BABI NA HUDU

2.4K 313 21
                                    

MADUBI
©AYEESH CHUCHU
BABI NA HUDU

Mukhtaar ya durkusa har kasa ya gaida Gwaggo.
"Na ji abinda ke tafe da kai yaro ban ki ta taka ba, ka ga Malam baya son karatun nan na boko,kannenta maza ma da yaya ya amince, ko na gaya ma sa ba amincewa zayyi ba".
"Da hakan Gwaggo, nayi tunanin hakan ne dan cigaban ita Ammah, tana da kwazo sosai a islamiyya. Ta dalilin hakan naga ya dace a ce ita ma ta san wani abu daga cikin boko yanda za ta iya rubutu da karatu itama ba'a barta a baya ba".
"Ai gaskiya na ji dadin bayanin nan naka, wani hanzari ba gudu ba,kai Dan wane gida ne?".
"Gwaggo ni jikan gidan Alhaji Na Allah ne,ba nan na ke zama ba, can Katsina muke zaune da iyayena. Wani aiki na zo yi na watanni huɗu anan Bakori, Sunana Mukhtar".
"Allah shi taimaka Muntari, nagode da nuna son taimakon Ammata".
Bayan sun tattauna Gwaggo ta amince da batun shi,bayan ta shaida ma sa cewa za ta tuntuɓi mahaifin Ammah.
Yinin ranar Gwaggo tunanin mafita ta ke ga rayuwar Ammah.
Ta na zaune ta yi zuru tana duban kasa, mafita ta ke nema wacce za ta sa Malam ya aminci da batunta.

06:15PM
"Gwaggo! Gwaggo!! Gwaggo!!!"
"Wannan kira haka na lafiya ne Ammah".
"Am.. Am.. Am..".
Tari ya sarketa, numfashinta na fita da sauri a sanadiyyar gudun da tayi.
"Ungo sha ruwan nan".
Ta kurɓa sannan ta ce
"Gwaggo ina cikin ɗaliban da aka dauka za su yi musakar Al-Qur'ani a Islamiyyar, idan munci mu ne zamu wakilci karamar hukumarmu".
"Kai Madallah da wannan daddadan zance, Allahu ya ma rayuwarki albarka Ammah".
"Amin Gwaggota".
Inna da ke cikin ɗakinta tana jiyo su, ta ɗaga hannayenta sama ta na ma Ubangijin talikai godiya. Fuskarta ta yalwata har ta gaza ɓoye hakoranta,kamar gonar auduga.
***
"Malam dama wata magana ce nike son mu yi".
"Ina jin ki Halima".
"Jiya na so mu yi maganar da daddare sai naga kamar ka gaji Shiyasa na ce in bari sai yau".
"Ai jiya na gaji sosai, ba laifi anyi ciniki sosai a kasuwa Inaga saboda lokacin kaka ne, ina jin loton da Ammah ta shigo ta fita nasan ganin ina bacci ne".
"Da ma maganar kan Ammah ce, ina ga ma ita ta zo ta sanar ma, an zaɓe ta cikin wadanda za su yi musabaqa".
"A'a lallai na ji dadi gaskiya, ashe dai tana maida hankali?"
"Ai Ammah ba daga nan ba. Toh Ameer din islamiyyarsu Ammah ne ya zo da batun koya ma ta karatu lokutan da basu islamiyya, dan ta fidda makarantarsu kunya, yaron jikan gidan Alhaji Na Allah ne".
"Ai ba matsala dan gidan tarbiyya ne, ki ja ma ta kunne ta kiyaye banda rawar kai".
"In Shaa Allahu ba za a samu matsala ba, tunda anan cikin gida za su rika karatun".
"Yauwa toh, ba komi yasa nike kaffa-kaffa da amanar da Allah ya ɗora man ba sai gudun ranar da wani banza can zai wargaza man kiwon da na ɗade inayi, ba ni son tarihi ya maimaita kansa, kin dai san abinda ya faru shekarun baya, da karatun boko ne ba yarda ma zanyi ba, yanda na tsani mutuwata haka na tsane shi kinfi kowa sanin haka, su Mubarak ma ba dan ya'ya maza su ke ba, babu dalilin da zai sa na saka su boko. Ya'ya amana ne a hannunmu".
"In Shaa Allahu za a kiyaye Malam, da Macen da namijin addu'a ce kadai mafita garesu Malam".
"Kayya! Halima miyasa kike son maida hannun agogo baya ne?".
"Ayi hakuri Malam".

***

Mukhtar ne ke sallama a kofar gidansu Ammah, ta fito sanye da hijabinta, ta gaida shi.
"Bari Inje in faɗa ma Gwaggo ka iso".
Gwaggo ce ta fito su ka gaisa da Mukhtar, tana kara ma shi godiya.
Tabarma Ammah ta shimfiɗa a karkashin bishiyar dalbejiya da ke tsakar gidan. Ta dauko littattafan da ta siyo (20 leaves exercise book).
Darasin harshen Turanci suka fara da alphabet, daga nan suka gangara kan Hausa wasulla da bakaken Hausa.
"Inyee Ammah ba! Kin bani mamaki yanda ki ka iya rubuta waɗannan baƙaken, ko dan kin iya rubutun larabci ba za ki sha wahala ba".
Kumatunta suka lotsa, wanda ya fito da tsarin hakoranta masu kama da kankara dake dauke da wushirya.
Bayan sun gama tayi bitar karatun da aka koya ma ta a islamiyya inda ta kuskure ya gyara ma ta.
Inna da ke madafi (kitchen) sai abin ya burge ta, ta kara jinjina irin kaunar da Gwaggo ke ma gudan jininta.
Littafin da take zane-zane ta fiddo ta ce "Yaya Mukhtar kalli wannan littafin".
"Call me MK ok! ".
" Mi kenan?".
"Nace ki kira ni da MK ba Mukhtar ba". "A'a ni ban iya kiran sunanka kai tsaye, Gwaggo ta hane mu da kiran sunan babba gatsal sai dai Ince Yaya MK".
Lumshe idanunsa ya yi, tare da fitar da sassaukar ajiyar zuciya.
"Ce Ya MK mu ji".
"Yaa MK".
Ya ɗaga ma ta babbar yatsansa.
"Wai mi MK ɗin ke nufi?".
"Mukhtar! Haka abokai na ke kira na da shi harda Hajiyata da yayyena".
"Dama kana da yayye?".
"Eh mu uku ne, Yaya Habib, Ya Sadiq, shi yaya Habib yayi aure watanni huɗu da suka gabata, yana aiki a Jami'ar Ummaru Musa, sai Yaya Sadiq da ke masters ɗinsa a Accra, Ghana, sai ni da ke UMYUK ina karantar Biochemistry, ina aji uku zan shiga huɗu".
"Kunji dadinku duk 'yan boko ne gidanku".
Sumar kanshi ya shafa, sannan ya karɓi littafin da ke hannunta yana dubawa, zane ne iri-iri a cikin littafin wanda Ammah ta zana. Ya girgiza yana yaba irin baiwar da Allah yaba Ammah, zamansu na awanni biyu da wasu mintuna kacal! Ya fahimci akwai baiwa a tattare da ita.
Agogon hannunsa ya duba, yaga karfe ɗaya saura.
"Ammah bari in wuce inada aikin da zanyi a asibiti yanzu, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, ki tabbatar Kinyi bitar abinda muka yi".
Ta gyada kai.
Ya yi ma su Gwaggo sallama, Ammah ta raka shi har kofar gida.
Suna fitowa Asma'u na kowawa bakin saitin gidansu Ammah, karaf ta ji muryar Ammah na cewa "Sai an jima Ya MK, nagode a gaida Hajiya".
Tsadadden murmushi ya sakar ma ta.
Cikin sauri Asma'u ta sha gabansa.
"Mi ka ke yi gidansu wannan yarinyar tunda dai na san ba ku haɗa komi ba".
Ko kallonta be yi ba, ya kara gaba.
"Mukhtar kana jina ka yi banza da ni?".
"Idan ki ka koyi yanda ake magana, ranar zan saurare ki".
"Ni din ce ban iya magana ba?"
Bai ko tanka ma ta ba, ya kara gaba.

MADUBI Where stories live. Discover now