TA FARU TA KARE

2.4K 223 37
                                    

MADUBI
©AYEESH CHUCHU
BABI NA SHA BIYU
(NWA)
I dedicated this chappy to my lovey-dovies (fans) 😘. Without "U" Chuchu couldn't write 📝 a word, it's Ur courage. I really appreciate it. I love 😍 U to za moon 🌑 & back.


Much love 😍 from the heart ♥ that cares.
Sit back and sip Ur Zobo 🍻 ehrrrn.

TA FARU TA KARE

"Yaron nan Salisu ya yi ƙokari, duk faɗin KAROFI babu wanda ya taɓa yin lefe irin nasa, ɗan gata ne wajen mahaifiyarsa ganin shi kadai ne namiji cikin ƴaƴanta,ma fi soyuwa a cikin zuciyarta. Na tabbatar zai riƙe Ammah bisa ga amana".
Cewar Innani kenan a sa'ilin da take duba lefen da aka kawo ma Ammah.
Gwaggo da ta gaza haƙuri ta ce "Innani yaron nan da kike magana ni shaida ce sam! Tarbiyyarsa na ga gibi. Duk inda direban babban mota yake, kadan ne na kwarai cikinsu. Tausayin irin rayuwar da Ammah za ta faɗa nike".
"Dakata! Halima, na lura tun da aka fara maganar auren nan ba ki farin ciki da shi. Shin ke ki ka haifi Ammah da za ki ta zaƙalƙalewa acikin al'amuranta? Aure ba fashi".
Daga Gwaggo har Inna ba wanda ya sake magana, shiru su ka yi, dan basu isa su maida ma Innani magana ba.
Ammah da ke ɗaki tana saurarensu, hawayenta su ka cigaba da tsiyaya.
Muryar Sa'a ta tsinkaya ta na gaida su Gwaggo.
"Wacece wannan kamar Sa'a?".
"Ni ce Innani ".
" Ikon Allah! Haka ki ka gamɓashe kamar wata uwar mata. Ga ƴar uwarki nan ana niyyar wanketa".
Sa'a ba tace komi ba, ta shige ɗakin Gwaggo.
"Kiyi hakuri da maganar Innani".
"Kayya! Ba komi Ammah. Yanzu dai yaushe angwayen za su kawo kuɗin sitting?".
"Ke ni ban sani ba, ki kyale ni".
"Ba kyale ki zanyi ba, Kinga dai dole kiyi kitso da kunshi. Kuma kawayena da na gayyato za su zo".
"Ni fa ba abinda zanyi".
"Karya ki ke yarinya, bari Inyi magana da Gwaggo. Daga nan in wuce in karɓo ma ki dinkunanki wajen Kabiru".
Daga haka ta fita daga dakin tabar Ammah da ƙunar zuci.
Sa'a ta sami Gwaggo suka tattauna duk yanda za su tsara komi, sannan ta wuce wajen tela.

***
"MashaaAllah! Wannan kyau haka Ammah? Lallai Salisu yayi dace".
"Mtsewwwww! Ke dai ki ka sani".
"ko kuma kika sani ba, an jima kadan mun kai ki gidansa, sai mu ga ta tsiya. Awanni biyu suka rage a daura aure kin zama ta sa halak malak".
Ba zato ba tsammani Ammah ta rushe da kuka.
Duk sai jikin Sa'a yayi sanyi.
"Ammah! Kin wuce irin wannan yanayin yanzu, aure fa za ki yi. Wata rana uwa za ki zama, ki sa ma zuciyarki salama ki yarda da ƙaddarar da ta hau ki. Addu'a ce za ki duƙufa yi". Nan Sa'a ta cigaba da ba Ammah baki, har ta sauko.
Gwaggo ce ta leƙo ɗakin "Ammah fito ɗakin nan ki shirya".
Ba ta musa ba, ta fito tana jan ƙafa.
"Amshi kindirmon nan ki shafe jikinki ds ya sha iska ki mun magana".
"Gwaggo kullum sai na shafa, ni na gaji". Ta faɗa a shagwaɓe.
"Maganin sanyi ne, ba za ki riƙa jin sanyi da ciwon ƙasusuwa ba. Kuma ba ki ga fatarki tayi kyau da kyalli ba?".
Ta gyada kai, ta wuce banɗaki.

Bayan ta fito wanka, tana goge jikinta, Sa'a ta miƙo ma ta wata kwalba.
"Murza wannan kowane lungu da saƙo na jikinki".
"Ku ji man Sa'a kamar wata Innata".
Ta dauki kayan da za ta sa ta fita.
Riga da siket na leshi (lace) na ta saka mai ruwan turowar hoda (fuchsia) da kalar ruwan bula (blue). Duk da fuskantar babu kwalliya, hakan be hanata yin kyau ba. Saboda sabon kitson da ke kanta ya ƙara fito da ita.
"Amarya! Amarya! Amarya ba ta laifi ko ta kashe ɗan masu gida".
" Sai dai in ba ta kashe ɗin ba". Faɗin Umaimah ƙawar Ammah a islamiyya.
Sa'a ta jawo rumbum kwalliya (make-up kit) da aka sako ma Ammah cikin kayan lefe. Ta hau Murza ma Ammah fuska da kayan shafar dai-dai da iyawarta.
"Inyeee! Ka ga Sa'a ƴan gayu. Ai shiyasa na ke son bodin (boarding) saboda koyon abubuwan zamani. Bare makarantarsu Sa'a ta yan gayu".
Murmushi Sa'a ta yi ta cigaba da yi ma Ammah kwalliya. Kafin a ce mi amarya ta fito ras!
"Idan ango ya gan ki sai ya ruɗe".
Guɗa su ka ji "Ayyiyiriririri! An daura auren Halimatu da Salisu". Nan fa guɗa ta buɗe cikin mata, kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Tagumi Ammah tayi, hawaye su ka silalo daga kwarmin idanunta. Zuciyarta ta tsananta faɗuwa.
"Haba Ammah! Miye na kuka kuma? So kike kwalliyar fuskarki ta goge?".
Shiru ta yi, tunanin abubuwa da dama suka zo ma ta a kwanyarta.
"Sa'a ki duba akwatin da ke ƙarƙashin gadon Gwaggo, za ki ga wannan saƙon na Ya MK ki saka man cikin kayana". Daga haka ta cigaba da kukanta.

MADUBI Where stories live. Discover now