MADUBI
AYEESH CHUCHU
BABI NA ASHIRIN
KOWA YA TUNA BARA...
Alhamdulillah we've reach 1k votes. Love you to the moon and back.Da kwatance-kwatance aka kai su gidan Malam Ibrahim. Motoci ukun nan suka yi parking a kofar gidan.
"Calm down! Babu abinda zai faru sai alkhairi". Ya dafa kafadarta.
Sai da ya fito sannan ya buɗe ma ta ita ma ta fito.
Ganin iyayensu sun fito ya sa suma duk su ka fito.
Alhaji Kabir ne a gaba sai Mami da sauran yaransu. Da kyar take tafiya har suka shiga tsakar gidan bayan Mami tayi sallama.
Ƙarar faɗuwar abu suka ji, ido biyu Mami ta yi da Malam Ibrahim.
Duk canzawar da yar uwarshi za ta yi ba zai kasa gane ta ba.
"Yaya ke ce?".
"Ni ce Ibrahim".
Sai kuma kuka ya kwace ma ta.
"Halima fito da tabarmi mun yi baƙi".
Gwaggo ta fito, ta bi su da kallo bayan sun gaisa.
Farin cikin da ta gani a fuskar mijinta ya gaza ɓoyewa.
" Innani ta tashi?".
"Eh abinci take ci. Sauri nake in wuce asibiti wajen Ammah sai Mairo ta dawo".
"Taimaka ma Innani ta fito".
Mami da tunda ta zauna kanta na a ƙasa ta kasa haɗa idanu da ɗan uwanta. Kamanninta sak! Da shi,sai dai jikin hutu da za ta nuna masa.
Gwaggo ta fito da Innani da ke takawa da kyar.
"Ibrahim lafiya kuwa? Na ji zuciyata na harbawa da ƙarfi kar dai Ammah ce ta rasu".
"A'a Innani zauna dai kiga abin al'ajabi".
Da taimakon Gwaggo ta zauna tare da kishingiɗa.
Mami ta taso daga mazauninta ta iso gaban Innani idanunta sharkaf da hawaye.
Ta duƙa gaban Innani.
"Innani ki gafarce ni".
Cikin sauri ta kai duba gabanta.
Tayi saurin rufewa, ta sake buɗewa.
"Ibrahim na gaji da mafarkin Halima da nake, kaga yau ga ta har a gabana".
"Innani ba mafarki ki ke ba Halimarki ce".
"Innani Yaya ce ta dawo".
Kuka Innani ta barke da shi.
"Ashe da rabon za mu gana? Ina kika shige duk tsayin shekarun nan ba ki waiwayo gida ba? Laifina ne da ban kore ki ba. Ki yafe ni".
"Ni zan nemi gafararki Innani, ke ce uwa duk abin da kika yi dai-dai ne. Ko ni ce hakan ya faru da bani da zabin da ya wuce hakan".
"Yanzu wadannan duk yaranki ne?".
" Eh Innani".
"Ba ni labarin abin da ya faru".
* * *
SHEKARU TALATIN DA BIYAR DA SUKA WUCE"Ranar wata talata da dare mun fito daga ɗakunan kwanan ɗalibai da dare, muna gab da fara zana jarabawarmu ta ƙarshe, ni da ƙawayena muka sami waje cikin ajujuwan, mu ka rarrabu don mu sami damar yin karatun ba tare da surutu ya hana mu ba.
Muna tsaka da karatu dahu ya mamaye ajin da na ke karatu, zan fasa ihu na ji an rufe man baki. Ina turjewa aka dauke ni cak sai bayan aji, anan maƙetacin mutumin ya min fyade. Na gane shi malaminmu ne.
Ya ja kunne na akan idan na faɗi wani abu sai ya kashe ni. A daren ranar nayi kuka na kai ma Allah kukana.
Kwatsam! Muna cikin zana jarrabawa aka ce Malamin nan ya yi hatsari ya samu tabin kwakwalwa.
Bayan mun gama jarabawa na dawo gida, alamomin ciki suka fara bayyana a tattare da ni, na yi kuka har nagode ma Allah.
Har a lokacin ba ki sani ba, har jarabawarmu ta fito na je na karbo tare da sakamakon mai kyau.
Yunwar da na ci a ranar ita ta sa na galabaita har juwa ta kwashe ni, na faɗi a tsakar gida.
A ranar ne asiri na ya tuno bayan kin kai ni asibiti. Kina kuka ina kuka har muka iso gida nan Karofi.
Anan ne kika furta "Halima ki tafi bani kaunar ganinki, bazan iya zama da ɗiyar cikina dauke da cikin shage ba. In ce ma al'umma mi? Diyata tayi cikin shege?".
Ibrahim na kuka kika kwaso kayana kika wurgo tsakar gida. Ya kwaso su ya maida kika sake watsar da su.
Ibrahim ya ce "Yaya zan bi ki inda za ki".
Da kuka muka rabu kika ingiza ni waje tare da rufe kofa.
Daga nan tasha na nufa ban san inda zani ba, ina kuka har muka isa Funtua,da kyar ma su mota suka haƙura dan banda kuɗin da zan ba su.
Na taho zan tsallaka titi da ban san ina zani ba, mota ta kaɗeni. Ba kowa ba ne sai Alhaji Kabir, shi ya taimake ni ya kai ni asibiti, a sanadiyyar hatsarin da nayi cikin ya zube.
Bayan na ji sauki yaga da ya mun maganar gida zanta kuka. Dole ta sa na ba shi labarina.
Ya matuƙar tausaya mun, ya ce zai maidoni gida nace ban zuwa. Ni duniya zan shiga, ganin haka ya tafi da ni Kano, ya yi ma Hajja mariƙiyarshi bayanin cewa ni marainiya ce. Da kyar Hajja ta yarda.
Dama yana da da da Hashim da bai fi watanni biyu ba a duniya wajen haihuwa mahaifiyarsa ta rasu, sunanta Aisha.
Watana biyar a Kano Alhaji ya nuna sha'awar aurena duk irin yanda Hajja ta ƙi sai da aka yi auren nan.
Aurenmu da shekara ɗaya da rabi na haifi Sadiq, suka taso kusan kai daya da Hashim. Na rike shi tankar ɗan cikina wanda har yanzu ya san babu wariya. Ta dalilin Hajja ya san ni ba mahaifiyarsa ba ce.
Bayan shekara uku na haifi Abdurrahman. Be shekara ba Alhaji ya tashi tafiya yin wani course a Landan (London), mu ka daga tare da yarana uku mu ka tafi can.
Shekara hudu bayan haihuwar ARK na haifi Ayeeesha wadda ta ci sunan marigayiya, naso boye sunan kwarai Alhaji ya hana.
Na dade ban haihu ba har sai da Ayeeesha ta shiga aji ɗaya na makarantar gaba da sakandire anan na haifi Laila. Shekaru goma tsakaninsu.
Dukkansu anan Landan suka yi karatunsu na addini da na boko.
Nima anan na cigaba da karatu na inda na kai matsayin ferfesa. Anan jami'ar Oxford nayi karatuna gaba daya anan kuma na ke koyarwa a sashen na'ura mai kwakwalwa.
Nayi rubuce-rubuce da dama wadanda har nan Nijeriya an kawo su ga dalibai.
Na samu lambobin yabo da dama daga kungiyoyi ma bambamta. Duk da ina Landan hakan be hanani tura taimakona ba.
Bayan Ayeeesha ta kammala digiri dinta ta dawo wajen Hajja a nan tayi bautar kasa, bayan ta dawo ne aka sa ranar aurenta da Hameed ɗane ga abokin Alhaji, duk da ARK ya nuna rashin amincewarsa, kuma dai suna son junansu aka yi bikin tare da na Hashim.
Kano muka dawo aka yi biki, sannan muka koma.
Wannan yaron shi ne Ajwad ɗan Ayeeesha, sai matar Hashim Fatima da ke dauke da ciki Shiyasa ma ba'a taho da ita ba.
Zuwanmu bikinsu Hashim na sa aka bincika mun halin da kuke ciki aka tabbatar mun da cewa kana Bakori. Innani na nan Karofi.
Yanzu haka dai dawowarmu kenan daga Landan muka shirya wannan tafiyar tunda mun dawo gida. Kin ji labarina bayan tafiyata Innani.
Alhaji shi ya zamar mun uwa da uba, ya bani duk wani gata".
Innani kuka take ba ƙaƙƙautawa.
"Na cuce ki Halima yanzu da ba dan kin fada hannun kwarai ba da shi kenan. Allah shi saka ma Alhaji da mafificin alheri. Ki yafe ni Halima".
"Innani nice zan roƙi gafarki".
Nan suka yafi juna.
"Yaya yanzu Wadannnan duk iyalanki ne?".
"Kwarai kuwa, ina naka?".
"Duk suna makaranta sai Ammah da ke asibiti".
"Ban labari in ji".
"Bayan tafiyar ki na dan tasa, ina sana'ar saida hatsi ina samun rufin asiri dai-dai gwargwado. Na auri Halima takwararki muka dawo Bakori da zama. Shekarar mu goma a tare ba haihuwa, Innani ta matsa na auro Mairo inda anan ta haifi Ammah, Mubarak, Yusuf da Abdullahi. A dalilin wannan abu da ya faru Innani ta tsani Karatun boko. Ko su mazan da kyar Innani ta bari.
Duk irin son da Ammah ke ma karatu dole ta haƙura, na Islamiyya kadai ta yi, Innani ta kawo miji aka yi mata aure,saboda bata son tayi girman da za ta dauko magana".
Nan ya basu labarin auren Ammah har zuwa yanzu da take kwance a gadon asibiti.
"Yanzu a dalilina aka hana Ammah ƴancinta? Duk a dalilin laifin mutum ɗaya. Kaico Nah".
"Ba laifinki ba ne ba Halima haka Allah ya ƙaddaro ma ta. Ta kuma yi biyayya duk da irin son Karatun da take".
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Mami itace Ammah da nake baku labarin idan mun zo zan zo ganinta".
"Kar dai ke ce Aunty Ayeeesha da Ammah ke yawan fadi har muka taba gaisawa?".
"Ni ce Gwaggo. Allah sarki Ammah ashe yar uwata ce shiyasa na ji ƙaunarta a ruhina".
"Jini daya ba wasa ba ai". Fadin Mami.
"Ku tashi mu tafi a duba lafiyar wannan baiwar Allah ". Fadin Alhaji Kabir.
Idanun Laila sunyi jajir! Ta sha kuka.
Muryarta a dishe ta ce" Yanzu Mami yarinya kamar ni sai ayi mun aure?". Ta fashe da kuka.
"Na tausaya ma ta, dole Aunty Ayeeesha ta taimaka ma ta. She really need help, at her stage she's infected with vvf. So disgusting. I hate that man". "Gaskiya Mami ba za a bar Salisu haka ba dole abi ma Ammah hakkinta. Irinsu idan ana kyalesu ba karami ta'adi za su yi a al'umma ba". Fadin Ya Diq
"a'a ku bar shi, duniya ce ta ishi kowa riga da wando. Mun bar shi da Allah".
Daga haka suka tashi don tafiya asibiti.* * *
GENERAL HOSPITAL FUNTUAManage with this one, the chapter is kinda boring wolla. Lol
Writing all this tarihi tarihi is not easy, i hate writing it. And I've to write some missing part for you guys.
Please bear with me.
Don't forget to
Vote
Comment
Share
Recommend
Thank you all for all your love and support.Indo A'i
www.chuchungaye.wordpress.com
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...