ban faɗa ma ki ba sunana Ayeesha, mu neighbors ne. Gidana na kallon na ki, mai green gate". Ammah ta yi murmushi "Sunanki dana danki duk na yan gayu. Dama kune mijina yace in shiga gidan".
"Ke ma gaki nan yar Gayu da ke. Eh mune ".
"A'a Aunty ki daina zolayata".
"toh na ji, ba ki fada man sunanki ba".
"Sunana Halimatu, amfi kirana da Ammah".
"Wow! You've a nice name. Sunan Mamita gare ki. Idan kika ganki da sister na Laila kuna kama. Haske da wayewa kadai za ta nuna ma ki".
" Allah sarki. Ashe dama ma su kudi na magana da talaka haka?".
Ayeesha ta danyi murmushi.
"Ai da mai kudi da talaka duk daya suke a wajen Allah. Kinga ni haka muka taso Mami ba ta yarda da wulakanta mutum ba. Ta kan daraja mutum ko a ya yake. Dawowarmu Nigeria mun dan sha wuya kafin mu saba. Amma yanzu ya zama tarihi, mukam ba kowanne mutum darajarsa".
"Halinku ɗaya da Yaya MK".
"Kar fa Kice na cika surutu, haka na ke. Ina da son mutane kar ki damu. Ban labarin waye Yaya MK?".
Nan Ammah ta kwashe labarinta ta ba Ayeesha har zuwa aurenta da Salisu. Rayuwar aurenta kadai ta boye saboda maganar Sa'a.
"Na tausaya ma ki Ammah, ki cigaba da haƙuri idan da rabo za ki yi. Sai na ƙara jinki kamar Laila. Zan zo ganin akwatin da MK ya baki amma ba zan zo karya alkawarin da ke tsakaninku ba".
"Bari in dauko ma ki shi ki gani ba sai kin bude ba".
Ta shiga daki ta fiddo da akwatin.
"Wow! Daga gani MK dan soyayya ne. Na so a ce shi kika aura dan tabbas zai cika ma ki burinki. Amma hakan ma wa ta kaddara ce da Allah kadai ya san nufinta".
"Hakane".
"Kinji an kira maghrib bari in tafi gida. Ina fatan zumuncinmu zai daure kafin mu koma".
"In Shaa Allahu. Ajwad tafi wajen Mama za ku tafi".
Yaron ya sake lafewa jikin Ammah.
Da kyar aka samu ya yarda suka tafi.
Sallah ta yi tana zaune tana azkar har aka kira sallar isha'i.
Bayan ta idar ta tattara kayan sana'arta tana shi ma Sa'a albarka.
Cikin ta ji yana ƙugin yunwa, ta lallaba ta haye kan gado saboda ƙullewa da cikin yayi.***
Ƙarar fadowar mutum ta ji samanta, an kai ma ta wawura.
Ta ƙanƙame jikinta, ta na sallalami.
"Sarauniya na yi kewar jikinki, ki taimake ni a matse nake".
Yanda yake maganar kadai zai tabbatar ma ka da cewa baya cikin hayyacinsa.
Ƙarar keta kayan jikinta ya dawo da ita hankalinta. Ta rushe da kuka, tana neman hanyar taimakon kanta.
Ta kasa ko da juyi ne,saboda karfin da Salisu ya sakar ma ta.
Ta runtse idanunta tana ambaton Allah cikin duk irin addu'ar da ta zo bakinta.
Wasu irin saƙonni masu birkita kwakwalwa da damula lissafi ya shiga aikata ma ta. Sam! Ta kasa jurewa da daukar wannan bakon lamarin.
Jikinta ya hau kyarma, zufa na karyo ma ta ko ta ina.
Dan ƙaramin bakinta ta ji an kai ma hari ta kasa furta harafi daya. Zuciyarta ba ta bar harbawa ba, har sai da Salisu yayi ma bakinta salama.
Kuka take bil hakki da gaskiya.
"Sauraniya! Yau kin fiye man mata dubu. Na ba ki sarautar zuciyata".
Ƙara ta kwalla a sakamakon wani azababben zafi da ya kai ma ta ziyara.Pweeeeeehhhhhh! I think someone prays for me today. I never thought of finishing this chapter today.
MashaaAllah! It's not my wish keeping you guys waiting. I'm really sorry. Accept my apology.
You know I do love 😍 you with all my heart ♥.
You're my Lovey-dovies na..
Add smile ☺ to my puppy face 😔 by voting, sharing and commenting. Jazaakumullahu khair as you vote and comment for this story.Here we're! MADUBI has lost it position for being #1 in mystery/thrillers month back.
Alhamdulillahi! Your votes and comments are like magic wolla 😂we're now #2.Please ONE WORD for the chappy.
The next chapter will be dedicated to those that vote and comment.
I love 😍 Irin Sosai din nan...
Don't break that chemical bond that exist between us.
Barakallahu feekum..
See ya leraaaOopps! Don't hesitate to drop ur suggestions at ayeeshasadeeq2010@gmail.com
chuchungaye.wordpress.com
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...