MADUBI
©AYEESH CHUCHU"Abinda yake raina zani fitar in huce takaici. Soyayyarki a raina zani aje ba za ta fice ba. Alamar tambaya tana ga mai yawaita tunani musamman ya shiga halin soyayyar zamani.."
~By Abdul D-OneBABI NA TALATIN (B)
Bonus Chapter
Ta cigaba da karanta saƙon yafi a ƙirga. Sai murmushi take yi.
"Nima na yi tafiya ne, i slept early. Thank you ".
Ba'a yi minti ɗaya ba sai ga reply ɗinshi.
"Har kin farka kenan?Ba kyau chatting gari be waye ba".
"Saboda mi? Ya gajiyar hanya?".
"Saboda mutanen ɓoye. Alhamdulillah ".
" Ni na fi ƙarfinsu saboda ina da yaƙinin Allah ba zai bari su cutar da ni ba".
"I like your confidence girl".
"I'm not a girl. Call me Woman".
"Ok! Uwar mata".
"Ya Abdul you're wicked. I'm not that kind old".
"Yaushe kuma na zama yayanki?".
"Saboda na san ko da shekara ɗaya ka girme ni".
"Ku matan nan wayaun ku yayi yawa. Daga yaya sai a yaye ka".
"Hahaaa! Kai kuma duk wayaunka sai ka tsaya su yaye ka".
"Eh mana idan aka yi katari da mai wayau irinki".
"Ai ni ɗin ba ta yau ba ce ".
" Nace uwar mata kin fusata. Gashi nan kin faɗa da bakinki".
"LWKD 😂.. Ya Abdul ba kyau chatting gari be waye ba. Allah idan aunty ta kama ka you're in hot soup. Ina gefe ba ruwana".
"Zan faɗa ma ta ƙanwarta ce mai surutun tsiya ta tsaida ni".
"Ni dai ba ruwana".
"Korata ki ke koh?".
"A'a naga dai cancantar hakan ne".
"Ok!yayi".
"Ba dai fushi ka yi ba?".Be maido ma ta da amsa ba, kuma ga alamar ya karanta saƙon.
Ganin haka ta sauka daga Facebook ta leƙa sauran kafafe.
Ta na nan har aka kira sallar asuba, tayi raka'atanil fajr,ta jira aka tada sallah.
Bayan ta idar,ta yi azkar ɗinta, tare da karatun Alqur'ani. Ta tada Amaal dake ta bacci, tayi ma ta wanka ta sa tayi alwala, suka fito ta shafa ma ta mai.
"Toh yi sallah".
Haka ta dabura sallarta.
"Aunty Ammah na iyar".
"Good girl. Je ki dauko kayan makarantarki".
Ta ruga da gudu.
Ammah ta linke daddumar, ta fita. Kicin ta isko Ladidiya na faman haɗa kalaci. Nan ta taya ta ta ƙarasa. Su ka jera a tebur.
Ta koma ɗaki tayi wanka, ba ta wani tsaya shafe-shafe ba, iyaka turare da ta shafa ta fesa na fesawa. Ta sanya doguwar rigar bou-bou, ta yafa mayafi da ya shiga da irin kayan.
Ta iske har su Ajwad sun gama kalaci, Aunty Ayeesha na goge ma Hameed baki.
Ya bata sumba a goshi. Ta gaida su.
"Aunty Ammah good morning ".
" Morning good boy. Sai school koh?".
Ya gyada ma ta kai.
Aunty Ayeesha ta dauki jakar mijinta ta rataya ta kama hannun Amaal, su ka fita.
Sai da tabbatar sun tafi sannan ta shigo ciki.
Ammah ta kai chocolate chip waffles a bakinta.
"Gaskiya Ladidiya ta kware a girki. Kin ji kunne na kamar ya tsinke".
"Ai ta yi catering School kafin aurenta ya mutu, Iyayenta suka koreta shi ne ta taho Abuja aikatau".
"Ooh ni Halimatu. Wannan wace irin rayuwa ce?".
"Abin da ban tausayi, mugun mijin ta haɗu da shi. Ta ce bugu, zagi ba wanda be ma ta. Abu kadan za ta yi ya hau ta da bugu. Akwai ranar da sai da jikinta ya farfashe da bulala,ta samu miscarriage.
Ta dau kudinshi ta je asibiti yana dawowa ya sake ta. Ta je gidansu Iyayenta suka ce su ba zasu iya jigilarta ba, ga ta ga ƙannenta. Dammi za ta kashe aurenta, dan haka zawarci ba a gidansu ba. Nan fa uban ya kore ta.
Shine fa da taimakon wata mata ta taho nan Abuja. Shekarar huɗu cikin bautar aure cikin yanayi na wahala, duk cikin da ta samu wahala ke sa shi zubewa".
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Na tausaya ma ta, baiwar Allah. Kin san ina tunanin yin rijista da Cooperate Affairs Commission ɗan mata da ƙananan yara da ke fuskantar matsala irin haka. Har da irin issues ɗina".
"MashaaAllah! Gaskiya kinyi tunani da kin taimaka. Na san Mami da Abba za su yi supporting dinki. Ga kuma manyan Brothers Ya Hashim, Ya Deeq ga Ya ARK tunda shi yafi sanin harkar ma, yana da Charity Foundation".
"Ya ARK ɗin? Uhmmm ni fa ba wai muna shiri ba ne. Ya cika Ego da yawa".
"Ba ki fahimce shi bane. Maza ba za ki raba su da wannan Ego na su ba,ko emotions na su ba kasafai ki ke fahimta ba, bare irin su Ya ARK zanga matarshi, yana da dadin sha'ani. Ke da Layla ne ku ka ma sa fassara maras ƴanci. He's a nice person. Da yake yana zuwa gidan nan sosai saboda su Ajwad, muna fira akan al'amura da dama".
"Ni tsoron magana ma nake da shi. Amma idan suna fira da Khalifa sai ki ce ba shi bane".
"Ai in dai wajen yara ne abin ba dama".
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...