MADUBI
AYEESH CHUCHU"She is black she's proud and she knows it, she's cool and everybody likes it. She's bold and she's very very humble, she's strong and can never never fumble, she's courageous".
Black is beautiful by FlavorYA BAYYANA
"Ya Salam! Ya ARK as Abdul Kabir. Ina hankalina ya tafi ne? What the heck? Is he fooling me? Ya Allah! Mi na yi kenan?".
Zuciyarta ce ke bugawa da ƙarfi ta rasa abinda ke ma ta dadi.
Ta ƙara kai duba ga hoton ta tabbatar da shi ne, hoton da aka dauka ranar da su ka yi meeting.
Sannan kuma Account dinsa ne da su ke chatting wanda ba ta taɓa zaton shi ne ba.
Sai yanzu take tuno tarihinsa da ya ba ta a takaice, ina kwakwalwarta da tunaninta suka tafi? Ta kasa gane cewa Ya ARK ne ABDURRAHMAN KABIR.
"Yes! Abdul Kabir. Yaa Allah save me from his tricky game".
Cikin sauri ta danna kan sunanshi dan duba furofayil ɗinsa.
Abdul Kabir (ARK) ta gani ƙuru-ƙuru. Hoton furofayil ɗinsa hoton takalmi ne, ta bi duk wani bayani (About Me) nan ta ƙara tabbatar da shi ne, ta shiga album ɗinsa nan ta ga hotunan sa, a gida, a wajen aiki, wajen cin abinci ne, sai ga hotunan sa da Khalifa."Wai mi ya dauke mun hankali da har ban taɓa tunanin in duba hotunan sa ba".
Ta dafe kanta da ke sarawa, komi ya kwance ma ta. Sunayen Allah ta cigaba da ambato.
Har ta danna lambar Laila ta fasa, za ta kira Sa'a ta datse.
Ta gama karanto sunayen Allah ta danna lambobinsa. Ya na dauka da kyar ta maida ma sa sallamarsa sanin muhimmancin haka.
"Abdul Kabir well you really tried in fooling me. Allah ya sa na gane kai ne Ya ARK. Why? Mina yi ma ka da ka dauki hanyar tozarta ni? Ka boye identity ɗinka a gare ni, asirin ka ya tuno. I hate you ".
Ta datse kiran tare da wurgi da wayar, hawaye na zuba daga idanunta.
"Ya cuce ni, he makes me fall for him. Allah ka saka mun".
Ita kadai ke ta suratanta. Ba ta iya bacci a daren ba, salloli ta yi ta jerowa, har ta ji ƙafafunta na zafi sannan ta zauna ta fara karatun Alqur'ani. Ta gama ta hau salatin annabi SAW, tare da istighfari.
Ta idar ta ðaga hannayenta sama ta roƙon Allah ya kawo ma ta mafita a rayuwarta.***
Tunda ya ajiye wayar hankalinsa a tashe ya ke. Ya rasa ina zai tsoma ya rayuwarsa.
Daukar wayar ya yi, ya latsa lambar Mustapha sai da ya kira kusan sau biyu a na ukun ne ya dauka.
"Haba Musty 2 missed calls, tunda kaga na kira a karo na biyu kasan important issue ne".
"Hala ba ka san lokaci ba ne ba?".
"Miya ruwana da lokaci, duk kai ka ja mun, nace tun farko na faɗa ma Ammah cewa ni ce, ka hana mu wani ƙara sanin juna ga shi nan she finds it out by herself. Idan ka ji maganar da yarinyar nan ta faɗa mun ba'a magana".
"Ya Rabbi! Wai ARK Kai ƙaramin yaro ne? Try to sort out things by yourself. Ni yanzu ban san ya zan yi da kai ba. You're fully grown and matured. Ka warware ƙananan matsalolinka da kanka, waɗanda na san ba ka iyawa sai muyi magana".
"Haka ma za ka ce ko? Anyway zan warware matsaloli na da kai and you'll be surprise".
Zuciya a wuya ya kashe wayar. Ya dafe kansa, yana tunanin mafita.
"Ni fa ba sonta na ke ba, i just like her nothing else ".
Ya gama duk wani tunanin shi, murmushi ya yi.
Bandaki ya shiga ya yo alwala, haka ya raya daren nan ba tare da ya runtse ba yana kai kukansa ga Allah mai kowa da komai.
***
Tunda ta koma bacci ba ta farka ba sai wajajen goma ta wuce. Wanka ta yi, idanunta duk sun zurma, ƙasan idanun sun danyi baƙi. Concealer ta shafa ma kasan idanunta dan ya daidaita da sauran fuskarta. Ta zizara kwalli, ba ta ko tsaya shafa hoda ba, turare kadai ta fesa.
Doguwar riga ta sa ƙirar Bahrain, mai ruwan goro da golden brown. Hula ta sa ma kanta tare da cusa gashinta cikin hular.
Silifas ne ma su taushi a ƙafarta, ta corridor ta bi da zai sada ta da kicin, ta shiga Inna Hindu na shirin daura abincin rana da yake 11 har ta yi.
Su ka gaisa, tare yi ma ta bangajiyar hanya.
"Mi ku ka dafa ne?".
"Ga kunun gyada nan da doya da kwai, sai farfesun kayan ciki".
"Bani kunun gyadar da farfesun. Kinga wani abu cikin roba da na sa a fridge?".
"Bari in zuba ma ki. Eh na gani mi ake da shi ne?".
"Halal Kitchen Marinade Sauce kenan, ana shafawa kaza, kifi duk kafin a gasa su. Sannan idan za'a yi sandwich da Shawarma da burger ana amfani da shi ma. Abubuwa da dama dai ya dauke da sinadarai ma su matukar amfani a jiki. Ki dai gwada za ki ban labari ".
" Har kin sa na ji kazar da Hajiya tace a gasa ma ta in sa shi".
"Ki gwada dai".
Ta ja kujera ta zauna ta na kalacinta. Bayan ta idar ne "Bari in je in gaida Mami da Abba sai in dawo in taya ki aikin".
Ta fita ta ƙofar da za ta sada ta da babban falon ƙasa ba kowa sai talabijin da ke aiki. Ƙamshin turaren da ta ji a falon ya sa ta tunanin ta san mai kamshin nan. Ganin ba kowa yasa ba ta kawo ma ranta komi ba.
Sama ta hau dan tabbatar dai Mami ta tashi dan ba ta bacci. Ta leka falo ba ta nan, tayi sallama shiru.
Hakan ya nuna ma ta tana gun Abba.
Da sallama ta shiga falon Abba.
Turus! Ta tsaya ganinsa zaune a ƙasan kafet mai taushi na alfarma yana gefen Abba.
Su ka haɗa idanu ta galla ma sa harara. Murmushi ya yi tare da kanne ma ta ido.
A hankali ta ƙaraso falon ta gaida Abba da Mami cikin ladabi da girmamawa.
"Yauwa yanzu na ke niyyar kiranki, na leƙa dazu naga ba ki tashi ba. Na san gajiyar hanya ce".
Ta murmusa.
"Ammah samu wuri ki zauna".
Ta zauna gefen Mami kanta a ƙasa.
"Abdurrahman ne ya zo mana da wata magana mai muhimmanci, duk da munyi matukar farinciki. Amma hakan ba zai hana mu ji ta bakin ki ba.
Yanzu ki na da dama da ƴancin zabar abokin rayuwarki. Abdurrahman ya shaida mana cewa kun aminta da juna,za ku zauna a inuwa ɗaya bisa umarnin Allah da ma'aikinsa, shi ne maƙasuɗin zuwansa dan ya gabatar da maganar ga manya".
Gabanta ne yayi mugun faɗuwa, ta daga kai ta kalli Ya ARK, murmushin mugunta ya sakar ma ta.
"Ammah idan har ARK tilasta ma ki ya yi, kar ki ji kunya ki sanar. Aure ana gina shi ne bisa so da kaunar juna da aminci. Idan har ba ki amince ba ki yi magana ". Faɗin Mami kenan da sam ba ta yarda da Ya ARK ba.
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...