MADUBI
© AYEESH CHUCHU
I dedicated this chapter to AuntySis,iLubiee (Lubabatu Maitafsir), Jamielerh (Barr. Jay (Gwaggo Jawiya), Aunty Badiyya, Zainab Dalhat, AishatuUsman, AsmieAmeen, Ummydaa,Fatie Nas, Zarah BB, Maijidda Musa, Najfar, Aunty Muneerat, Beauty Rush Ladies, Aunty Ammah and lot more.. Kun biyo ni bashi..
Thanks for always being there for me. God bless you all as you stand by my side.
ILYSVM❤
BABI NA SHA BIYARKOWANE TSUNTSU...
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Allah ya isa shege dan iska".
Ta ci gaba da gunjin kukanta,bakinta ya haɗa da na sa dan dole ta yi shiru. Duk irin ture-ture da Ammah ke yi hakan be sa Salisu ya saurara ma ta ba. Sai da ya tabbatar ya gamsu sannan ya kyaleta. Be ko dubi halin da take ciki ba ya tsallaketa ya wuce falo ya kwanta.
Haushi da takaicin kansa ya ke ji,shi kadai ke ta maganganunsa da ya kasa boyewa a zuci.
"Wai ina hankalina ya je na far ma wannan yarinyar? Ko da ya ke tana da mamora, ko ta nan zan more kudina. Ba ta da wani amfani da ya wuce bauta".
Ammah kuwa na can kwance ko motsi ta kasa,tayi iyakar bakin ƙoƙarinta na ta tashi amma abin ya ci tura.
Kan kunnenta aka kirawo sallah har aka sallame ta kasa tashi. Muryarta ta dishe saboda kuka ba ta fita.
Gari ya yi haske sharr! Salisu na kwance be da niyyar tashi yayi sallah, dama Ammah ce ke da jimirin tada shi duk da irin zagin da take sha a yayin tada shi.
09:13am
Miƙa yayi tare da yin hamma ya buɗe ƙofar falon, wanka ya je yayo.
Ido huɗu su ka yi da juna, ya daure fuska tamau! Fuskarta duk ta bushe tayi fari fat! Da hawaye da majina.
Yayi saurin dauke Idanunsa ya dau kayanshi ya fita daga ɗakin.
Sai da ya gama shirinsa tsab! Ya leƙo ɗakin "Ke kuwa anyi raguwar banza. Idan ma za ki daina lambo ki daina ki tashi ki gyara kanki idan ba ki iyawa kuma kiyi ta zama haka har in dawo daga tafiyar da zan yi. Ga kuɗi nan kan kujera ki kai ma Hajiyata idan kin so ki dauka ciki ki ga yanda zan babbalaki idan na dawo dan be wuce kwana uku zamu yi ba,zan raka uban gidana unguwa".
Yana fita ta saki ajiyar zuciya,ta dafa gado ta tashi ta kasa tashi.***
"Ba fa za ka zo ka ajiye ni a wannan ƙauyen ka kama hanya ka tafi ba".
"Ni ke da ikon yin duk abin da na ga dama yi Habibtee".
"Ok! Shi ya ba ka damar bin matan da ka ke dan kana head of the family? Idan ka dawo ba ka iske ni ba, mu haɗu kotu dan na gaji da irin wannan zaman da mu ke da kai. Na faɗa ma idan ni ce ban gamsar da kai, ka ƙara aure zan fahimce ka. Amma irin wannan rayuwar ce ba zan yarda da ita ba. Ba zan iya zama da mazinaci ba".
"I've heard enough of it!". Ya daga ma ta hannu.
Ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.
"Dan ka san banda wajen zuwa a ƙasar nan dole ka wulaƙanta ni. Ka sake ni ka ƙi saki na. Ba zan so hankalin iyayena da ƴan uwana ya tashi ba saboda taurin kai irin nawa. Soyayya ta rufe man idanu na kasa gane aibin da Bro ARK ya gano a tattare da kai. I thought that rashin so ne. Haba Hameed! Why all this sudden change?".
"Ki yi haƙuri Habibty, ban san mi ke damuna ba. I'm addicted to it. Ki taya ni da addu'a".
"Meyasa ka boye min tun farko? Ba ka jin kunyar kanka? Idan da ni ce ke bin maza da tuni ka sake ni, da tuni duniya ta ji labarin abin da nike aikatawa. Amma da yake ni mace ce, banda ƴanci zaɓama kaina abinda ya dace da ni, banda ƴancin yin magana. Ni ce mai iya hakuri. Ba ka sani ba cewa da mace da namiji da ke zina da aure duk zunubinmu daya? Allah ne ya haramta ga bayinsa".
Jikinsa yayi sanyi, ya rungume matarsa gam!
"Idan na dawo zamu yi magana. Take care of yourself and Ajwad for me". Ya ba ta peck a kunci ya juya ya tafi.
Tabi Ƙaton enlargement picture dinsu da kallo.
Duk inda ake neman ɗa namiji ya kai Hameed ya kai har ya wuce, sai dai kyan ɗan maciji.
Ta sa hannu ta share hawayen da suka zubo ma ta. Ta cigaba da hiɗimomin gabanta.11:35am
Idan da hawaye na ƙarewa da tuni na Ammah sun ƙare. Kuka take marar sauti, ko'ina jikinta ciwo yake ma ta.
Sallama ta ji daga bakin ƙofar falo, ta amsa saboda dishewar da muryarta ta yi ba'a jin sautin maganar.
"Ammah! Ammah!! Ammah!!!".
Ta bankaɗa labulen, shashsheƙar kukan Ammah ta jiyo daga cikin ɗaki da sauri ta shiga ɗakin hankalinta tashe.
"Ammah miya same ki?".
Shiru ba amsa. Idanunta su ka sauka akan ɗigon jinin da ke kan zanin gadon.
Da sauri ta daga Ammah, wadda ta fasa wani razanannen ihu.
"Ya Allah! Wannan wane irin abu ne haka? Wa ya aikata hakan a gare ki?".
Hawaye suka cika idon Ayeesha, tausayin Ammah ya ratsa kowane sashe na jikinta.
Ta rasa ta ina za ta fara, dan duk jini ne a jikin zanin gadon da jikin Ammah. Ta runtse idanunta ta buɗe.
Cikin azama ta fito tana leƙa inda za ta hango kicin. Can kuwa ta hango shi,gawayi ta gani cikin murhun da ake zuba shi sai risho da ajiye a gefe saman wani katako,yanda za ta kunna dukkansu ba ta sani ba, dan a tarihin rayuwarta ba ta taba amfani da risho ba bare gawayi.
Fita tayi daga gidan,cikin mintuna ƙalilan ta dawo da vacuum flask manya guda biyu cike da ruwan zafi.
Bahon da ta gani a tsakar gida ta shiga da ita banɗaki ta juye ruwan zafin ciki, ta juye sauran a cikin bokitin wanka ta sirka sannan ta fito.
Ita ta taimaka ma Ammah ta gyara kanta bayan ta gasa jikinta da ruwan zafi mai ratsa jiki.
Fayau! Ta ke jin jikinta wanda da kyar take tafiya saboda tsamin da jikinta ya yi.
Zanin gadon Ayeesha ta jika cikin ruwa. "Ammah ina sabulu?".
"Yana nan bayan randa a waje".
Ayeesha ta wanke zanin gadon fes! Ta shanya shi.
Falo ta isko Ammah zaune tana hawaye "Ki yi shiru Ammah, tabbas an zalunce ki. Wannan child abuse ne, kuma it's like a rape case".
Ammah ta yi shiru dan ba ta fahimci abin da Ayeesha ke nufi ba.
"Yanzu muje gidana ki ci abinci, na duba banga abinda za ki ci ba. Kin ɓoye mun wani abu Ammah. Ki dauke ni yayarki ta jini. I'll fight for your right. Kamar yanda na san zan kwato ma Laila. Raina ya ɓaci, a ce be duba ƙanƙantarki ba, dole mu je asibiti a duba lafiyarki. Zai dawo ya iske ni da Daddyn Ajwad zan haɗa shi".
Ammah dai ido ne na ta, ta kasa magana saboda wani irin azababben zafi take ji.
Da kyar su ka isa gidan Ayeesha. Tangamemen gidane ginin zamani wanda harabar gidan ke zagaye da shuke-shuke, daga gefe anyi ma'adanar ajiye motoci (parking shade), sai gazebo da ke zagaye da kujeru hudu da teburi a tsakiya.
Gidan ya matuƙar tsaruwa, duk abin da ake bukata na more rayuwa dai-dai gwargwado akwai shi kamar ba a ƙauye ba.
Ammah tabi falon da kallo, har Ayeesha ta dawo dauke da tray ba ta sani ba.
Ta shimfiɗa ma ta food mat "Sauko ki ci abinci".
Ta dan dafe kujerar ta zauna, shayi ne mai kauri ta haɗa ma ta da toasted bread, sai farfesun kaji (chicken pepper soup).
Tayi serving Ammah.
Wayarta ce kirar NEXUS 6P ta hau rurin neman agaji.
"Hello Amour! ".
" ok! Har kun isa Katsinar?".
"Allah shi huta gajiya. Promise me you won't look at any babe".
"That's my love. Take care of yourself please ".
" I feel your soft kisses".
Ta ajiye wayar ta na murmushi.
Ammah tana ta kallonta.
"Kun birgeni Aunty Ayeesha. Sai na ji dama ni ce ke. Ina son zama yar gayu in yi ilimi".
"Kar ki roki irin tawa rayuwar Ammah. Ki roki wacce ta fi tawa wadda za ta dace dake. Duk macen da kika gani a gidan aurenta ita kadai ta san irin ƙalubalen da take fuskanta. Na wata yafi na wata kowa da irin matsalar shi. Idan na fada ma ki tawa sai kin yi mamaki, amma na fi jin tausayinki sama da ni. At this age of yours kamata yayi a ce kina makaranta ba gidan miji ba, lalura ɗa namiji ba ki isa daukarta ba. Na san ba ki wuce tsarar Laila ba".
Murmushin ƙarfin hali ta yi "Yanzu Aunty kema har matsalar kike fuskanta a gun mijinki?".
"Kwarai kuwa Ammah! Ai bari ki ji KOWANE TSUNTSU KUKAN GIDANSU YAKE. Matsala ta tasha bambam da irin taki".
"Toh Aunty kiyi ta addu'a mana, kina tashi da dare kina gaya ma Allah. Malaminmu a islamiyya ya ce idan kana fama da matsala ka kai kukanka wajen Allah zai yaye ma ka. Idan har ba'a yaye ma ka ba to tabbas wata ƙaddara ce, sai kayi ta addu'a Allah Ya baka Ikon cinye ta. Shiyasa ko na damu da na tuna ina addu'a sai inji sanyi na san wata rana Allah zai yaye mun".
Rungume ta Ayeesha ta yi "Thank you Ammah. Zan bi shawararki kuwa na san ba zan taɓe ba".
Sai da ta tabbatar Ammah ta koshi, ta shirya suka fita dan zuwa asibiti.
***
Da kwatancen Ammah su ka isa Bakori. Comprehensive Health Care (CHC) suka je, inda suka siya kati sun yi sa'a consultant na nan.
Ayeesha ta ma shi duk wani bayanin abinda ya faru.
Fada ya dinga yi "ba zan duba ta ba sai azzalumin mijinta ya zo, kashe ta yake son yi ne?".
"Doctor ka yi haƙuri ka duba lafiyarta itace abar damuwa".
Salatin da Nurse keyi ya tada hankalin Ayeesha.
" Ai wannan sai anyi ma ta dinki".
Salati da sallalami kawai Ayeesha ke yi, hawaye na ta zarya a kan fuskarta.
"Allah ka taimaki baiwarka Ammah".Ammah ta sha kuka har da majina jaje-jaje a hancinta saboda azabar da tasha wajen dinkin da aka yi ma ta.
Duk wani abu da ake buƙata Ayeesha ta yi komi.
Likita kuwa yai ta fada kamar ya ari baki.
Yana rubuta magungunan da za a sayo ma Ammah.
"Gaskiya kunyi wauta ba karama ba a ce kun aurar da yarinya haka da ba ta da ƙarfin daukar lalurar aure. Bayan ma haka da yake mijinta Be da imani yayi ma ta mummunan aiki haka kamar wadda aka yi ma fyade. Duk wanda ya gani fyade zai ce an yi ma ta".
Ayeesha ta yi shiru tana tunanin irin hukuncin da za ta yanke.
Bayan likita ya sallame su suka fito daga asibtin. Ayeesha na tuki, Ajwad na gefenta, Ammah na baya.
"Ammah kince ke yar Bakori ce, ki mun kwatancen gidanku in kai ki iyayenki su san halin da kike ciki. Ba zai yiwu kiyi ta zama haka ba. Idan ba gawarki su ke son dauka ba watarana. This is domestic violence da mafi yawan maza ke yi ma mata. A hana ki abinci,a dukeki sannan a far ma ki da rashin yardarki. Ammah duk kin haɗa wadannan abubuwan a yan ƙananan shekarunki. Dole a dau mataki".
"Aunty na gode da taimakonki a gare ni, Allah shi saka maki da mafificin alheri. Amma ba zan iya zuwa gidanmu ba koda yanka ni Salisu ke yi, hankalin su Gwaggo tashi zayyi. Dan Allah ki rufa man asiri kar ki faɗi ma kowa halin da nake ciki. Daga ke sai Sa'a ku ka san halin Salisu ita ma nayi amanna ba za ta faɗi ba".
"Ammah wace irin zuciya ce da ke har a cuce ki ki gaza daukar mataki. Kar ki ga ke yarinya ce ba ki da baki. Daga randa aka yi maki aure kina da yanci kamar su Gwaggo. Kina da hankali har aka ga zaki iya kula da wani. Idan har ba'a taka ma Salisu birki ba to ki tabbata haka zai cigaba. Wani abin da kanmu muke kwatar ma kanmu ƴanci".
"Matan birni ke kwatar yancinsu idan aka zalunce su, mu kuwa nan ƙauye mace ba ta da wannan ƴancin. Na bar ma Allah komi shi zai saka man".
"Dadinki daya kina da ilimin addini dai-dai gwargwado. Shiyasa kika fita daban".
Suna ta tattaunawa har su ka iso karofi duk da hanyar ba ta da kyau sosai.
" Gidana za ki zauna har mijinki ya dawo".
Ba ta musa ba. Duk da tana tsoron abin da zai je ya dawo.
BAYAN KWANA BIYU"Ammah! Wai gidan ubanwa kika shige kina ji ina kwala ma ki kira".
Kafa yasa ya harbi ƙofar ya ji ta ƙiƙui.
"Kutimesi! Kar dai a ce guduwa yarinyar nan tayi? ".
Yayi kwafa, yasa makulli ya buɗe ƙofar falon.
Yana shiga ya jiyo sallamar mutane, ya fito yana amsawa.
Turus! Ya tsaya yana mamakin ganin fuskokinsu.MashaaAllah! By the way we're now in chapter 15.. The journey of a thousand miles start with a step!
A beg you in the name of God! Don't hesitate to send your suggestions, corrections and advice on your view with #MADUBI we're like one family.
Indo A'e lobiyu da yawa.ayeeshasadeeq2010@gmail.com
chuchungaye.wordpress.com
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...